← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 89

Sashe 10

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai na iya cewa zafi ai ba ma sai an faɗa ba. Ita kuma sai ta cigaba da faɗin" Kishi fa gaskiya ne Sadiya sai wanda aka yi mawa ya ke sanin haƙikanin zafin abin. In ka nuna damuwa a ce ka ɗaga hankalinka wane wane Alhalin ba wanda ya san irin zafin da kake ji acikin zuciyarka."

"Kwarai."

Na bata amsa sai ta cigaba da fadin" Ki daure Sadiya akwai zafi amma ki daure. Dangin mazajen mu suna neman ganin gazawarmu ce shi ya sa, shi na wajena ya auri yarinyar ogansa shi kuma na wajen ki ya auri yaruwansa duka fa domin a kaimu ƙasa ne kuma Allah ya fi su, ki daure zafin zai ta ƙaruwa barin ma in sun fara zama tare amma ki yi ta addu'a da ikon Allah za ki samu komai da sauƙi kin ji ko?

'"Na ji. Kuma in sha Allahu ba damuwa."

Mun dade muna mgana ta na ta bani shawarwari sai a lokacin ta ke faÉ—a min ashe a lokacin mganar auran ya Usman da ta dawo gida ba yaji ta yi ba ta ce kawai ta zo gida ne ta samu kwanciyar hankali amma dangin miji suka buga mata tambarin ta yi yaji, ni kaina na sha mamaki na ce mata mu ma haka aka ce mana wai kin yi tashin hankali har da su yin yaji.

"Uhm wallahi ni ban yi yaji ba. Da amincewarsa na taho gida Sadiya. Gwara mu yi nesa da juna sai na samu damar rage jin zafinsa domin a zauna lafiya. Ba gashi an yi ba kuma muna zaune gida É—aya da ita ba sai dai tana bangarenta ina nawa, ni dai ina zaman musulunci da ita, itama haka amma ba zan yi zaman daÉ—i da kishiya ba Sadiya shima ai na faÉ—a masa matarsa ta yi rayuwarta nima na yi tawa ni da Æ´aÆ´ana."

"Shi ne alheri ma."

Domin ban ga amfanin haɗa kai da kishiya yanzu ba kai ya waye ban da mutanen da wa ke maida kishiya yar'uwa wallahi gazarwar ki ta ke nema in kuma ta samu sai  ta yaƙe ki.
Anty Zabba ta yi ta bani wasu labarai ta na faɗa min na zama jaruma. Shawarar da za ta bani kar na ce zan bibiye ta na ɗauke kaina a kanta sai na zauna lafiya amma kar na sakar mata kar kuma na ƙi ba ta dama a yi zaman musulunci wanda ba zai wuce jaje ko taya murna ba, ta yi na ta rayuwar nima na yi tawa a hankali a hankali zafin zai gushe har wata rana ma sai na manta ina da kishiya. Ina dariya na ce.

"Daman ana mantawa?

Itama ta na dariyan ta ce" Sosai ma. Barin ma in ba gida É—aya za ku zauna ba"
Sai na ce mata ban sanin masa ba nan na ke faÉ—a mata ni fa har yau bai faÉ—a min ba amma na ji yana waya ashe shi ne ya roke su kar su faÉ—a,min har sai bayan shi ya faÉ—a mini da kansa.
Cikin dariya ta ce" Ya yi miki irin na ÆŠan"uwansa nima ai bai faÉ—a min da farko a gari na ji. Ni ko na yi irin taki ban nuna masa na sani ba."
Nima ina cigaba da ba ta labarin a wajen wata yar uwata na ji labarin. Anty Zabba ta ce na yi jarumta na cigaba da bin shi a haka na ga iya gudun ruwan shi. Hira ta ɗauke mana hankali har sai da aka kira sallar isha'i sannan muka yi sallama sai na ji zafin da ke taso min a saman ƙirjina ya na raguwa samun wanda mu ka yi hira ƙwatakwancin mai damuwa ko na ce gyambo irin nawa.

Muna gama wayar ban koma falo ba sai da na yi sallar isha'i sannan na koma falo wajen su Jidda sai na iske ma suna salla bayan sun idar nace Jidda ta ɗibo min abinci tun da ɗazu da rana ban ci ba. Da gaske ne na ji sauƙi sauƙi a cikin raina tunda har ban ma yi barci da wuri ba sai da na jira dawowan Yallabai wajen tara na dare, ina ta kallonsa ina tunanin daga wajen Gimbiya ya ke amma sai na yi saurin kauda wannan tunanin kamar yadda Anty Zabba ta ba ni shawara.

Shi kan shi na san ya ga chanji. Domin ni da kaina na haɗo masa ruwan lipto ya sha bai ci abincin ba ya ce cikinsa ya cika mun zauna da yara muna kallo har goma na dare sannan na ce su je su kwanta saboda makaranta gobe, mu kuma sai wajen sha ɗaya muka shiga kwanciya domin Yallabai ne ya ce sai ya ƙarisa kallon wani american film ɗin da muka fara kallo a MBC ACTION.
Saboda ya ga na É—an sake masa ya na ta ba ni labari ashe tun fitan shi suna tare da Uncle Abba sai daren nan suka je ya gaida Nene shi ya kawo shi gida sannan ya wuce.
Ina gyara gashin kaina na ce" Allah ya kai shi lafiya "
Su Yallaɓai an samu fuska ya na tarawan jiki duk da har ga Allah ba na cikin Mood ɗin haka nan na bashi dama, kuma daman al'adata kwana biyu ya yi ya ɗauke ni da na ke yi kwana biyar a baya. Yau ban san da me zan kare kaina ba. shi kan shi ya ɗan ga chanji domin ban yi masa wani rawan jiki ba, kar dai ya ce na yi masa kamar gunki ne ya sa na ɗan motsa masa kaɗan  na ga mamaki a saman fuskarsa amma bai furta min ba ni kuma ban bashi damar mgana ba, domin niki niki na yi da raina ina ta faman sha masa kamshi.

Da asuba ma da na ga take taken shi na son ƙarawa sai na yi masa barcin ƙarya dole ya ƙyaleni. Bayan su Jidda sun tafi makaranta ni da shi ne kaɗai a gida, Marwa ta zo kwasan sauran kayanta ita na samu ta yi min gyaran gida muna ta hira da ita tana ma gidan sai ga Saude na ce ba na ce ta zauna a gida ta warke ba sai ta ce min ai ta ji sauƙi.
Su suka ɗeɓemin kewa domin Marwa ta yi min abincin rana sai wajen ukun rana suka tafi. Yallaɓai kuma daman tun safe ya ce min yau da yamma ko da daddare ya na so zai yi mgana da ni, ina jin haka a raina na ce daga baya kenan. Sai na ji kamar ba na son jin ma abin da zai gaya min saboda ba zai zama wani sabon abu a wajena ba. Har na saka ma kaina dangana na ce zan tsaya na saurare shi ko domin na ji abin da zai ce min. Sannan ina son na san ta in da aka haihu a ragaya, to eh mana domin har yau ban ji labarin yadda wannan auran bazatan ta ya faru ba, shin daman can an shirya sa ne ko yaya abin ya ke! Bai ba ni wannan amsar ba mutum ɗaya ne ko zuwa biyu ko Yallaɓai ko kuma ita kanta Gimbiyar.

  Wajajen ƙarfe biyar da wani abu na yamma muna falo tare da Yallaɓai shi ya na aiki a saman system ɗin sa ni kuma ina kallo a Mbc bollywood domin na fahimci suna series masu kyau da ma'ana. Jefi jefi muna hira duk da ƙarfin hiran na bakin Yallaɓai ne ya na ba ni labarin aikin su na kaduna da irin alherin da ya ke fatan samu kallonsa kawai na ke yi, a baya ne in ya na faɗa min haka na ke jin daɗi amma yau sai na ji ko kaɗan ban wani damu ba, in zai lura ma ni ina ta taɓe masa baki ne labarin duk ya gundure to Allah na tuba yanzu ai komai ya samu ba nawa ba ne ni da ƴaƴana ba, namu ne har da ita kanta Gimbiyar wa yasanin ma ko da kuɗin ya ke saka ran yi mata hidima da kuɗin ma ya kawo min kishiya.

Fitsari ya tashe shi nan tiolet ɗin falo ya shiga ya kama ruwa. Ya tashi kenan ba daɗewa wayarsa da ke gefensa a in da ya tashi ta fara haske kaamar tana silet ne ina zaune amma na kasa tashi domin na daina saka ido akan wayar Yallaɓai domin tsira da kwanciyar hankalina. Duk da ina ankare da shi ni dai tun bayan faruwan auran na su ban taɓa ganin sun yi waya ba kamar ta ɗan rage kiran shi a bisa baya. Wata zuciyar ta ce min ke Sadiya in suna wayar ma za ki sani ne! Balle ma suna gari ɗaya ai suna ma haɗuwa su yi abin da a waya ma ba za su iya ba.

Tunanin haka kawai ya sa na yi tsaki mai karfi na tashi da niyyar na bar masa falon. Amma sai zuciya ta rinjaye na ƙarisa wajen wayar ina ganin tana cigaba da hasken alamun mai kiran ya kasa haƙura.

"Daughter."

Gabana ya faɗi ya yi wani raga raga, kirjina ya amsa dum! Har sai da na dafe ƙirjinan nawa saboda na ji nauyin da ya yi min na neman rinjiya na. Dai dai lokacin Yallaɓai ya fito daga tiiolet ya na daura mazugin wandon shaddan da ke jikinsa.

"Sadiya ta a taimaka a wanke min tiolet É—in mana."

Duk ƙokarina da nuna jarumta yau na kasa, me ya sa ta ke kiran shi? Ba kullum suna tare ba! Don kawai yau bai fita ba ta ganshi ba shi ne sai ta kasa sukuni sai ta neme shi! Ƙila ya fara ɗanɗana mata daɗin shi ne ba za ta iya hakura da shi ba, ina jin tahowar Yallaɓai ya na mgana amma turiri na ke ji na fitowa daga zuciyata har ina jin zafin a cikin bakina.

  "Kawai kin yi ma tiolet ɗina tawaye shi sai a yi sati ba a kalle shi ba."

Ya faɗa dai dai yana ƙarisowa wajen da na ke tsaye.

"Na ga kina tsaye! Me ya faru?
Chapter 10 · 0% Book details