← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 89

Sashe 76

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sake faÉ—a tana kuka, sai na zama yar kallo kawai domin film kawai Ma'u ke yi ta na zuba acting. Kukan da ta ke yi domin a ji tausayinta ne amma ni na san wallahi ba kukan nadama ba ne.

"To in sharrin sheÉ—an ne me ya sa shi sheÉ—an É—in bai faÉ—a kan kowa ba sai kan Sadiya? Ki dai faÉ—i manufarki kawai."
In ji Ya Auwalu Ya Hamza kuma ya karɓe da cewa" Nima shi na gani ba rami ba abin da zai kawo maganar rami."
Karar Baaba ta karɓe da cewa" Ba ya wuce yar tsaman dake tsakanin su. Tunda kuma ta ba da haƙuri ai shikenan ko?

"Ba shiken ba Baaba."

Na faÉ—a a fusace saboda na ga tana son ture laifin yarta.

"Ba shike nan ba, zarafina ta ci, ta yi min ƙazafi yau ko ƙararta na kai wallahi sai min yi sharia da ita."

Baaba sai ta kasa mgana ni kuma sai na cigaba da faɗin"Me ya sa duk a cikin gidan nan ba ta son ganin bayan kowa sai ni? Me na yi mata? Abin tambayan kenan ni kuma na san abu ɗaya ne na yi mata tun a baya da na faɗi cewa Ya Abubakar na sonta har aka fasa auranta da Ya Hamza. Daman tun a baya ta faɗa min zan gani yadda na hana ta abin da ta ke so nima sai ta yi barazana da farinciki na ga shi  kuma ta ɗau hanya kuna gani."

Na faÉ—a ina kallonta ta tsorata ba ta É—auka zan kawo wannan mganar ba sai ta daburce tun da ga mijinta a wajen ta fara rantsuwan ba haka ba ne.
"To in ba haka ba me na yi miki? Miji É—aya muke aure ko facaloli ne mu da za ki bi ki addabi rayuwata?
"Wallahi ba ki yi min komai ba Sadiya ko a baya da na faɗi haka yarinta ne. Amma tunda na auri Alhaji na cire komai a raina domin ya zame min garkuwan da na ke jjingina dai-dai da rana ɗaya ban taɓa nadaman auran shi ba."

Sai ta É—an dakata ta na kuka shi ta ke kallo, duk makircinta na fahimta ba ta so mganganuna su yi tasiri a zuciyarsa shi ya sa ta tsiro da wasu maganganu.
Shi ta ke kallo ta na faɗin" Alhaji shin dai-dai da rana ɗaya ka taɓa ganin wani chanji daga wajena a kan ka?
Sai ya girgiza kai kafin ya ce" Babu Ma'uta. Kuma kin ban labarin daman cewa Yayanki Hamza aka so ki aura sai Allah bai yi ba. Ni tsakanina da ke sai godiya da tarin alheri Asma'u."

"Alhamdulillah ka gama mgana"

Baaba ta faɗa da ƙarfi,kawai sai na ga Ma'u ta rarrafa zuwa gaban Alhaji ta faɗi ta na faɗin" Ka yi min gafara Alhaji in ba ka yafe min ba ina za ni Ba ni da wani uba kamar ka Sannan ba ni da wani gata sai gatan ka da gatan ƴan'uwana Don Allah ka yi haƙuri ka yafe min sharrin sheɗan ne ba zan ƙara ba."

Bai ce komai ba sai ta cigaba da kuka ta na masa magiya sai ya saka hannu ya É—aga ta zaune ya na cewa ta share hawayenta.

"Na yafe miki Asma'u. Uba ba zai taɓa riƙon yarsa a zuciyarsa ba. Sai dai ba shi zai hana ban faɗa miki cewa ba ki kyauta ba kin yi kuskure Babba. Ki yi juya ki nemi gafaran Dubu in kuma ta ce ba za ta yafe miki ta yi dai-dai ba zan matsa mata ba, na san ba zan ce ta cigaba da zumumci da ke ba, amma zan faɗa mata kar ta zama mai yanke zumumci da ke, ta yi miki kara sabo da ni da Mahaifiyarki. Amma tabbas ba ki kyauta ba ni kaina ban ji daɗin abin da kika aikata ba, ina jin kunyar kaina da waɗansu mganganun da aka ce daga bakin ki a ka ji su."

Ta na kuka ta na faɗin za ta roƙe ni gafara ba ni ba dukkanmu za ta roƙi gafarammu. Ta fara da roƙon Gwaggo da cewa ta yafe mata ba za ta ƙara ba.
"Bakomai Asma'u na yafe miki amma don Allah ki kiyaye. Dadiya fa Æ´aruwanki ce bai kamata ki bari sheÉ—an ya yi tasiri a kanki saboda ita ba."
Da ta je gaban Ya Aina ta na kuka ta na cewa ta yafe mata kai ta kauda kafin ta ce" Bakomai amma dai kin ba ni mamaki sannan ki yi haƙuri ina ji a raina ba zan ƙara yarda da ke ba."

Ya Balki kam sai da ta kalleta ta ce" Kin dai ɓata wayon ki Ma'u ban zaci haka daga gare ki ba. Ki gyara domin ko a nan gaba ba munafunci da gulma ba shi da amfani."
Ya Murja ba ta ce komai ta dai ce Allah ya yafe mana gabaÉ—aya amma ita kanta ai ta sha mamakin Ma'u.
Ya Auwal ma yace shi in dai na yafe shima ya yafe. Yallaɓai ko da ta isa gaban shi tun kafin ta yi magana ya dakatar da ita da cewa.

"Abin da kika aikata kin san bai chanchanci yafiya ba ko? Saboda kin haɗa fitina fitinar ba domin Allah ya taƙaita ba da yanzu lamarin ya wuce tunanin kowa. Sadiya matatace da muka yi aure tsawon shekaru goma sha biyar amma ni na san abin da za ta aikata da wanda ba za ta aikata ba, abu ɗaya zan faɗa miki shi ne ki daina biye ma zuciyarki ki kuma yi yaƙi da sheɗan da kika ce shi ya rinjaye ki. Mgana ta karshe shi ne alaaqar dake tsakanin ki da Yayata don Allah ta tsaya haka nan.  Ina son na zauna lafiya da matana da ƴan'uwana."
Sai ta kasa mgana Ya Hamza ya ce daman alaqa in ba alheri a cikin ta rabuwan shi ya fi.
Har Ya Abubakar da ya ke É—an amshin shata sai da ya ce mata ba ta kyauta ba.

"Ba Sadiya kika tozarta ba mu kika tozarta. Kuma ba zan ƙi faɗa miki kin ba ni kunya ba. Allah ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba."
Shi ko Ya Hamza gyara zama ya yi ya na faÉ—in" Ke yanzu in Sadiya ta haÉ—a kai da abokiyar zaman ki ta ci duduniyarki za ki ji daÉ—i? Ta girgiza kanta sai ya cigaba da faÉ—in" To me ya sa kin san ba daÉ—i kika aikata abin da kika aikata?
Sai ta ba shi amsa da sharrin sheɗan ne kamar zai deke ta ya ce" Ke ce sheɗaniyar kenan kuma in ba ki yaƙi da sheɗancin da ke tare da ke ba, ba za ki zauna lafiya ba. In wannan karom mun yi miki afuwa wallahi tallahi kika sake aikata makamacin haka sai dai ki je can gaban hukuma ki fitar da kan ki."

Y Muntari kuwa hadisi ya jawo mata ya ce addini ya hore mu da mu so ma junanmu abin da muke so ma kan mu. Sannan ta shiga hankalinta kar ta koma ga Allah haƙƙin zumumci ya bibiyeta."
Mijinta ko cewa ya yi ya yafe mata domin ya san sharrin sheÉ—an ne ba halinta ba ne har ya na share mata hawaye.
Ni ce ta ƙarshe Ma'u ba ta ji kunya ba wai ta kalleni tana cewa na yafe mata sharrin sheɗan ne.

"Ni da ke mun san gaskiya. Ba wani sheÉ—an daman kin shirya ma hakan. Ma'u abin da kika yi min mai zafi ne. Ina so ki sani ko na yafe miki ba zan iya cigaba da zumunci dake ba"

Na faɗa kai tsaye saboda ba zan yi ƙarya ba zan yanke alaqata da Ma'u  domin ko ban yanke ba, ba na jin zan iya cigaba da mu'amala da ita.
Sai kawai Baaba ta ce ai ni ce na ke da kafiya tunda ta roƙe ni gafara me zai saka ba zan yafe mata ba.

"Na ce na yafe mata. Amma ba zan iya cigaba da zumumci da ita ba. Nan ɗin da ya haɗamu dole in mun haɗu mu gaisa domin  ni ba zan yi gaba da ita ba. Amma duk wani abu daya dangance ni na cire ta a ciki shi ne mgana."
Kuma kowa ya goyo bayana har Alhajinmu wannan karon bai yi magana ba.
Abu É—aya ya ce min shi ne" Ki yi mata kara Dubu. Ki yi mata kara ko saboda ni. Ba yanzu ba in zuciyarki ta huce ki sada zumumci da Asma'u domin har abada ita É—in jinin ki ce."

Saboda Alhajinmu da kuma karan da ya ce in yi masa. Shi ya sa na gyaÉ—a masa kai ina mai faÉ—in" To Alhaji in sha Allahu zan yi yadda ka ce"

"Na gode miki Dubu. In na faÉ—a kina ji, in na kuma ba ki unarni nan ta ke kike yi ba tare da jinkiri ba. Allah ya yi miki albarka."

"Amin Alhajinmu."

Sai ya kalleni kafin ya ce" In na ce kin yi kuskure a lokacin kike aminta da cewa kin yi kukure sannan ki ce za ki gyara. To yau ma zan ce kin yi wani kuskure guda É—aya kacal Dubu."

Ba ni kaÉ—ai ba. Kowa da ke falon sai da ya kalli Alhajinmu cikin mamakin kalaman shi.

"E kin yi kuskure guda É—aya. Kuskure kuma shi ne me ya sa kika ta ka zuwa gidan Asma'u ki ka ja ta da faÉ—a? Me ya sa kika yi haka?

"Raina ne ya ɓaci Alhaji. Raina ya ɓaci na ji baƙin cikin da ban taɓa ji ba, shi ya sa sai zuciyata ta ɗebeni har na je gidan ta amma ka yi haƙuri tun da na yi kuskure."

"Na haƙura tun da kin ce na yi haƙuri. Kin amince ba ki kyauta ba?

Sai na gyaÉ—a masa kai lokaci É—aya ina mai dukar da kaina ina mai kallon adon cafet É—in falon.

"To tun da kin amince ba ki kyauta ki juya ki ba ma Asma'u haƙuri."

"Shi ne adalci kam"

In ji Baaba.

Ba domin Alhajinmu ba ne da ba wanda ya isa ya sa ni ba ma Ma'u haƙuri amma Alhajinmu ne shi isar kowa ne anan falon gabaɗaya.

"Ki yi haƙuri."

"Ba komai."
Chapter 76 · 0% Book details