Sashe 25
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya faɗa cikin ƙasa da murya shi kan shi jikinsa ya yi sanyi, sai da na yi masa mirmishin jin haushi sannan na yi baya ina mai riƙe kuguna kafin na ce" Ni na zama a bar zolayan ka ne Yusuf? Ko bashi daman mgana ban yi ba na cigaba da faɗin" Ina ruwana da abin da ya shafe ka kai da amaryan ka. Ni abin da ya shafe ka ne ya zame min dole na ji ba wanda ya shafeta ba, in ka na so mu zauna lafiya a gidan nan ni da kai to ka cire ni cikin wannan lissafin na ka. Mgana in ta shafe ka ba ni da yadda zan yi amma in ta shafi amaryaanka ne ka cire ni a ciki saboda babu ruwana a ciki na faɗa maka."
Na faÉ—a ina mai sake nuna masa yatsa cikin gargaÉ—i.
"Laifi ne domin na faÉ—a miki! ? Ba na so ki ji labari a waje ba za ki ji daÉ—i ba."
"Na ji a wajen mana Sai me?
Na tare shi cikin tsawa kafin na cigaba da faɗin" Sai me don na ƙarishe jin sauran labarin daga waje? Auran ma ai shi kanshi daga wajen na ji to saboda haka ma wannan ka daina zaunar da ni ka na ɓata min lokaci ka na gaya min, ka bar na ji daga wajen ya fi min da ka zaunar da ni kana tattauna abin bai shafe ni da ni ba."
"Ni al'amarina bai shafe ki ba Sadiya.?
"Na ka ne ya shafe ni, amma na ta bai shafe ni ba. Saboda haka ka koya ma kanka É—aura kowa a mizanin matsayin shi in har kana son zaman lafiya."
Kallona ya ke yi, ni ma shi na ke, domin a lokacin ina jiran ya ƙara cewa tak ne a kan mganar Gimbiya ya ga hauka amma sai na ga kawai ya koma ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin" To shi kenan ki yi hakuri ba zan ƙara ba."
"Better."
Na faɗa ina mai juyawa zan bar masa bedroom ɗin, har na riƙe handle ɗin kofar sai na tuna da wani abu da sauri na juyo ina kallon shi, shi ma ni ya ke kallo sai kawai ya ga na dawo gabansa na tsaya kafin na kira sunan shi.
"Yusuf"
Kallona kawai ya ke ba tare da ya yi mgana ba.
"Abin da ka ke yi ba shi zai goge taɓon ka yi min kishiya ban sani ba. Sannan ba shi zai goge taɓon ka yi min kishiya a lokacin da ban yi tsammani ba, ba kuma shi zai goge wannan taɓon da ka yi min a cikin zuciya ta ba. Ni dai na yi ma kaina alƙwarin ba za a ji wani abu daga bangarena ba, amma ka sani duk abin da za ka yi ba zai taɓa goge taɓon ka shammace ni shammatan da ban taɓa tsammani daga gare ka ba, gwara ka yi harkan gaban ka kamar yadda ka saba, kar wajen ƙokarin kare kanka ka ɓata komai Yallaɓai. Gwara kawai mu tsaya a hakan ba na son wannan jaye jayen maganar naka domin ni ba burgeni ka ke yi ba sai ma haushin ka da na ke ji, gwara tun kafin rayuwankan mu su kai ga ɓaci gwara mu kiyaye ma juna."
Na faÉ—a ina mai kallonsa cikin ido, ajiyar zuciya kafin ya ce" In sha Allahu."
Ban tsaya bi ta kansa ba na fice har ina bango masa kofa kitchen na koma ina aikina ina masifa ni kaɗai ba ta yuyu kawai na zauna Yallaɓai na raina min hankali gwara na yi ma abin tufkan hanci ko zai gane duk kallonsa kawai na ke yi, ban kara komawa Bedroom ɗin nan ba har sai da ya yi wanka ya fita, na yi masa ta yi abin karyawa ya ce min ba zai ci ba, ko ta kan shi ban bi ba ya ce min zai fita ana jiran sa na ce Allah ya tsare.
Sai da ya fita na koma bedroom ɗin na gyara sannan na wanke kaina saboda ina so na yi kitso sannan na yi wanka. Ban ko faɗa masa gobe ne tafiyarmu Yashe ni da Rahila ba sai in ya dawo, sai yanzu ma na ƙara jin tafiyata ma ta zama dole ni ba zan zauna Yallaɓai na neman kashe ni da baƙin ciki da kalamansa ba.
Mai kitsona na kira a waya na ce mata ta zo anjuma ta yi min kitso, su Jidda ko wancan satin ni na yi musu saboda na kira wayarta ban samu ba yau É—in ma ta ce min ta na da yan kitso amma in za ta samu zuwa za ta gaya min.
Mun yi waya da Rahila ni na kira ta kan tafiyar mu ta ce min goben za mu tafi, saboda Ya Aina ta shiga kasuwa yau da kuɗin da muka haɗa gabaɗaya za a ɗan tsinta kayan kitchen sai zanin gado da labulanya in kuɗin sun ragu sai a ƙara mata da wani abu sannan ta na faɗa min ɗinkunan Amaryan ma nan Kano aka kawo mata suma in an gama tare da su za mu wuce na ji daɗin haka domin ba na so ma a ɗaga tafiyar nan ta mu kamar fa a kan ƙaya na ka haka na ke jin kaina a gidan gabaɗaya.
Na buÉ—e data ne na shiga group É—in gidanmu na ga Ya Aina ta yi godiya ga kowa saboda kuÉ—in da a ka haÉ—a ba ta dai faÉ—i a dadi ba, ta ce ta je ta faÉ—a ma Alhajinmu ya na ta saka mana albarka anan ne na ji Ya Murja na maganar yan tafiya na ji ta na ceewa har da Ma'u a cikin masu zuwa ita da ta ce ba za ta samu zuwa ba amma Ma'u ta ce ta shirya ta na tunanin direba ne zai kai su, duk ina gani ban yi magana ba sannan an yi maganar cikin matar Ya Hamza ko ta Ya Auwal in wata za ta samu zuwa duka dai suka ce ba za su samu zuwa ba sai kawai a ka saka Zaitunan Yaya Abubakar a cikin masu tafiya.
A raina na ce sai dai mu haÉ—u a can domin can anjuma da na sake hawa na ga Ya Murja na min mgana ni ba zan je ba ne? Kafin na ba ta amsa ma Amina ta faÉ—a mata gobe za mu tafi ni da Rahila saboda mun yi waya da ita da safe na faÉ—a mata.
 Kawai sai Ya Murja ta yi tagging ɗina da cewa" Uwar gida yaushe ne tariyan Amaryan ta ki?
Kamar zan amsa ta, sai na fasa kowa ya kirani a waya amma ban da ita, shi ya sa na yi kamar ban gani ba, amma ga mamaƙina Ma'u ce da ta zo ta ba ta amsa da cewa" Ƙarshen watan ne fa Ya Murja."
Mamakinta ya ƙara kamani wato ita har ta sani kenan, ina gani Ya Murja na sake tambayan a ina amaryan za ta zauna? Ta ce ba ta sani ba tukunna amma dai haya a ka ce za a kama mata.
 Ni dai kawai sai kallo na kasa magana Amina ce ta shiga hiran ta su ta na faɗin"Ya Ma'u ki bari Uwargida ta amsa mana mana"
Sai ta tura emojin dariya kafin ta ce" Na wakilceta ne.'
Yaya Murja ke ce ma Amina wai ta san akwai wata yayar mijina da suke aure a gida ɗaya da Ma'u suna shiri sosai a wajenta ƙila ta ke samun labari. Amina ta ce ikon Allah! Daga nan ba ta ƙara magana ba. Ta bar su suna ta mganganun su kamar ma da gayya suke yi ban ce komai ba na kashe data kawai na ijiye wayar saboda in na ma zauna ina gani sai raina ya yi ɓaci a banza.
Kayana na shirya a cikin akwatina mai ɗan girma. Lame ta aiko min da mai da showel gel jiya. Kaya na diɓa sama da kala biyar domin sati zan yi a Yashe haka na yi niyya. Har wajen la'asar mai kitso ba ta zo ba sai da na ƙara kiranta sai ta ce min tana hanya. Ba na so na je da kaina a tsife domin na gaji da shi a haka gwara na kiteshi ga shi an fara sanyi ma kar ya karye min.
Zuwan mai kitso ya sa na É—an saki da ya ke Æ´ar zamfara ce ta na da hira muna ta fira muna dariya har su Jidda suka dawo makaranta ban yi girki ba daman sai na ce in sun cire kaya Jidda ta sulala musu ko indomie su ci, mai kitso na ta mamakin girman Jidda ina dariya na ce.
"Kin dai daÉ—e ne ba ki ganta ba Maman Nana."
Ta na jinjina kai ta ce" Ko! Amma duk da haka Jidda ta ƙara tsawo masha Allah. Mun kusa kaiwa ga suruki ga Baby ma masha Allah itama ta na ta girma."
Ina ta dariya ban yi magana ba ina kallon Jiddan da ta cire unirform ta saka doguwar riga na atamfa sai nima na ga ta yi min girma, ba ta ma gama cika 14 ɗin ma sai watan gobe, sai dai nima na yarda ta ɗauko tsawon kafan babanta, Baby ce ke da jikin gaba gaɓan girma. Ni na ce Jidda ta dafa duka indomie ɗin tare da mu, Baby dai sai da tasha tea kafin a gama sai kuka ta ke yi wai ta na jin yunwa, sai da muka gama kitson sannan muka ci indomie Maman Nana ta ce ba za ta ci ba na ce sai dai na saka mata a cooler ta kai ma yara. Haka ko aka yi gabda mangariba ta tafi na ba ta kuɗin kitsonta da na adaidaita sai indomie ɗin da na saka mata a wata roba na ce ta kai ma su Nana daman haka na ke yi mata wani lokacin ko ma ta ci in za ta tafi in akwai na kan zuba mata na ce ta kai ma yara.