Sashe 45
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
An ga tururuwa har mutanen Rano duk sun zo, yan nesa kuma sun ta kiran waya. Kwana uku Nene jiki ya yi sauki ta na mgana ta na kuma motsa hannunta kaÉ—an kaÉ—an dai. Hajiya Tafida ma ta zo ta kwana É—aya ta koma. Su Kawu Abba kuma kullum sai sun zo nima na kira Gida na faÉ—a Gwaggo sun zo ita da Alhajinmu da Ya Abubakar sannan su Rahila ma Ya Aina ta haÉ—o su gabaÉ—aya sun zo har asibiti sun duba Nene Ma'u kuma daman anan suka iske ta ma, ni fa har mamakinta na ke yi ko Nene ta haifi Alhaji mustapha sai haka shima ya na zuwa kuma ba sa zuwa hannu rabbana, kamar yadda muke dafo abinci ni da Hauwa haka itama ta ke zuwa da shi.
Za mu haɗu da Gimbiya kullum amma tsakanina da ita gaisuwa ce, Jidda kuma ta koma gida saboda Gimbiya na asibiti, Yallaɓai kuma daman barci kawai ke kai shi gida da safe kafin ya wuce wajen aiki zai biya haka da yamma in ya dawo, wata rana har sai na fara gangyaɗi ya ke cewa na tashi mu tafi gida yara fa Ɗorayi Salisu ke kai su in sun tashi makaranta sai za mu koma gida mu biya mu ɗauko su.
 Kwanan Nene goma a asibiti sannan aka sallame ta ta dawo gida. Kuma ban taɓa fashin zuwa asibiti ba kullm safiyar Allah duk da zirga zirga ya sa duk na ji jikina na ciwo ga shi ina fama da ciwon mara kwana biyu nan ga ciwon kai da daddare na dai sha mgani amma ko Yallaɓai ban faɗa mawa ba. Da Nene ta koma gida Gimbiya ma can ta tare, ta na kula da ita kowa kuma yabon ta ya ke yi da ƙoƙarinta ni kaina na yaba mata ni kuma da ba a yabe nin ba na yaba ma kaina domin ni don Allah na yi. A baya kafin Gimbiyar ta yi ni na yi ko a yanzu ɗin ma ina iya bakin ƙoƙarina.
*Janafty*
*TKG*
12.
FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622
Gidana duk ya yi ƙura to ba na samun zama. Shi ya sa da aka sallami Nene sai na ɗan ɗaga kafa da zuwa Gwammaja in yau na je gobe ba zan je ba. Yallaɓai shima ya samu natsuwa tun da har Kaduna ya shiga ya kwana biyu. A ranar da zai dawo daga kadunan na je can Gwammaja da ya ke Jumma'a ne tare da su Jidda na ne tunda sai da na jira suka dawo muka taho tare. Na yo ma Nene ferfesun kayan ciki saboda na son ta na so, amma ina kawowa sai na ga Gimbiya ta yi mata amma duk da haka Nene ta karɓa ta ce za ta ci ko zuwa Gobe ne.
A gabana Anty Bahijja ta É—anÉ—ana ferfesun kai tsaye ta ce wai Nene ba za ta ci ba na cika ya ji kuma ya yi gishiri. Kuma ni dai har ga Allah na ci kafin mu fito komai lafiya na kuma san laluranta me ya sa zan cika mata gishiri da ya ji? Duk da haka ban nuna wani abu na danne a gabana ta ce wanda Gimbiya ta yi mata za ta ci shi ne ba zai mata wani abun ba.
"Wannan ko in kika ci sa ina ga sai kin koma Asibiti Nene."
Sai Nenen ta ce to su ci mana, irin dai kar na ji ba daÉ—i. Ko a fuska ban nuna ba illa Nene da na kallah na ce" Ban san gishirin ya yi yawa haka ba Nene ki yi hakuri."
Sai ta ce min haba bakomai ta gode da kyautatawa.
Falo na koma ranar Hauwa ba ta zo ba, Munnira ma haka ba ni da abokin hira, ina gidan Naja'atu ta zo da Anty Maimuna Nene ta sha magani ta kwanta sai suka baro ciki suka dawo falo suna hira suna shewa ina zaune kamar da gayya suna jefa min mgana.
Wai Naja'atu ke faÉ—in Gimbiya kar ta tsaya wasa ba wasa suka kaita ta yi ba. Haihuwa suke so. Ko kunya ta ma ba su ji ba kuma sun ganni domin har ita Naja'atun ma mun gaisa da ita.
"Ahto faɗa mata dai. Ni fa ciwon da ta yi kwanaki har na buga murnan mun samu ƙaruwa ashe ba cikin ba ne."
Ita kuma ta na mirmishi ta ce" Haka shima fa ya yi ta cewa ko ciki ne Daugther sai da muka je asibiti aka ce ba ciki ba ne sai da ya ba ni tausayi yadda na ga ya nuna damuwarsa."
"Allah sarki bawan Allah. Hauhiwa ya ke so amma an katse mishi ita a gidan shi da karfi da ya ji."
"To ai shi ya sa da Allah ya bashi dama ya mallaki gida biyu. Can É—in da aka katse mishi nan kuma ba sai a buÉ—a masa ba."
Anty Bahijja ta faɗa har suna tafawa da Anty Maimuna. Ni ko sai na yi kamar ban ji su ba wayata na ke latsawa amma a ƙasan raina baƙin ciki ne ya cika ni, nan suka ta yada min mgana amma ban tanka su ba shi ya sa tun kafin mangariba na yi shirin tafiya na shiga na yi ma Nene sallama.
"Na gode Sadiya Allah ya saka da alheri."
Na amsa mata da Amin na tasa kan Jidda da Baby, ko jiran Yallaɓai ma ban yi ba duk da na san in ya dawo nan zai biyo amma baƙin ciki ba zai bar ni na zauna. Ban kuma ƙi yi musu sallama ba na ce musu zan tafi har ita gimbiyan.
"Ba za ki jira shi ya dawo ba?
Gimbiyar ta ce min ni kuma sai na ce mata a'a ban san lokacin da zai dawo ba gwara na tafi kawai.
"E ki tafi kawai shi in ya dawo ma ya na da wata matar a nan za ta kula dashi kafin ya ƙariso."
Sai na yi mirmishi kafin na ce" Ai hakan ne ya kamata."
Saboda kamar haka ɗin ne in ya zo sai wajen sha ɗaya ya ke komawa gida sannan ba duka ranakun ba ne in ya koma ya ke cin abincin da na dafa in na kawo masa sai ya ce ya ci abinci a Gwammaja. Shi ya sa abin da ta faɗa bai zame min wani baƙo ba
Muna tafe a cikin adaidaita ina sharan ƙwalla saboda baƙin ciki, da Jidda ta gani ta yi magana sai na ce wani ƙwaro ne ya faɗa min a ido, haka na koma gida na ƙule a ɗaki na sha kukana na ƙoshi kuma da Yallaɓai ya dawo Gwammja ya sauka sai sha biyu saura ya shigo gidan nan ina zaune idanuwana biyu ban yi barci ba na yi masa sannu da zuwa ya amsa.
"A haÉ—a abinci?
Na faɗa lokacin da na ga ya na tuɓe shaddar da ke jikinsa.
"No. Na ci abinci a gida"
Haka kawai ya ce min ya tura kofa ya fice ina zaune na ji ƙaran buɗe ƙofa ya shiga tiolet sai na kaɗa kaina na koma na kwanta wasu hawaye masu zafi suka zubomin ban iya saka hannu na tare su ba. Domin saukar su ɗin wani ni'ima a cikin zuciyata. Ina kwancen na ji shigowarsa har kuma ya gama shirin kwanciya ya zo ya kwanta ina jin sa amma ban yi wani motsin da zai gane idanuwana biyu ba.
Kwanciyarsa ba daɗewa na ji an kira wayarsa yanayin yadda ya ɗauki wayar ne da maganar sa ya sa na gane Gimbiya ce. A kan gadon aurena ina kwance daga gefe Yusuf ke faɗa ma wata macen ya na sonta. Har ya na ƙasa ƙasa da murya wajen furta mata. I LOVE U TOO DAUGHTER." Kukan zuciya na ke yi amma hawaye suna zuba daga saman ƙuncina a baya in aka ce hakan za ta faru sai na ƙaryata a tunanina Yallaɓai ba zai iya son wata mace sama da yadda ya so ni ba, amma tun daga lokacin da ya yi auren nan na fahimci cewa duk ƙarya ce, yarda da aminci da na ba ma Yallaɓai tuni na fahimci cewa na yi kuskure Namiji ne shi kuma zai iya sauya launi duk lokacin da ya so kamar yadda ya fara sauya min lokaci bayan lokaci.
Ban san adadin lukutan da na ɗaukan barci bai iya ɗauka ta ba, na yi kuka kukan baƙin ciki wannan ƙololin abin da ya yi min sauƙi daga ƙasan zuciyata na ji ya na ta so min, ina ma kukan ne amma ina jin kamar ma ƙaruwa ya ke yi ba ya raguwa. Yallaɓai ko barci har da minshari na juya ina kallon shi ina jin wani kuka na ƙara taso min, yaushe a ka yi daren ballatana har garin ya waye? Har Yallaɓai na neman ya yi min nisa. Nisan da har abada ba zan iya dawo dashi kusa da ni ba, ganin kamar ya motsa ne ya sa ni kuma na tashi na faɗa tiolet a ciki na zauna na sha kukana sannan na tashi na kama ruwa nufina na ɗauro alwala amma sai na ga period ɗina ya zo. A lissafi daga watan jiya zuwa watan nan al'adan nawa ya ɗan dai dai ta sai dai ina fama da matsanacin ciwon mara ne a lokacin na kira Dr. Aisha ba ta ɗauka ba amma na bar mata saƙo ta wsop da niyyar in ta gani sai ta sanar da ni yadda zan yi.