← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 89

Sashe 60

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na katse mishi tunani sai ya ɗago yana kallona kafin ya ce" Alfarma zan ƙara roƙa a wajen ki."
"Ina jin ka"
"Kin san ina sonki ko Sadiya ta?
"Na san wannan ka tafi kai tsaye? Me kake son na yi maka?

"Izinin ki na ke nema."

"Izini kuma? Izinin me?

Na faɗa cikin ƙanƙance ido ina kallon Yallaɓai.

"Ina so Daughtet ta dawo gidan nan da zama"

Sai na zaro ido ina kallon shi cikin mamakin kalaman shi.

"Nufina na É—an lokaci saboda kin san dai na faÉ—a miki dokar likita ko? To ba a samu wacce za ta je gidanta domin ta zauna da ita ba. An ce ta koma wajen Nene ni kuma na ce a'a Nene ma ba ta da lafiya sai na yi tunanin duk duniya bayan iyayena ba ni da kamarki. Za ki kula da Daugther a gaban idona haka kuma za ki kulata da ita a bayan ido na shi ya sa na yanke shawaran za ta dawo nan gidan ta zauna tare damu har ta fita daga dokar likitoci."

Har ya gama mgana kallon shi na ke yi cikin mamaki. To yanzu kuma abin da ke shirin tunkaro ni kenab? Gimbiya a gidana? Ban taɓa tunanin haka ba shi ya sa na zama kawai ina kallon Yallaɓai na kasa mgana."

"Ki yi magana mana Sadiya."

Ya faÉ—a ya na matse hannayena cikin na shi.

"Me kake so na ce? Ka na so na ce a'a ne?

Na faÉ—a ina kallon shi sai ya yi saurin girgiza kai kafin ya samu zarafin mgana na tare shi da cewa" Na ce a'a mutane su je su ce kai da gidan ka na hana ka yin abin da kake so?

"Ba haka ba ne. Haƙƙin ki ne na sanar da ke. Kuma muhimmanci ki ne ya sa na ce ta zo gidan ki ta zauna tare damu."

Kallon shi kawai na ke yi na ma kasa mgana saboda mamaki.

"Aiki zan riƙa yi ma matarka Yallaɓai?

"Aiki kuma? Haba wani irin aiki kuma? Ko ni da na gina gidan nan da sunan ki na gina shi saboda haka duk wacce za ta zo ta zauna alfarman ki za ta ci. Ita Daugther rigar alfarman da kika yi min za ta shiga ciki amma in har kin ce a'a shike nan ba ni da zabi sai ta koma Rano kawai."

"Ka san zan iya cewa a'a me ya sa ka kawo mini mganar?

"Na san ma ba za ki ce Aa É—in ba ne shi ya sa."

Shuru kawai na yi ban yi mgana ba, uhm ni fa namiji ya daina mamaki ya zo ya na yaudarata da mgana yanzu na ce ban yarda ba magana ta fita a gari a ce na hana ta zama a gidan mijinta gida ba na uwata ba kuma ba na ubana ba. Gidan shi ne ya na da damar da ko kare ya kawo ya sauke ba zan yi magana ba. Abu É—aya ne ba zan É—auka cin zarafi da wulakanci. Sai na kalle shi na ga shima ni ya ke kallo ya na jiran ya ji me zan ce.

"Shike nan bakomai ai gidan ka ne itama gidanta ne."

Na faɗa ina danne wani abu daga ƙasan zuciya.
Rumgumeni ya yi daga zaunan ya na faɗin" Na gode Abar ƙaunata"
Kallon shi kawai na yi ba tare da na yi masa mgana ba.

"Amma ina da mgana."

Sai ya ɗago ya na kallona ni kuma sai na gyara zama ina faɗin" Ta zo ta zauna ban damu ko yau ko gobe ko sai ta shekara ko kuma anan ɗin ma zata zauna gabaɗaya ba. Ai gidan ka ne itama tana da iko da shi saboda haka ba ni da hurumin na ce wani abu akan haka, abu ɗaya ne ba zan ɗauka ba a zo har gidana a ce za a ci min mutumci, in hakan ya faru ba zan yi shuru ka san halina ba ni da hakuri matukar aka taɓa min mutumcina."

"In sha Allahu ba abin da zai faru. Daughter tana girmamaki ina da tabbacin ba abin da zai faru."

"To wai kar ma ya farun ne na yi mgana ka ce na cika cewa an yi min kaza."

"Ba zai faru ba in sha Allahu."..

Ya faɗa ya na min mirmishi. Hannuna na zare a na shi kafin na miƙe ina faɗin" Wani ɗaki za mu sauke ta?
"Wanda kika ce Madam"
Sai na kalle shi kafin na ce" Ko ɗakin nan nawa na baƙi? Tun da kusa ne da namu."
"Ba matsala?
"Babu mana."

"To shike nan a yi haka É—in."

Sai na jinJina kai kafin na ce bari in na gama da yara sai na shiga na dan ƙara gyara ɗakin
Sai ya riƙo hannuna na juyo ina kallon shi. Shima ya na kallona har ya na wani sauke ido.

"Na gode Abar ƙaunata"

"Yallaɓai ni kuma yaushe na koma Abar ƙaunar ka kuma?

Ya na mirmishi ya miƙe ya rumgumeni ya na faɗin" Tun a ranar farko da na fara ɗora idanuwana a kan na san cewa tabbas ke ɗin Abar ƙaunar Yusuf ne."
Ni dai ina ta dariyan yaudaran Yallaɓai saboda na yarda da zaman matarshi a gidana shi ne zai zaunar da ni ya na min ruwan kalamai. Kai jama' a Maza na abin da suke so ranar kusan raba dare muka yi muna hira da Yallaɓai da na yi magana jikinsa na rawa saboda wata macen sai na ke tunanin in da na yi boren ban yarda ba ya na gaba gaba wajen ci min mutumci ko ba a yau ɗin nan ba nan gaba sai ya yi min gori kuma dangin sa su ji labari su tsine min.

Da safe ya ke faɗa min sun yi waya da Gimbiyar an yi ma sallama saboda haka yanzu daga nan asibitin zai je ya ɗauko su. Na ce to ni kuma zan ɗan kara gyara ɗakin. Wanka ya yi muka karya tare su Jidda sun tafi Tahfeez da wuri tun da jiya ba su je ba. Ɗan gyara gidan na yi na saka turare daman ɗakin da Gimbiyar za ta zauna tun jiya na gama gyara shi daman kuma a gyare ya ke sai dai ƙura.

Karfe sha ɗaya da wani abu na safe na ji ƙaran buɗe get da shigowar mota. Ban fita ba domin ba zan iya zuwa tarban kishiya ba ai na yi iya abin da zan iya yi. Ina falon yara suka shigo Gimbiya ne da Anty Bahijjja sai Maman farko Yallaɓai daga baya ya shigo ɗauke da kayan su. Na karɓe su faram faram kamar yadda na saba na yi musu kuma jagora har ɗakin da zata sauka Maman farko na ta yi min sannu da godiya ina amsawa na je na kawo musu ruwa suka ce sun ƙoshi fita na yi na ba su waje Yallaɓai bai zauna ba ya fice tare da Maman farko da zai maida ta gida ita dai na rakata har haraba sai bayan tafiyar su ne na dawo cikin gida na yi zamana a falo can ba daɗewa sai ga Anty Bahijja ta fito ta kalleni daga sama har ƙasa kafin ta ce.

"Wai ashe kin ji haushin hana Gimbiya shan faten nan da kika yo mata ranar a asibiti Sadiya ?

Na kalleta ban yi mata mgana ba sai ta cigaba da faÉ—in" Ni ban san kin ji haushi ni fa har a zuciyata ba da wata munafa na yi ba kawai sai ga shi kin turo Tafida ya zo ya na min faÉ—a tun da an taba uwarsa ba."

"Ni ban turo shi ba."

Na faÉ—a ina kauda kaina gefe sai ta basar kafin ta ce" Koma da mene ne ni ban ce haka domin na ci zarafin ki. gwara ma ki daina jin haushina."
Mirmishi kawai na yi ban yi magana ba to me zan ce? In yi magana ta ce na zageta ko na yo mata rashin kunya..
Ta gama zagayen gidan ta koma ciki ba daÉ—ewa sai ga Naja'atu ta zo kamar kayan Gimbiyar ta je ta kwaso mata. Wajen uku na rana suka tafi lokacin har na gama abinci amma ba su tsaya sun ci ba
Anty Bahijja har ta na ƙara jadaddamin likita ya ce ko botiki kar Gimbiya ta ɗaga ta rika cin wake da abinci mai allayahu, hutu kawai ta ke bukata kuma shi za ta yi, na ji tsoron Allah tun da dai Tafida ya na ce sai an kawo ta gidana na kula da ita sosai

Mamaki bar bar ni na yi mgana ba har suka fice daga gidan. Na saki a tsaki a fili na ce" Tun da ni na yi mata cikin ba.' ko kuma ni mahaifata ba ta taɓa ɗaukan cikin ba."
Daman ni na san za a rina an saci zanin mahaukaciya ko ita Gimbiya ba ta munana min ba irin su Anty Bahijja yan kanzagi ai za su munana min.
Zuciyata na kai nesa na riƙa shiga ina duba Gimbiya ba saboda Anty Bahijja ba sai saboda Allah da kuma Yallaɓai. Na samu bayan ta ci abiinci ta sha mgani sai ta kwanta barci sai bayan la'asar ta tashi ta yi salla.

Saboda ita na yi mana Tuwon semo da miyar kuka mai naman rago tun da ta ce min ta na so. Da yamma da su Jidda suka dawo makaranta ya sa sai ga ta fito falo ma muna ta hira da ita. Sai dare Yallaɓai ya dawo yadda ya ganmu tare ya sa bakin sa ya ƙi rufuwa sai washe haƙora ya ke yi ina lura da shi. Kamar magungunanta akwai na barci ta na sha ta ce min za ta shiga ta kwanta sai na ce ma Yallaɓai ya je wajenta ya kwana saboda makirci har ya na ce min.

"Ba matsala."

"Babu."
Chapter 60 · 0% Book details