← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 89

Sashe 12

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai a lokacin lda suka haɗu da Yaya Abubakar a wajen jana'iza bayan sun gaisa ya yi masa murnan aure ya kuma ce Sadiya ce ta sanar dasu. Tun daga lokacin ya ji jikinsa ya mutu. Ashe ashe tuni Sadiya kallonsa kawai ta ke yi bai sani ba! Sai a lokacin ma ya riƙa tunano attitude ɗin da ta riƙa bashi tun ranar Anniversary ɗin su, bai taɓa kawo ma kansa labarin auran sa da Gimbiya ta ji ba, Bai taɓa tunanin roƙon da ya yi ma ƴan'uwan shi da alfarman da ya roƙa ba su yi masa ba. Ya a ka yi sadiya ta ji wannan mganar? Sai a lokacin ya tuna abin da ta yi jiya lokacin da ta ga Gimbiya na kiran wayarsa a she duk a lokacin ta na dannewa ne amma ta sani kawai kallon shi ta ke yi.

Ya tuna a lokacin ya na hanya zai koma office daga wajen jana'iza ya kira Abba ya na faÉ—a masa Sadiya ta sani ba tare da shi ya faÉ—a mata ba.

"Laifinka ne Tafida me ya sa ka yarda ma aka É—aura auran ba ka koma gida ka faÉ—a mata ba?

"Na so haka Abba amma Nene ta ce yanzu yanzu mu tafi Rano."

Ya bashi amsa cikin karaya. Kalmar ɗaya Abba ya sake faɗa masa sai ya ji ya ƙara jin mutuwar jiki.

"Kai ba ka jin shawara. Da tun tuni ka ji shawaranmu ni da Tariq da  a bakin ka Sadiya za ta ji wannan mganar gashi yanzu an ɓata komai sai dai ka yi hakuri ka zuanar da ita ka yi mata bayani "

"Ba zan iya ba Abba. Ina jin kunya."

Tafida ya faɗa  a marairaice.

"To sai wa zai iya faÉ—a mata in ba kai ba?

"Kai mana. Don Allah ka taimake ni ka zo ka yi magana da ita."

"Mtseww. Ni na ce ka yi auran? Can ta matse maka "
.
Daga haka Abba ya katse wayarsa ya bar Tafida da tattaradi.

Bayan tasowarsa daga office har gida ya koma amma wallahi ya kasa shiga ya kasa iya tattara kalaman da zai yi amfani da shi wajen kare kanshi a wajen Sadiya.
Kawai sai kuma ga Kiran Nene da cewa ya zo gida tana son ganin shi, gaban shi ya faɗi domin a irin wannan kiran ne ya na zuwa a ranar bai yini ba sai da ya zama mijin Gimbiya abin da bai taɓa hasashe ba, ko ma yana hasashen bai kawo shi nan kusa ba.

*Janafty*
*TKG*

04.

FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622

RANAR ÆŠAURIN AURAN GIMBIYA DA YUSUF.

Ya ji tsoro da kiran Nene shi a tunanin shi kiran gaggawan da ta yi masa ko jikinta ne ya tashi, kuma ta ce ya zo gida da gaggawa tana neman shi sai ya firgita shi ya sa ya fita ko ƙaryawan da Sadiya ta matsa ya tsaya ya yi bai yi ba ya ce sai dai in ya dawo.
  Bai taɓa kawo ma kansa hashashen ga in da kiran Nene ya dosa ba saboda a yana hanya ma kafin ya ƙariso gidan sai da ya kira lambar wayar Gimbiya amma ba ta ɗauka ba sai ya ƙara firgita a tunanin shi jikin Nenen ne ya yi tsanani. Hankalin shi bai ma kawo masa a muryanta bai ji alamun ciwo ko wani abu ba.

Karfe takwas da rabi na safe ya shigo gidan, ya haɗu da Hajiya iya a ƙasa suka gaisa kuma ya ga ba ta ce masa komai ba, bai dai ji hankalinsa ya kwanta ba sai da ya shiga falon Nene ya ganta zaune a kan kujera ta yi wankanta tas da ita kuma cikin ƙoshin lafiya sannan ya iya sauke ajiyar zuciya na samun salama da natsuwa.
Bayan ya zauna a gefenta ya shiga gaisheta cikin ladabi ta amsa masa cikin fara'a da soyayyar da ta ke yi masa wacce ba ta iya ɓoyuwa a cikin idanuwanta.

"Ya wajen ita Sadiyan? Ina takwarata da Maimuna? Ina fatan duk kuna nan lafiya."

Kansa na ƙasa ya ce"Duk lafiya lau Nene. Su Jidda kuma suna makaranta sun koma tun jiya."

Kai ta gyaÉ—a kafin ta ce" Allah ya taimaka. Allah ya yi musu albarka gabaÉ—aya."
Ya amsa da Amin Amin shuru na wani lokaci saboda ya ji falon shuru sai ya É—an waiwaya ya kalli É—akin da Gimbiya ta ke kwana ya gansa a kulle sannan ba alamun ta na ciki sai ya juya ya na kallon Nene lokaci É—aya ya na faÉ—in" Ke kaÉ—ai ce Nene? Daugther ta fita ne?

"E. Ta fita yanzu ba daÉ—ewa an kirata daga wajen aikinta."

Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Ina hanyan zuwa nan ma na kira wayarta ba ta shiga. Ni fa hankalina ya tashi da kiran ki Nene na É—auka ko jikin ne ya tashi."

Sai da ta yi mirmishi kafin ta ce" Ko ɗaya lafiyata ƙalau Tafida."
Sai kuma ta yi shuru shi kuma sai ya bi ta da Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon kwana Nene."
Ta amsa masa da Amin Allah ya sa.

Shuru ya sake biyo baya na tsawon mintina biyar. Ya na kallon Nene ya ji ko za ta ce wani abu. Amma ya ga ta yi shuru kuma ya san tun da ta kira shi akwai mgana.
Sai ya gyara zama shi ya kauda shurun kafin ya ce" Nene akwai damuwa ne? Ko wani abu kike so na yi miki?
Sai ta kalleshi, ko acikin ƴaƴanta Yusufa na dabam ne. Shi ne ya ɗibo kusan hallayar marigayi mahaifinsu. Shi ne kawai in ta yi shuru ya ke fahimtar ta na buƙatar wani abu amma ta na jin nauyin tambaya.

"Nene ki yi mgana mana. Komai kike so nan duniya zan iya miki shi ko da ya gagareni zan nemi taimako a wajen wanda zai iya yi mini alfarma domin na faranta miki."

Ya faɗa ya na matsowa kusa da ita. Sai ta ɗago ta kalleshi kafin ya ji ta saka hannayenta duka biyu ta kama duka hannayensa lokaci ɗaya ta na faɗin" Alfarma na ke so na roƙa a wajen ka Tafida. Amma kar ka ji a ranka ko na tursasa ka ne, ina so komai da zai faru ya zama da amincewarka da yardan ka ne."

Cikin mamaki ya kalleta kafin ya ƙara jimƙe hannayenta ya na faɗin" Nene ni ne fa Tafida! Umarni kawai za ki ba ni na cika miki shi ai tsakanin mu ba alfarma Nene."
"Akwai Tafida. Akwai alfarma a tsakanin uwa da É—anta. Nima yau albarkacin wannan alfarman na ke so na ci a wajen ka Tafida."
Da sauri ya ce" FaÉ—i ko miye Nene, ni ko zan cika mganarki da sunan umarni ba alfarma ba."

Ta na mai kallonshi hannuwansu sarƙe cikin na juna ta ce" Tafida ka san a shekarun baya da ka kawo mganar auran Sadiya na goya maka baya a lokacin da ƴan'uwanka suka ƙi fahimtar ka ko?
Sai ya gyaɗa mata kai amma gabanshi na faɗuwa domin bai gane in da mganar Nene zai dosa  yanzu kuma ba.

"Har ga Allah tun  ganin farko da na fara yi ma Sadiya a cikin falon nan nawa a shekarun baya na yaba da hankalinta na kuma san ka yi dacen samun mata tagari. Sadiya ba ta gazamin ba kuma ba ta yi min komai ba wallahi sai ma tarin alherinta zuwa gareni."
Ta ɗan dakata tana kallonshi kuma shi har ga Allah ya ƙosa ya ji in da mganganun Nene suka dosa.
  Ajiyar zuciya Nene ta sauke kafin ta ce" Tun muna ƴan mata ni da Hajiyar Tafida muka yi alƙwarin da fatan in mun yi aure mun hayayyafa za mu yi haɗin auran zumunci a tsakanin y'aƴaƴyanmu domin ƙara karfafa zumuncin da ke tsakanimu, sai ga shi kuma mun auri mazaje abokai, sai amintan mu ya yi girman da mutane ma suna kwatance damu. Tafida tun da na haife ka na ji a raina kai ne za ka iya cika mini wannan alƙwarin. Zaman ka a Rano a gidansu Gimbiya da shaƙuwar da ke tsakaninku sai muka sakankance za ku dai dai ta kanku har burin mu ya cika kwatsam sai ka zo mini da mganar Sadiya."

Zuwa yanzu kam jikinsa ya yi sanyi shi ai ba yaro ba ne tuni ya fara fahimtar in da maganganun Nene suka dosa amma bai katse ta ba, gwara ya ji ta har ƙarshe domin ya san a ina za ta dire mganganunta.
Ita kuma kallon shi ta ke yi ta na ƙara nazarta yanayin sa. Amma ko a fuska bai nuna mata wata alama da za ta ce mganganunta ba sa yi masa daɗi ba. Sai kawai ta cigaba da faɗin.
Chapter 12 · 0% Book details