Sashe 70
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya Hamza ya faɗa kafin ya cigaba da faɗin" Ni ban yi mamakin abin da Ma'u ta aikata ba daman can halinta ne ta na wani muƙu muƙu na munafunci ba Sadiya ni nan Hamza Muhamamad Yashe jinin Sadiya ba zan bari cin zarafin da a ka yi mata ya tashi a banza ba. Sannan duk wanda ya taɓa zuru'an Mama kamar zuru'an Gwaggo ya taɓa. Sannan duk wanda ya nemi tozarta zuru'an Gwaggo kamar zuru'an Alhaji ya taɓa. Kuma taɓa waɗanan zuru'an dai-dai ya ke da ka taɓa mana mutumcin mu da darajan mu, kuma taɓa darajanmu dai-dai ya ke da ka nemi faɗa damu. Saboda haka wannan lamarin ba Sadiya kaɗai ya shafa, har damu gabaɗaya."
 "Gaskiya ne wannan."
"Sabo da haka, yanzu zan kira Alhaji a waya na faÉ—a masa abin da ke faruwa. Ya kamata ya sani saboda abu ne da ya shafi auren Sadiya. Sannan za a yi zama zan kira Auwalu jibi asabar mu shigo Kano. Ba Ma'u ba har Baaba sai an kira. Za ta ci ubanta sai mun ji in yayar Yusuf ita ce jininta ba Sadiya ba. Kuma daga wannan a yi mata iyaka da komai yadda za ta fahimci Sadiya ma ta na da gata."
"Haka ne gaskiya ne. Haka yakamata a yi."
Nan take ya ce ta ba ni wayar da ya ke a speaker ta saka wayar shi ya sa na ji komai. bayan na amsa mun gaisa ya ce" An ce kina ta kuka? To ki share hawayen ki, mu Æ´an'uwanki za mu tsaya miki har sai gaskiya ta bayyana. Shi Yusuf É—in me ya ce? Ko wani mataki ya ce zai É—auka?
"Ya ce zai É—au mataki amma bai faÉ—a min matakin da zai É—auka ba."
"Ok. Daman ai na can gidan su matakin na hannun shi, mu kuma na mu na gida mu ne za mu gyara lamarin. Ki kwantar da hankalin ki, in ba za ki koma gida ki yi kwanciyar nan ki samu natsuwa har zuwa da safe. Amma shi kan shi Yusuf ɗin in bai wanke ki a wajen yan'uwansa da zargin da suka zarge ki ba, za mu saka baki mu mu ɗaukan miki mataki, ba ta yuyuwa a ɓata miki suna sannan a bar shi ya tafi a banza"
Bai kashe wayarsa ba sai da ya jadaddamin na kwantar da hankalina wannan karon Ma'u ta ƙai ƙarshe kuma sai ya ga ƙarshenta. Sai na ji hankalina ya kwanta ba tabbaci gareni akan Ya Hamza ba. Ina da kyakyawan yaƙini a kan zai tsaya a kan wannan mganar har sai an ƙwatomin haƙƙina kamar yadda ya faɗa, sai na ji hankalina ya ɗan kwanta ko hukuma ba ta shiga ciki ba, hukumar ƴan'uwana za su tsaya min har sai gaskiya ta yi halinta. Har sai ainihin fuskar Ma'u ta bayyana a gaban kowa ya gane ta.
 Ya Aina ta dafa min ruwa zafi na sha da bombita. Ta ce na kwanta na huta ciki na shiga na haye gadonta kuma cikin ikon Allah na ɗan samu barci amma zuwa huɗu da rabi na tashi lokacin Marwa ta dawo daga asibiti ba ta dameni da tambaya ba ƙila Ya Aina ta ce kar ta dame ni ne, amma dai mun gaisa har ina zolayanta da Amaryan kawu ta fita ta na faɗin" Kai Umma."
Tsakar gida na fita na yo alwala na iske Ya Aina ta tankaÉ—en garin tuwo. Yaran duk ba sa nan sun tafi hadda yamma, É—aki na koma na ta da salla, ina cikin sallar na ji muryan Rahila sai da na idar sai ga ta sun shigo ita da Ya Aina.
"Ah Sadiyalle daman kina nan?
Ta fada ta na ƙoƙarin zama a saman kujera.
Sai da na É—ago ina faÉ—in" Ga ni ko kin gani Rahilatu."
Sai lokacin muka haÉ—a ido ta ga yadda idanuwana suka kumbura saboda kuka.
"Ciwon ido kike yi?
Kafin na ba ta amsa Ya Aina ta ce" Kuka ta yi."
Sai ta kara kallona kafin ta koma kuma ta na kallon Ya Aina.
"Me ya faru?
"Daga ina kike da yamman nan?
Ya Aina ta katse mata tambaryarta.
"Makociyata ce ƙanwarta ta haihu. Shi ne muka haɗu gabaɗaya muka taho barka muna zuwa na ga anguwarku ne sai na ce su wuce bari na shigo mu gaisa."
"Me ya faru?
Rahila ta tambaya bayan ta dire maganarta.
"Lamarin ne abin mamaki da takaici."
"Wai me ya faru don Allah?
Nan Ya Aina ta labarta mata dukkan abin da ya faru sai Rahila ta saki Sahla da ke hannunta ta na shan nono kafin ta ce" Innalillahi kai Ma'u ta yi asara. Kai jama'a wannan wani irin cin zarafi ne da cin mutumci?
Ta faɗa har idanuwanta ya na kawo ƙwalla
Ni ta kalla ni ko na dukar da kaina ne kawai ban yi magana ba, saboda ana ƙara maganar abin ne ina jin ƙunar zuciyata na ƙara ƙamari.
"Duk abin da ke faruwa tsakanin Ma'u da Sadiya ban taɓa ba ma Sadiya gaskiya ba sai dai na ba ma ita Ma'u saboda dai kar ta ji a ranta muna wareta saboda ita ba cikin mu ta ke ba. Amma ni kaina na san Ma'u da wani abu a ranta game da Sadiya. Sai dai har ga Allah ban taɓa tunanin ta yi nisa haka ba. Ban taɓa tunanin za ta iya ba da goyon baya a ci zarafin Sadiya ba. Ban taɓa tunanin za ta je ta kai mganganu masu muni haka ba, mene ne riban ta ? Me ta samu? Har wata can ta fi mata jininta? Mene ne riban abin da ta aikata?
"Riban ta na tozarta. Ribanta a ci mutumcina na muzanta na wulaƙanta a idon duniya. Daman ta faɗa min a ranar da aka fasa auranta da Ya HamzaCds cewa sai ta yi sanadiyar muzgunama rayuwata kamar yadda na hana ta farincikinta nima sai ta hana ni nawa farincikin. Kuma ta daɗe ta na yi min bita da ƙulli wannan ne dai ya yi munin da ba zai ɓoyu ba."
Na faɗa ina maida hawayen da suka cika min ƙwarmin idaanuwana.
"Ba shakka."
In ji Rahila kafin Ya Aina ta karɓe da faɗin" Shi ne daman ta ke riƙe da shi? To ai abin da kika yi ba laifi ba ne. Ta dalilinki aka samu masalaha sannan aka cece taɓarɓarewan zumuncin mu gabaɗaya."
"Uhumm. Ni fa mamaki na ke yi wai Ma'u ce za ta yi ma Sadiya haka? Me ta tsare mata? Me ya sa ta yi haka? Har da zuwa ta na ba da labaran da ba su da tushe ballatana makama."
Rahila ta faɗa ta na ƙara bayyana mamakinta.
"To ai duk komai ya zo karshe. Domin Hamza ya ce ba za a bar mganar ba za a yi zama na musamman."
"Sosai. Ko ni ban goyo bayan a bar mganar ba. Ita kanta Ya Murja hakan sai ya zame mata darasi da kwashe wasu labaarn ta na faÉ—a mata."
Ya Aina ta ce" Kar ma ta yi hankali ita ta sani. Amma yaushe kana Babba ka riƙa bin yaro ƙarami kana gaya masa maganganu. Ni fa ban ɗauka za ta fita da mganar Marwa ba har sai da na ce mata ya ce ba ya so kowa ya ji sai sun gama dai-daitawa da ita Marwan sai ya je ya sanar da magabantan shi amman shi ne ta je ta faɗa ma Ma'u ita kuma ta je ta sanar ma ƙanwar uwarta."
Ya Aina ta ƙarishe faɗa cikin bayyana zafin abin har a cikin zuciyarta.
"Wata Marwan? Me ya samu ita Marwa É—in?
Ya Aina ce ta sanar da ita abin ake ciki.
"Shi ne fa ta je ta kwashe ta faÉ—a ma Ma'u ita kuma ta sanar ma Yayar mijin Sadiya shi ne ta ke ce ma Sadiya yadda ta shanye Yusuf shi ne za ta haÉ—a shi da É—iyar yayarta domin shima a shanye shi tun da mu yan dangin asiri ne."
"La'ila. Ya Aina"
Rahila ta faÉ—a ta na tafa hannuwana cikin al'ajabi da mamaki.
"Gaskiya Ma'u ta yi asara. Ta zama jaka tunda ta iya zaɓan bare a kan jininta. Na ji ta fita daga zuciyata sam"
"Wallahi nima. Ta fita daga raina kwata kwata. Ji wani tsohon labari da ko mu da aka yi shi muna da wayau, mun manta amma ita da ta ji labari ta iya riƙe shi a ranta har ta na kai shi gaba. Tir da ita. Tir da mai hali irin na ta."
Haka suka haÉ—u suna ta tattaunawa ni dai ina gefe ina jin su su sai yau suka san Ma'u? Ai ni na daÉ—e da sanin hallayarta mara sa kyau.
"Gwara da kika je gidanta kika yi mata hauka tun da ba ta da mutumcina."
In ji Rahila.
"Nima haka na ce."
Ya Aina ta maida mata martani. Rahila ta daɗe sai gabda mangariba ta tafi, ni kuma ina gidan Yallaɓai bai kirani ba nima ban kira shi ba. Yau ko su Jidda ban tuna da su ba, sai na ji komai ma ni ya fita daga kaina, ba na son komai kuma ba na jin daɗin komai, har dare da Babansu Marwa ya dawo ya ganni a gidan Ya Aina ba ta buɗa masa ba sai dai ta ce yar matsala ce muka samu da Yallaɓai. Nan fa ya zauna ya na min nasihan haƙuri da rayuwa jin sa kawai na ke yi domin duk abin da zan faɗa masa ba zai yarda ba gwara kawai na yi masa shuru.
Can dare Ya Auwal ya kira Ya Aina ya ce Ya Hamza duk ya yi masa bayani kuma jibi shima ya na ta fe. Har Gwaggo sai da ta kira Ya Aina ta ce labari ba daÉ—i suka ji Alhaji ma duk ya shiga damuwa. Ita ta yi mata ma wasu bayanan, Gwaggo sai salati ta ke É—aukowa ta na direwa.
"Asma'u ta ba ni kunyam ban taɓa tunanin sakara ba ce sai yau."