Sashe 39
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sadiya ki sani ban aure Daughter domin kin taɓa gaza min ba. Ki kaddara zaɓin Allah ne sannan ikonsa ne. Ke ma ki sani ba ta rage ni da komai ba kar ki yi tunanin akwai ta bangaren da ta gaza min ne ko ɗaya. Ke ma ki ɗauka a kaddaran Allah ne aurena da ni da ke, ki yi mata biyayya domin wakiliyata ce, in ta yi miki gyara ki gyara in ta kwaɓa miki ki kwaɓu, in ta ba ki umarni ki bi wanda bai saɓa ma shari'a ba. Ba zan lamunci ki yi mata cin zarafi ko rashin kunya ba ba na so na ji wata baraka a tsakanin ku, Ku ba yara ba ne ballatana na ce komai sai na faɗa muku dukkanmu nan mun san komai saboda haka ina roƙon ku ku haɗe kan ku mu zauna da juna lafiya har mu zama abin kwantance a wajen su don Allah."
"In sha Allahu."
Ta sake faÉ—a ni kuma a yangance na ce" Allah ya sa."
Sai kawai ya juyo kaina.
"Sadiya."
Sai na kalleshi sannan na amsa masa.
"Na'am."
"Na ɗora miki wani girma. Ki sani ki ce ni i don ba na nan ko da ma ina nan ke ce wakilyata. Kin fi ta sanina sosai fiye da ita. Ki riƙe girman ki, ni ma kuma ki riƙe min nawa girman. Don Allah ki yi zama da ita da zuciya ɗaya in wani saɓani ya haɗa ku ku zauna ku warware a tsakanin ku kar ki biye ma masu an ce ka ce domin ya na ɓata alaqa ba na fatan ku samu saɓanin da har ni sai na shiga ciki. Na fi son ku yi zaman lafiya da har ni ba zan ji kan ku ba don Allah."
Ajiyar zuciya na sauke domin na ga ya ƙura min ido sannan na ce" Allah ya ba ni ikon ɗaukan girman."
Abin da kawai na ce kenan na yi shuru ita kuma sai ta ce" In sha Allahu ba za ka taɓa samun baraka daga bangarena ba"
"Ma sha Allah na ji daÉ—in haka. Allah ya yi muku albarka ya kuma zaunar damu lafiya gabaÉ—aya."
A cikina na amsa da Amin, ya É—an sake yin shuru kafin ya ce" Sai maganar raba kwana. Wani tsari kuke ganin za ku yi?
Ya fada ya na kallon mu, ni ko sai na yi kamar ban ji ba.
"Duk yadda Maman Jidda ta tsara dai dai ne ni a wajena."
Ta faÉ—a ta na kallona sai nima na kalleta kafin na ce" Ah ke ma kina daman ki tsara É—in."
Sai ta kalleshi kafin ta ce" To kai ka faÉ—a mana."
Kai tsaye ya ce" Ni ba ruwana wannan ai maganar ku ne."
Ya faÉ—a lokaci É—aya ya na duba wayarsa.
"Ni dai sai na ga gwara ita ta faÉ—a "
Ta faÉ—a tana kallona, nima ko ina kallonta na ce" Ke ma kina damar ki faÉ—a duka É—aya ne da ni da ke É—in"
Ganin mun fatra ja in ja ya sa ya kalleni kafin ya ce" Sadiya ki faÉ—a mana ke ce Babba."
Zan yi magana ya dakatar da ni da cewa" Ke za ki tsara na ce ko?
Sai na ga ya wani haÉ—e rai ya na kallona a raina na ce daga baya kenan.
"To kamar kwana bibbiyu ya yi ko?
Na faÉ—a ina kallon su sai ya kalli Gimbiya kafin ya ce" Ya yi ko? Da sauri ta ce" Ya yi."
Sai ya juya ya na kallona kafin ya ce" Shikenan kwana biyu ya yi Madam."
Ko kallon shi ban yi ba domin ni yaudaran Yallabai wanne ne ban sani ba.
"In ba na gidan ɗaya to haƙƙi ne a kaina na je na duba yadda ta kwana. In kuma wani uzuri ya taso zan iya kiran waya. Kuma duk wacce ke son mgana da ni za ta iya kirana nima kuma a duk in da na ke zan iya kiran kowaccen ku, dukkaa ku mata na ne da Allah ya ba ni ku ta ƙarƙashin inuwar aure saboda haka ba bu shamaki a tsakaninku gabaɗaya ɗaya kuke a wajena."
"Allah ya zaunar da mu lafiya. Madam É—ina yi mana addu'a.".
Sai kawai na yi kamar ba da ni ya ke ba sai na kalli Gimbiya ganin ta na kallona shima sai na ga ya na kallona cikin basarwa na ce" Wai ni?
Mirmishi ya yi kafin ya ce" Wace ce na ke kira Madam in ba ke ba? Sai na jinjina kai a raina na ce ai ka ce Madam tun da ka gama da ni ka yo sabuwa na zama cus ba ni da amfani dole na koma Madam ko burgeni sunan bai yi ba domin tabbas na ke da shi wulakanci ne na É—a Namiji shi ya na kiran ta da Daughrt ni kuma Madam kamar wata inyamura.
Ni na rufe zaman da addu'a sannan ya ce mu yi musabaha da juna, hakanan na mika mata hannu muka yi masabahan shi kuma ya duba lokaci ya ce goma har ta gota bari ya zo ya maida ta gida.
Shi da kanshi ya leƙa falo ya ce Baby ta yi barci sai Jidda kaɗai a gaba na ya ce ta je ta haɗo kayanta na kwana biyu ta zo su tafi kamar zan yi magana amma sai na ce ba yanzu ba ba tare da ya yi magana da ni ba ina ji ina gani ya ta sa Jidda tare da Amaryansa da ba zai bari ta kwana ita kaɗai ba ya je maida su gida. Mun yi sallama da Gimbiya kadahan kadahan Jidda kuma na ce ta tafi da azkar ɗin ta da Qur'ani kar ta manta da koyarwa da na yi mata ta ce min in sha Allahu.
Bayan tafiyarsu na kai Baby ɗaki na gyara mata kwanciya tare da yi mata addu'an barci. Sannan na rage mata hasken ɗakin na fito. Heater na kunna ya yi zafi sannan na yi wanka na saka kayan barci na duba agogo Yallaɓai ya fi mintina talatin da fita bai dawo ba, har na je kitchen na sha ruwan zafi daman da rana shinkafa na da fa Jallop. Ban damu da Yallaɓai ba tun da sai dare ya zo min gida ai ya cika cikinsa a can shi ya sa ko tunanin dafa wani abu ban yi ba. Bedroom na koma na kwanta amma na kasa barci tun ina mamakin Yallaɓai har na daina mamakinsa domin lamarinsa ya wuce tunanina da hasashena.
Ba ni na ji karan buɗe get ɗin Yallaɓai ba sai sha ɗaya da mintina na dare, saboda akwai waya a gefe sai da na duba ajiyar zuciya kawai na saki a ƙasan raina ina tausan kaina kar Yallaɓai ya shigo na yi masa dibar albarka, saboda ma kar a samu matsala sai na yi lamo cikin bargo kamar mai barci ina jin sa ya shigowarsa cikin gida da zagayen da ya yi ya rarrage hasken ɗaku nan sannan ya shigo cikin bedroom ɗin ya zube key ɗin motarsa da laptop ɗin a saman madubi ta gefen ido na ke kallon shi shammata ta ya yi ya kamani ina kallon shi sai ya yi min mirmishi kafin ya ce.
"Sorry kin ga na daÉ—e ko?
"Akwai ruwan Zafi in za ka yi wanka ne."
Na katse shi daga maganar saboda ba na son na ji. Karya ce da renin wayau ne kawai a cikin zencen sa.
"Ok."
Ya faɗa, ya na mai tuɓe kayan jikinsa ya rage daga shi sai gajerun wando sannan ya kalle ni kafin ya ce" Zan samu tea mai zafi Madam?
Ya faɗa ya na min wani kallo, da kamar na ce a can ɗin da ka tsaya ba ta ba ka ka sha ba ne? Amma dai na danne zuciyata na mike na zo zan fita ya ja min kumatuna lokaci ɗaya ya na faɗin" Na gode Matata ta kaina."
Kai na fara tunanin ƙila dai Yallaɓai ya zauce ni domin ya na ta surutai marasa ma'ana.
Kitchen na shiga na kunna gas na ɗora masa ruwan tea. Ina da shayin goriban da na siya wajen Aisha Lame saboda Yallaɓai shi na zazzaga masa na dafa masa bayan ya tafasa na tace masa a mug na kai masa ciki na iske har ya fito wanka ya na shafa mai, kan madubi na ijiye masa, kamar ina sauri na koma kan gado na kwanta sai ya juyo ya na kallona kafin ya ce.
"Ko taya ni ma shiryawa ba za a yi ba?
Ya faɗa ya na wani mini mirmishin da a baya ya san ya na kunna ni, amma a yanzu da zan fito na faɗa masa yadda na ke ganin baƙin sa in ya yi min wannan mirmishin da tuni ya kama kan shi.
Sai da na shige cikin bargo sannan na leƙo kaina ina faɗin" shirin barcin ne sai an ta ya ka?
Na faɗa ina masa wani kallo, shi wai ba shi da ganewa ne, ni fa da zai ƙyaleni da ya burgeni bai san bina ma da ya ke wani ƙara min takaicinsa ya ke yi ba.
"Da ko barcin ne ai kina shirya ni ko?
"Da ka ce yanzu kuma kiÉ—a ya sauya dole ma ruwa ya sauya."
Na faɗa ina hararan shi ta gefen ido, tsabar ma Yallaɓai ya maida ni shashashan madina sai kawai ya kwashe da wata dariya kafin ya ce.
"Me ya sauya? Uhm My Sady Baby?
Bakina ne na yi masa limzani amma na kusa na yi masa wani gimgimeman tsaki, ganin in ma tsaya ina biye masa mahaukaciya zai maida ni nishaɗi ya ke yi shi fa amarcin ya karɓe sa matuƙa sai faman washe baki ya ke yi, baya na juya masa kawai ina ƙokarin ya ƙi da abin da ke taso min daga ƙasan zuciyata ina jin sa har ya gama shirin barcin sa ya kashe mana fitila ya zo ya kwanta na ɗauka zai yi gefen sa ne sai kawai na ga ya matso kusa da ni ya kwanto saman jikina ya na kiran sunana.
"Saddy.."