← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 89

Sashe 54

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dare muka dafa shinkafa Jalop da nama, muna ma cikin ci ne sai ga Yallaɓai ya shigo gidan bai ma wani tsaya ba ko abincin da na yi masa ta yi bai ci ba ya dai sha ruwa sai nama ya ci, cincin kuma da na ɗibar masa a leda ya ce na saka masa ya tafi da shi, ina jin haka sai na ɗibar ma Gimbiya kar ta ga ya je da shi ita ban kai mata ba, tunda ni ma ta na kawo min abubuwa in dai ta yi har soyayyen naman ma na ɗibar mata ya ko karɓa ya na ta murna har ya na ce min.

"Allah ya saka miki da alheri Sadiya ta."

Na amsa masa da Amin to har ya tafi fa sai ga shi ya kirani a waya wai zai zo na zuba masa abinci Gimbiya ba ta yi girki ba saboda ba ta jin daɗi. Na ce to ya zo ba daɗewa sai ga shi, a raina na ce shi ma dai da gulman shi na fa yi masa ta yi da farko ya ce ba zai ci ba ya ɗauka ta dafa masa ne in ya koma kar ya ce mata ya ci a wajena ta ji haushi sai kuma ta ɓare da shi a babba kula na saka musu mai yawa ya na ta min godiya.

"Godiyar nan ta yi yawa Yallaɓai sai ka ce na yi maka wani abu."

"Wani abu ne mana. Ke dai kawai Allah ya yi miki albarka."

Na amsa da Amin Amin sannan muka yi sallama ya tafi, ko washegari da ya ke gidana ma sai da ya karɓan mata tuwon shinkafar da na yi miyan agushi, ya na faɗa min ba ta yi girki ba ai ba ta son kamshin girki a raina na ce ko dai ciki ne? Amma ban furta masa ba amma dai na ce ya kamata su je asibiti ya ce za su je in sha Allahu.

  Tuwon da ɗan yawa na yi na aika can Gwammaja sai Hauwa da Mutaƙƙa ya zo ya karɓan mata sannan Musbahu ya zo da wani abokin shi, suma sun ci na saka musu cincin da Nama, da daddare ma sai ga Adnan ya na gidan sai ga Datti ya zo Allah ya sa da sauran shi sai na saka musu da ya ke kuma sun san juna suna ta hira. Wannan salla ban samu wasu yan yawon salla ba da rana dai Firdausin Ya Balki ta yo min zuga ƙawayenta da ƴan'uwanta bayan sun ci abinci da za su tafi na ba su 2k goron sallah ina ta tsumayin ƙannen Marwa amma ba su zo ba ranar salla ta uku kuma Gwammaja muka yi ni ban tsaya dafa wani abinci ba tea muka sha da safe muka tafi suma can ɗin cike gidan ya ke can na iske Gimbiya ina ganinta na fahimci ba ta da lafiya ta yi zuru zuru sai kwanciya ni dai kamar shigar ciki na gani tare da ita amma ban yi mgana ba haka ma kowa ke faɗi in ya ganta su Anty Bahijja ne yan faɗin in sha Allahu ma cikine za ta faɗa ma Tafida ya kaita asibiti a tabbatar.

Har su Hauwa sai da suka ce min kamar Amaryan ki na da shigar ciki na ce ban sani ba wallahi
Munnira ta kalli Gimbiya ta sake kallonta kafin ta ce" Ke Sadiya na ba ki tabbacin Amaryan Tafida ciki ne da ita."
Duk da acan ƙasan raina na ji wani iri amma ai tunda an yi dare ni na san garin zai waye komai daran daɗewa shi ya sa na yi mirmishi kafin na ce" Ina musu fatan haka"
Saboda ni na san Yallaɓai na son haihuwa Allah ne kawai bai bashi masu yawa ba na tabbata zai fi kowa farinciki da hakan shi ya sa a ƙarƙashin zuciyata  na yi ta karfafama kaina Gwiwa in ma ta na da cikin. Cikin na Yallaɓai ne kuma ni da na sha yi ma kaina alƙwarin in Yallaɓai ya ƙara aure har ya samu ƙaruwa zan fi shi murna da farinciki sannan zan so duk wani abu da ya fito daga jininsa ko tsatson sa. Shi ya sa na yi ta kiran sunan Allah a raina har ya kawo min agaji na ji na samu salama.

Muna Gwammaja har tara na dare da É—aya da É—aya kowacce mazajensu na ta zuwa É—aukan su. Wannan karon dai Cincin kawai da nama na kawo ma Nene ta yi ta saka albarka, Hajiya Iya da Maman farko sai na kai musu cincin kawai suma suna ta godiya da faÉ—in" Sadiya ba kya gajiya? Ina zan gaji ina ganin su ne kamar iyayena mijina suma yadda zan kyautata ma Nene haka suma na ke yi musu kamar yadda suma na ga Æ´aÆ´an gabaÉ—aya ba sa nuna bambamci a tsakaninsu. Gimbiya dai har da su Cake ta yi amma ina tunanin ba dawa ta yi aka yi mata an kawo min da yawa jiya har da dambun nama ga soyayye. Na gan shi na ma su Anty Bahijja suna ta ci da Naja'atu da ta zo daga baya.
Wannan salla Yallabai bai siya mana kaji ba wai ya manta lokacin da na tuna masa kuma duk an siye sai dai bayan sallah ya ce mu bi shi bashi, ni kuma ban ji daÉ—i ba saboda ni dai na fi son naman kaza fiye da naman rago shi ya sa ban ma wani ci naman sosai ba kuma wannan sallar ban yi dambu ba na gaji Marwa ta ce za ta yi na ce ta bar shi kawai.

Sai da Yallaɓai ya dawo sannan ya ɗauko mu gabaɗaya wannan karon ma a gidan gaban ya ce na zauna ita kuma a baya ita da yara. Sai dai muka fara kaita gida muka sauke su ita da Jidda sannan muka juya gida, muna hanyar komawa gida Yallaɓai ke faɗa min gobe zai kai  Rano Gombiya ta kwana biyu.

"Gobe? Ita da ba ta da lafiya?

Na faɗa ina mai kallon shi, sai ya kalleni shima kafin ya mai da hankalin kan tuƙin shi ya na cewa" Nima haka na ce mata amma ta matsa ita sai ta je. Sai na ce ta je ta kwana biyu ko?

Kai na gyaÉ—a kafin na ce"Haka ne. Tunda kuma ai ba kwance take rigis ba."
Daga haka na yi shuru ina jin shi ya na faÉ—a min wai ta matsu ne ta ta ji an ce duka yan'uwanta sun je can sallah.

"Har da Tariq da Farida?

"E mana. "

Sai na jinjina kai kafin na ce" Ban É—auka za su zo ba. Na ga ba su daÉ—e da komawa ba ne."
Ya na dariya ya kalleni kafin ya karkato ya na min raÉ—a.

"Maaganar Kawu da É—iyarki ne musabbin zuwan shi."

Sai na kalleshi ina faÉ—in" Da gaske? Sai ya koma ya gyara zama hankalinshi na wajen tuki ya na mai faÉ—in" Da gaske na ke faÉ—a miki. Gobe in na kai Gimbiya za mu haÉ—u mu kara tattaunawa yadda muka tsaida za ki ji "

Sai na jinjina kai kafin na ce" Allah ya tabbatar mana da alheri."
"Amin. Ai in sha Allahu Alheri ne tun da na ga Kawu ya susuce shi fa ya matsa mana sai mun haÉ—u akan mganar nan"
Ina mirmishi na ce" Allah ya tabbatar Yallaɓai."
Ya amsa da Amin muna tafe muna hira har gida, Marwa suka shige ciki da Baby ni da Yallaɓai muka zauna a falo muna kallo muna ta hira sai a lokacin ya ke faɗa min ya kama min shagon su na ƙasa sai kuma ga maganar auran shi da Gimbiya wai ya yi tunanin ya yi min mganar zan ce dannen kirji ne. Shi ya sa kawai ya buɗe ma su Musbahu da wani ma'aikaci da ya ɗauka suna zama a ƙasa shi kuma office ɗin shi na sama.

"Bakomai. Allah ne bai yi lokacin ba. "

"Zai yi lokacin in sha Allah soon."

Na ce Allah ya sa amma ba wai domin na wani yarda da shi ba.

"Wai shi Musbahu wani matsayi ka ba shi a wannan kamfanin naka ne Yallaɓai?

"Manaja na ne shi. Wanda na É—auka kuma mataimaki ne kafin dai mu ga abin da Allah zai yi kin san komai a sannu sannu ya ke tafiya."

"Haka ne. Kai kuma fa?

Ya na yar dariya ya ce" Ni? MD Managing derector."
Hannu na ɗaga masa ina faɗin" Allah ya ƙaro dubban Nasarori mai girma MD"
Ya amsa ya na shafa gashin kaina daman ina saman kirjinsa ne muna zaune a waje É—aya muna hira muna kallon wani film a MBC action.
Sai wajen sha biyun dare muka kwanta ni da Yallaɓai kafin mu kwanta sai da ya kira Gimbiya ta yi barci ba ta ɗauka ba sai da asuba ya same ta. Jikinta ya tambaya ta ce da sauƙi ina gefen shi ni ban ma ce ya ce mata ina gaisheta ba amma sai gashi ina jin sa ya na ce mata na ce ina mata sannu sai kawai na kalle shi ta gefen ido girgiza kawai na yi saboda Yallaɓai ya yi nisa ba ya jin kira lamarin na shi ya koma har da kage ni yaushe na ce ina mata sannu! Ai na yi mata sannun jiya da muka haɗu ba shiken nan ba.

Daga ni har shi da wuri muka shirya ni duk da na tsaya na dafa shinkafa da miya da salat wanda zan tafi dashi ɗorayi. Yallaɓai sai da ya ci sannan ya fita ya ce zai je ya ɗauko su Gimbiya mu shirya in ya ijemu a Gwammaja za su wuce. Ban yi masa mgana ba sai da ya ɗaukota suka dawo gidan ta shigo na yi mata ta yin abinci ta ce ba za ta ci ba ganin kamar ta na wani zumɓuran baki da ya ce tare za mu fita gabaɗaya sai kawai na ce masa su tafi mu in mun tashi za mu hau adaidaita.

  "Kin tabbata ba matsala?

"Babu ku je kawai Allah ya kiyaye hanya."
Chapter 54 · 0% Book details