Sashe 51
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kawu sai kawai ya kashe wayarsa Yallaɓai ya kalle shi ya na faɗin" Ya haka? Me ya sa ka kashe?
"Ba ka da waya ne? Ya kira ka ta wayar ka. Ni ka ganni nan ba ni da lokaci ɓatawa a kan ku. Yauwa surukata yanzu ya za a yi ne? Kin ji dai matsaya ta."
Ina mirmishi na ce" Na ji Kawu yanzu ya kake so a yi? Yadda kace haka za a yi."
Sai ya yi shuru kamar ya na nazari ni kuma sai na ce" To ko zan kira ta ne sai mu ba ku waje?
Da sauri ya ce" A'a sai na yi mgana da magabanta ta zan fara mgana da ita.
Sai na jinjina kai kafin ya cigaba da faÉ—in" Za mu yi waya dai in na koma in sha Allahu."
Ina mirmishi na ce" Allah ya sa. Kar ka ji komai Kawu kana da ni. Kuma Marwa yarinyar kirki ce ga natsuwa ba ina yabon ta ba ne fa."
"Haba na sani. Ai na ga abubuwa da dama a tattare da ita."
Ya faÉ—a ya na shafa sajen sa, Yallabai na gefe bai saka mana baki ba amma ya na sauraran mu. Tallar hijabai na yi masa sai ya ce" Hijabai kika fara saidawa kuma?
Sai na gyaɗa masa Zaraf Yallaɓai ya ce" Ko za ka siya ma Marwatu ne?
Hararansa ya juya ya yi kafin ya ce" Ina ruwanka? Ba hijabai ba, ka san dai ko kasuwar Hijaban ne zan iya siya mata ita gabaɗaya ba ko?
"Tabbas ko mai garin Rano Allah ya ja da zamanin ka."
"To ka yi shuru. Ka jira lokaci kawai."
"Allah ya nuna mana lokacin."
Har da nima na amsa da Amin ɗin, cewa ya yi na ijiye masa guda goma na yayyensa da ƙannensa duk zai siya musu har da Innayi.
Yallaɓai na gefe ya ce" Nene ta gode."
"In kai uwarka ce ni yayata ce."
Sai Yallaɓai ya koma kawai ya yi shuru ya na danne dariyan shi, nan ta ke na faɗa masa kuɗin ya saka min ya ce na ijiye masa in zai wuce zai dawo ya ɗauka ina ta masa godiya ya ce.
"Haba bakomai an zama ɗaya. Kin fara saidawa Hijaban ne ina shagon Saloon ɗin?
Sai na yi shuru ban yi magana ba sai ya juya ya na kallon Yallaɓai kafin ya ce" Kai ya maganar shagon da ka ce min ka kama mata ƙasan offishin ka? Sai na ɗago ina kallon shi domin ni ban ma san da labarin ba.
"Na saka Musbahu a ciki sannan ai na faɗa maka na ɗauki wani yaro Auwalu. Su na gyara ma ƙasa ni kuma ina sama saboda ina so na faɗaɗa kamfanina in sha Allahu."
"Allah ya ba da sa'a. Ita kuma fa?
"Zan buÉ—e mata in sha Allahu."
Sai ya kalleni kafin ya koma ya na kallon shi lokaci ɗaya ya na faɗin" Mallam ba wani in sha Allahu. Tun yaushe ka ke alƙwari ba ka cika ba? Na san fa ba rashin kuɗi ba ne, Mallam ka samu kuɗi ka san na sani ko?
Yallaɓai ba ya son kallona kai ya kauda kafin ya ce" Ba ni na yi alƙwari ba? To zan cika in sha Allahu."
"Better domin yanzu ina bayan ta ne. Ba zan lamunci ka danne mata haƙƙi ba tsab za ka iya ji sammaci daga hukumar kare haƙƙin ɗan adam."
"Ba Shakka."
Yallaɓai ya faɗa ya na kallon shi, shi kuma ya miƙe lokaci ɗaya ya na gyara zaman hulan kan shi kafin ya ce" E haka na ce. Sadiya ba ri mu je amma zan dawo kafin na wuce."
Sai nima na miƙe ina musu fatan a dawo lafiya nan na bar su a falon suna ta halin su shi da Yallaɓai ni kuma na koma cikin gida saboda murna kamar na faɗa ma Marwa sai kuma na ce ba ri dai in yi shuru na jira ce shi kamar yadda ya ce kar na yi gaggawa amma ita kanta Marwa sai da ta ce Umma kina ta fara'a ina dariya na ce mata abin fara'an ne ya same ni.
Ba su suka dawo ba sai bayan la'asar lokacin har Marwa ta gama shinkafa da miya da salak, ta kuma gyara gidan ya na ta kamshi, shi kuma Kawu tuni na haɗa masa Hijabansa waje ɗaya kololin daman ni ya ba ma zaɓi na zaɓar masu kyan ciki, ni kaina na ƙara ma na ni da yara har da Marwa na zuwa sallar idi. Bayan sun ci abinci tare da Yallaɓai ya ce zai wuce amma zai shiga Gwamnaja ya duba Nene tare suka sake fita da Yallaɓai ina jin su da na raka su Haraba Yallaɓai na faɗin ya kawo na Nene ya kai mata ya ce ai ya san hanyar gidan haka suka fita suna ta halin su da suka saba.
Sai dare Yallaɓai ya dawo misalin tara da wani abu ashe ma a gidan ya ke ni na ma manta, ni dai ina ɗakin da yanzu ya zama wajen kwana na shi kuma bayan ya yi wanka Marwa daman na saka ta hada masa tea, a falon yara na ji su tare da su suna ta hira har na yi barci ban san lokacin da suka kwanta ba da safe Marwa ce ta yi hidiman gidan da yara har da shi kan shi Yallaɓai domin ina ciki na kulle ƙofa ko ma ya zo ba zai tarar da shi a bude ba sai da ya bar gidan sannan na fito.
Haka a daran ma lokacin da ya dawo na shige ciki Marwa kawai ya gani da yara. Tun ya na É—aukan lamarin wasa har dai ya fahimci na riga na hau dogin zuciya har ya bar gidan ya koma can ni ba na mgana da shi, ban ma yarda mun haÉ—u ba saboda ba na so ma na gaishe shi, Marwa ta koma gida ni kuma ina ta zaman jiran Kawu amma shuru sai dai na yi ta saka ma abin albarka na yi addu'an in da alheri Allah ya tabbatar tun da na gama al'adata har na yi wankan tsarki tun jiya.
Hijabai sun ƙare na ci kasuwar salla, na yi magana za a kawo min wasu amma sai bayan salla har Ma'u ta aiko Zainab ta karban musu guda biyar, har Baaba ta siya mawa kuma Alhamdulillah ina samu sosai ɗan riban da ba za ka raina ba.
Har Yallaɓai ya sake dawowa gidana ba na masa mgana. Rana ta farko bai neme ni ba sai ana biyu shima na son saboda matsowan sallah ne, ina ɗakin da na mai da shi nawa da daddare Jidda ta shigo ta ce wai Abban su na kirana a falon shi, kamar na yi fuska na ƙi zuwa sai na fasa na tashi na saka mayafi na fita falin na same shi zaune ya na kallo amma ga wasu manyan lodoji a gabansa kamar na wani tambarin kamfani amma ban tsaya na duba ba.
Sannu da zuwa na yi masa ya amsa yana kallona ni kuma sai na kauda kaina a tsaye na tsaya ban ko da niyar zama.
"Madam ki zauna mana."
In dai Yallaɓai ya san ya tafka rashin kirki ya iya kame kame, in ka ji ya na cewa Madam ya cuce ni ne zai yi min ƴar murya. Kamar ba zan zauna ba sai dai na dofana ɗuwawuna a saman kujeran da ke gefensa.
Shuru na wani lokaci ya kasa mgana kunya duk ta kama shi.
"Har na fara barci Jidda ta taso ni."
Na faÉ—a ina kallon shi fuskata ba Annuri sai ya nuna min ledojin gaban shi kafin ya ce" Na ku ke da yara"
Abin sai ya ba ni mamaki, amma ban yi magana ba na sunkunya na jawo ledojin ina dubawa na ga dai abaya guda biyu ta manya sai na yara sai takalma sai kuma pakiatan na yara na su Jidda kenan sai reborn da man kitso da É—an kunnaye.
Ban tambayi daga ina ba kawai na maida su leda ina faÉ—in" Mun gode Allah ya sa albarka."
"Amin. Rigunan da takalman ni na siya muku Daughter ta yi oder din su daga Epgyt sai na ga sun yi mini kyau sai na ce a cire muku sauran kuma ita ta ce na kawo ma su Jidda su yi kwalliyan sallah."
"Allah ya saka da alheri."
Na faÉ—a kai tsaye sannan kuma na mike nan na bar masa kayan zan wuce sai ya kira sunana.
"Sadiya."
Sai na juya ina kallon shi, ni ya ke kallo kur kafin ya ce" Ki dawo ban gama mgana da ke ba."
Sai na koma na zauna ina kallon gefe ina jin sa ya na mirmishi kafin ya ce" Uhm Halimatussadiya. Sadiya ta Yusuf shi kaÉ—ai duk fushin ne ba a gama ba?
Kamar ya na mgana da dutse ko motsi ban yi ba.
"Ya mganar shirye shiryen salla? Me kika shirya ne?
Sai na kalle shi kafin na ce" Shiri ai ya na hannun ka."
"Ke fa? Ai mun saba ke ce ke shirya komai."
Kallonsa kawai na yi ban yi mgana ba da dai ya ga ba yi zan yi ba sai ya gyara zama ya na faɗin" Lokaci ya ƙure ku yi hakuri na so na ƙara muku kaya ko ɗaya ne."
Ban ce masa komai ba sai ya cigaba da faÉ—in" Musbahu zai kawo cefane, sannan zan yi layya ke ma zan yi miki in sha Allahu."
"Allah ya saka da alheri."
"Amin My Sady."
Ko kallon shi ban yi ba sai ma na ce" Ka gama mganar zan iya tafiya?
Sai ya gyaɗa min kai na miƙe zan tafi ya sake kirana bayan na juyo sai ya ce" Ba ki ɗauki kayan ba to."
Shi ya sa na koma na É—auka na bar masa falon na kuma san ya bi ni da kallo, a É—aki na je na zube kayan na yi kwanciyata da safe ma ranar shi ya kai yara makaranta suna ta murnan za a ba su hutun salla.
Ban masa mgana ba na ga ya turamin kudi a acct É—ina sai ga kiran shi na É—auka muka gaisa.
"Na kitso ne da kunshi. Ke da yara."