Sashe 55
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na faɗa kai tsaye, saboda na ga sai wani cin magani ta ke yi ni dai ban ko bi ta kanta ba can su ƙarata yara ne suka raka su haraba ni dai daga ƙofar falo ban ƙara gaba ko'ina ba. Sun tafi ba daɗewa nima na tattara Iyalaina muka ya da zangon mu a Ɗorayi duk sammakona sai da su Rahila suka rigani zuwa Ma'u ce kawai na riga ta zuwa Amina daman tun jiya ta iso gida ya cika maƙil kwanmu da ƙwarkwatan mu Alhajinmu baki ya ƙi rufuwa.
Ko su Ya Hamza ban da salla ba abin da ke fitar da su waje duk ana tare a falon Alhaji ana ta hiran yaushe gamo. Abinci daman kowwccen mu ta yo girkinta nan fa aka baje ana ta liyafa ana hira ana ta dariya cikin Annushuwa kowa kuma da ruƙunin da ya ke zaune ni dai ina zaune ne da Khaleesat da Amina sai Ya Hamza saboda daman tun muna yan mata Ya Hamza na cikin Fav ɗina shi ma haka domin yadda ya ke kula da ni ko Rahila da suke uwa ɗaya albarka haka itama Rahila Ya Auwal ne na ta ko da matarsa ma sun fi ɗasawa ita kuma daman Ma'u tana rukunin Ya Murja ne Ya Aina kuma ita da Yaya Abubakar da Ya Balki ne in dai ya na gidan to tare suke zama Datti kuma ɗan gatan Alhaji ne ya na gefen shi. Saboda yau ta ke salla kuma an daɗe ba a haɗu ba sai ba a yi faɗa ba ana ta hiran zumumci ana ta shewa sai salla ke ta da mu.
 Â
Mun haɗu gabaɗaya mun yi ta hotunan tarihi da mu da ƴaƴanmu gabaɗaya. Mu ne har dare sannan Alhajinmu ya ce kowacce ta yi shirin tafiya gidan ta. Ni ban jira Yallaɓai ba domin ban san ko yaushe zai dawo ba, Ya Aina ta ce gobe Marwa ta koma gida sai na marairaice ina faɗin" Haba Ya Aina sai jibi dai. Kin ga gobe zan dawo za mu je can Gandun albasa ne"
"To Allah ya kaimu."
"To ke Ya Aina ku bar ma Sadiya Marwa É—in gabaÉ—aya mana tun da dai ta na son ta."
In ji Ya Hamza saboda shi É—an ba ruwan shi ne, ba kuma shi da tsoron yin mgana in dai ita ce a zuciyarsa.
"Sai ta haÉ—a da Jidda duk su aurar da su ita da Injiniya."
Ya Auwal ya faÉ—a ya na dariya Gwaggo na wajen har ta saka baki da cewa" To ko a yanzu Sadiya ce uwar Marwa. Ita Aina Mama ce ita kuma Sadiya Umma ce ka ga ko Umma ce uwar amarya."
Muna ta dariya gabaÉ—ayanmu Ya Aina dai ba ta ce komai ba sai mirmishi. Tare muka fita da Ya Ainan Ya Auwal ya É—au motar shi ya kai mu gida ni ya fara ijewa ni da yara ita kuma ya tafi kaita gida.
Yallabai kuma sai wajen sha É—ayen dare ya dawo ni kuma na gaji domin har ma na fara barci sama sama na ji dawowar shi da mganar shi da safe kuma bai yi min wata mgana ba nima ina sauri za mu je gidan su Mama sai ban tambaye shi ba. Tare da yaran muka sake komawa can Gwammaja daga can muka haÉ—u gabaÉ—ayanmu ban da dai Ma'u. Daman jiya ta ce za ta je kura wajen Baaba amma kaf É—in mu ne muka je gandun albasa gidan su Mama. Inna Mariya daman ta na gida ne mijinta ya daÉ—e da rasuwa.
Mun daɗe domin sai la'asar muka koma Gwammaja Ya Auwal da Ya Hamza sun yi musu alheri nima na kai musu nama da cincin da cake wanda na diɓa cikin wanda Gimbiya ta kawo min, suna ta mana godiya sun daɗe daman ba su ganmu mun haɗu gabaɗaya a lokaci ɗaya ba sai dai wani lokacin leƙowa dabam dabam. To wannan karon salla duk ya game mu waje ɗaya. Bayan mun dawo Gwammaja ne Yallaɓai ya kirani a waya ya ce na tura masa lambar Mijin Ya Aina Allah ya sa ina da shi na tura masa kuma ni ya ƙi faɗa min komai ya dai ce in na dawo za mu yi mgana saboda zumuɗi ana mangariba na tarkata su muka hau adai daita muka koma gida shi ko Yallaɓai sai wajen goma ya dawo min gida ina ta jiran shi in ji labari. Na yi ta naniƙe masa ina tambayansa ya ƙi faɗa min sai ja min rai ya ke yi daga ya ce bari ya yi wanka sai ya ce bari ya yi kaza har na gaji na ƙyale shi da muka zo kwanciya ma sai da ya ja muka yi ɓarnan ruwa bayan mun gama kuma ya ce ya na jin barci sai da safe da dai na fahimci da gangan ya ke wasa da hankalima sai na ƙyale shi.
Da asuban fari wayar Ya Aina ta tashe ni daga barcin da na koma sai ga labarin da Yallaɓai ke min ƙwalele ta na faɗa min domin ina ɗaga wayar ta ko gaisawa ba mu yi ba ta ce.
"Ke Sadiya jiya da daddare ba sai ga Baban su Jidda tare da baƙi ba."
"Baƙi? Wasu baƙin?
Ba maganarta ne ya ba ni mamaki ba sai illa baƙin da ta ce ya zo da su.
"E mana ko ba ki sani ba ne?
"Ban san ko abin da na sani kike son ki sanar da ni ba Ya Aina."
"To ke wani labari kika sani?
Kai tsaye na ce" To ni dai na san Autan su Nene Kawu Abba ya zo gidana ya ga Marwa ya ce ya na so. Kuma Yallaɓai ya ce min sun haɗu jiya sun tattauna kuma shi Yallaɓai ya karɓi lambar Baban Marwa a wajena ban san kuma da mganar wasu baƙi ba."
Cikin sauri ta ce" To ai mganar ne. Sun zo su uku da Baban jidda da wani sai shi mai son Marwa É—in."
"Ma sha Allah? Da me suka zo?
"Sadiya wai neman izini suka zo suna so a ba su dama ya fara mgana da Marwa in sun dai daita ba su son ya É—au lokaci."
"Alhamdulillah. Ya Aina Allah ya sa an ba shi dama."
"Babanta ya bashi dama Sadiya tun da dai daga bangaren ki da mijinki ne. Ba ki ga yadda ya ke jin daɗi yadda suka mutumtata shi ba ya ce tabbas ya ƙara ganin darajansu na yadda kafin su fara magana da Marwa sai da suka zo neman izini."
Ina murmushi na ce" Ya Aina ai Kawu Abba mutum ne. Tare suka tashi da Yallaɓai fa tun suna ƙanana da wannan wanda suka zo tare Yayan Gimbiya ne Amaryan Yallaɓai. Kuma ina mai baki tabbacin ki bi lamarin da addu' a in dai Marwa ta auri kawu ta gama yin miji."
Ya Aina ta ce"Ikon Allah. Ni ban ma san shi ba. Amma ya faɗa ma Babanta tarihin shi ya ce an taɓa saka masa rana yarinyar ta rasu tun daga ranar bai ƙara neman wata ba sai yanzu akan Marwa. Sannan ya ce ya na noma ya na kiwo."
Na karɓe da faɗin" Kwarai an yi masa tallar mata ba adadi ya ce ba ya so. Ke ce ba za ki san shi ba amma Rahila ta san su shi da Tariq tun Yallaɓai na neman aurena sun sha zuwa tare. Ya Aina gidan gona gare shi a Rano wai kin ga gidan da ya gina a can ne? Ba wai ina nuna ya na da kuɗi ba ne amma ina mai faɗa miki ya na da rufin asiri mata da yawa suna rubibin shi saboda in ba ya faɗa ba sai a ce saurayi ɗan shekaru talatin ne ba arba'in. Ke Ya Aina har Shema ƙawar Ma'u ta yaba da shi ya ce ba ya so, kin tuna na taɓa mata mgana har ya so ya zama faɗa kika ce na yi shuru?
Ya Aina cikin mamaki ta ce" Na ko tuna ikon Allah."
Ina dariya na ce" To kin ji fa. Ai mu sai godiya mun yi suruki ni uwar Amarya kuma surukar ango."
Ya Aina ma dariyan ta ke yi kafin ta ce" Kin sani kika yi min shuru ko Sadiya.?
"To ai na yi shuri ina ta addu'a kar na zo na faÉ—a kuma a ji shuru."
"Haka ne kuma to Allah ya sa alheri. Yanzu a sanar da su Murja ko mu jira zuwa gaba kaÉ—an?
Sai na ce" A'a su ba yanzu ba amma ki sanar da Alhajimmu da Gwaggo."
Da haka muka yi sallama duk Yallaɓai na jin mu muna gama wayar na yi masa gwalo ina faɗin" Labarin ka ya yi kwantai Yallaɓai "
Ya na dariya ya ce" Na ji bakomai. Kema ai kwantan kika samu"
Nima na ji bakomai tun da bai faɗa min ba ya riƙe labarin shi, sai daga baya ya ke faɗa min yadda aka yi ya ce min na sanar da Marwa domin Kawu ya na so ya fara mgana da ita.
Ina dariya na ce" To Kawu fa da gaske ya ke yi "
"Ai Kawu ya susuce. In ba gani ya yi an yi auren ba to Kawu zai iya ba da mu."
Ina ta dariya muna ma cikin mganar Ya Aina ta sake kirana ta ce ta manta ba ta ce na zaunar da Marwa na faÉ—a mata in ji Babanta na ce kar su damu zan sanar da ita. Yallabai bai fita da wuri ba sai azahar ya ce zai je Rano ya É—auko Gimbiya na ce sai ya dawo nima ranar ban fita ba ina gida amma na yi waya da su Ya Hamza suma duk sun É—au hanya domin komawa gida saboda aiki Amina ma ta bi Ya Auwal za su sauke ta a kaduna sai fatan Allah ya kai su lafiya.