Sashe 21
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri na bi bayan kiran. Bayan ta É—auka mun gaisa ta na min tsiya da cewa"Uwargida ran gida. Ko kina barci ne?
Ina É—an mirmishi kamar ta na ganina kafin na ce"Barci kuma Ya Aina? Na tashi tun safe."
Yara ta tambaya na ce suna makaranta, Yallaɓai kuma da za ta tambaye shi sai da ta yi dariya kafin ta ce" Ina Yallaɓai Ango? Dariya na saka mai sauti kafin na ce" Ya na nan lafiya. Sai dai ya ɗan fita tun safe."
Fatan dawowa lafiya ta yi masa sannan ta yi min mganar kan dalilin kiran na ta.
"Kan maganar bikin Yashe ne. Yau fa saura kwana takwas. Na fara haɗa gudummuwar ne ina kira ina ƙara tunasar da ku, kema ina jiran na ki, gwara mu haɗa da wuri mu aika musu dashi kafin tafiyar tamu."
Kai na gyaÉ—a mata kamar ta na kallona kafin na ce" Gaskiya ne. To kamar nawa nawa za mu ba da?
Ya Aina ta ce" Ban yanke ma mu mata ba. Mazan dai na yanke ma nasu, mu kawai kowacce ta kimanta abin da ta ga za ta iya ba da wa sai kawai kowa ta ba da nata."
Nan ma na ce hakan ya yi, mun rabu da cewa za ta ji saƙo tun da ina da acct lambarta sai ta ce min kar na tura a nata Atm ya yi expire sai dai na tura a na Marwa anan ta ke tara kuɗin, in ma sun gama haɗuwa ta na tunanin anan za mu yi siyayya wasu kaya duk da yadda suka ce a yi daga can haka ɗin za a yi.
Mun gama waya kuma sai ta bar ni da tunanin nawa ya kamata na ba da, acct balance ɗina na duba kuɗin da ke ciki duka duka 35k ne, shima sun taru ne da kuɗin asibitin da Yallaɓai ke ba ni, wannan zuwan da na yi ma ko na adaidaita bai ba ni ba, ni kuma ban yi masa magana ba, tun da na san ya na yi sai na saka tsarin haka a raina na cewa a ranar ƙila bashi da kuɗin ne.
Ga shi nima ina son zuwa bikin nan in na tura 30k gabaɗaya ni ba ni da kuɗin da zan riƙe a hannuna. Kuma a yanzu ba zan iya tambayan Yallaɓai kuɗi ba. Sai na ke ganin kamar komai ya tashi daga yadda na san shi zuwa wani abu na dabam. Na yi ta tunanin mafita ban samu ba sai kawai na ce zan tura 25k, ni sai na riƙe 10k a hannuna na tafiya in Yallaɓai ya ba ni kuɗin mai da sauran su na san zan samu wani abu a ciki ko da in mun je can zan iya ƙara ma mai bikin.
Amina na kira muka yi mganar sai ta ce Ya Aina ta kira ta itama jiya da daddare. Ta ce min 20k mijinta ya ba ta ita kuma ta na da 10k za ta ƙara zama 30k kenan ni kuma sai na ce hakan ya yi ta yi ƙoƙari.
"Yaya Sadiya ke hamsim za ki ba da ko? Matar Yallaɓai ce da kanta."
Ta faɗa cikin zolaya, nima sai na biye mata har kuma muka gama waya ban iya faɗa mata ga abin da zan ba da ba. Yanzu fa ba da ba ne, gani na ke yi kamar an shata mana wani dogon layi tsakanina da Yallaɓai a raina na ji ba zan iya tambayar shi kuɗi ba, ba kuma domin in ya na dashi ba zai ba ni ba. Zan iya karesa a gaban ko waye, in dai Yallaɓai na da kuɗi nima ina da shi, zai ɗauka ya bani kuɗi kawai na hidimata bayan na hidiman gida zai ba ni sama da adadin da na ce, in kuma na ce masa ina da buƙata jikinsa na rawa zai ba ni sai dai in dan bai da shi ne gabaɗaya. Na kuma san in na faɗa masa muna da biki a Yashe an yanke mana kuɗi wallahi zai ba ni kawai ni ɗin ce ba zan iya yi masa mganar ba.
Tun da yanzu ya zama ba nawa ni kaɗai ba. Na saka ma raina ya zama dole na miƙe na nemi sana'ar yi ko domin wata rana. Tunda in a baya ina tunanin daga ni sai shi sai ƴaƴanmu yanzu kiɗa ya sauya dole ma rawa ya sauya. Ya auro wata kuma in suka fara zama akwai yuyuwar su tara wasu zur'an to abubuwa da dama za su tashi daga yadda suke a baya su sauya wani muhalli yanzu.
Nan take ban tsaya ma wani cewa ko zuwa anjuma ba na tura kuɗin, nan ta ke na tura ta acct ɗin Marwa na kira Yaya Aina na faɗa mata na tura 25k ta yi ta godiya da saka albarka sai ta ke faɗa min Ma'u 100k ta turo yanzu itama ita 50k mijinta 50k, na san wacece Ya Aina ba da munafunci ta faɗa ba da dai Ya Murja ce sai na ce da gayya ne, addu'an Allah ya saka musu da alheri na yi, mun rabu da ita cewa zuwa gobe in kuɗin sun haɗu za ta je gida ta gaya ma Alhajimu sai a san yadda za a yi. A bakin ta ma na ke ji Rahila tun ranar talata za ta wuce in ji Ya Muntari a raina na ji kamar nima na shirya na bi tun daga ranar ban taɓa jin ina yin nesa da Yallaɓai ba irin yanzu, kawai ina son na je can wani wajen da zan manta da ƙarin auran sa ma'ana dai zuciyata ta samu kyakyawan natsuwa. Duk da ban tambayi izininsa ba na yanke shawaran zan shirya ina tunanin tare za mu tafi da Rahila.
Saboda ma jin haka ni da kaina na kira Rahilan a waya muka yi mgana. Ta ji daɗi da na ce mata ina ganin tare za mu wuce ranar talata ɗin. Bayan mun gama wayar da ita ina zaune ina tunanin wai ba mu da wasu ƴan'uwane daga nesa? Ko a wasu garuruwan? Ko dangin Mama ni dai na san duk suna kano ne, Alhajinmu kuma daga yan tumaki sai Yashe, ina zaune ina tunanin da a ce muna da dangi a can Lagos in na tafi sai an ganni. Sai Gimbiya ta tare Yallaɓai ya gama amarcinsa sannan zan dawo saboda ina jin kamar ba zan iya zama a gidan nan ina ji ina gani Yallaɓai na tafiya gidan wata ya na kwana ba. A cikin daren nan kishi zai iya saka ni na haɗiyi zuciya na mutu, ina zaunen nan ina faman tunane tunane Hauwa ta zo ta na ta buka get ban ji ba sai da ta kira wayana sannan na tashi na je na buɗe mata.
Ita kaɗai ta zo yara duk suna makaranta. A falon yara muka zauna na kawo mata ruwa da lemu sai soyayyen nama da dambun naman da ya yi mini saura. Sauran cincin da cake su Jidda duk sun cinye tare da Yallaɓai ni gabaɗaya ma komai ya fita kaina a bakina ma ina jin kamar na rasa ɗanɗano.
Hira kawai muke yi da Hauwa yadda ba ta min maganar ba, nima a raina na kudiri niyyar ba zan yi mata ba, daga ita har Munniran muna nan har azahar sai da muka yi salla ne sannan na É—ora mana taliya fara tunda ina da Miya, na dawo falon kenan sai ta ke ce min da wuri za ta koma gida saboda yara yan makaranta za ta je ta yi musu girki, ni kuma sai na ce sai na da fa taliyan da yawa in É—ibar mata sai ta tafin musu da shi.
Nepa sun maido wuta sai na kunna mana kallo a tashar Arewa24 suna haska wani Hausa Film, hiran duniya kawai mu ke yi da Hauwa ta É—auko min wannan na hira mu bari mu kama wancan. Kuma na lura da magana a bakin ta amma ta kasa yi min kila tana tunanin ko har yanzu ban sani ba ne.
Ni kuma daman na ce ba zan yi musu mgana ba in sun yi min sai mu yi ta kare in ba su yi min ba to sai dai a tafi a haka.
Ruwan zafin da na saka a gas ya tafasa na je na karya taliya na saka sai na kuma dawowa falon na zauna.
Hauwa ta kalleni ni kuma ina É—an cire abin taliya da ya É—an shigar min kumba.
"Anty Sadiya."
Hauwa ta kira sunana, na É—ago ina kallonta amma ban amsa ba, itama sai ta kasa ce min komai, sai na mai da kaina kan abin da na ke yi sai da na cire sannan na kalleta ina faÉ—in" Kin kirani kuma kin kasa cewa komai. Me ya faru ne?
Kai tsaye ta ce min" Wai kina so ki ce min ba ki san wani abu ya faru ba?
Sai da na juya baki sannan na ce" Ban sani ba Hauwa. Wani abu ya faru ne?
Na ƙarishe faɗa ina tsare ta da ido, mamakina ta ke yi, ko a har yanzu Yallaɓai bai sanar da ita ba?
"Hauwa me ya faru ne?
Na faÉ—a ina katse mata tunani sai ta yi saurin É—aga hannu kafin ta ce" Ba ruwana. Tun da ba ki sani ba."
Mirmishin takaici na yi ina kallon Hauwa kafin na ce" Me ye ban sani ba! Wai na auran Yallaɓai da Gimbiya?