← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 89

Sashe 46

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin haka ya sa kawai sai na ɗauro alwala sai da na fito ne na duba lokaci a wayata na ga 2 saura ne na dare. Sai kawai na ɗau casbaha ta na koma na kwanta. A kwancen ina ta hailala da salatin Annabi a hankali a hankali kuma sai na samu sauƙin zuciya har barci ya kwashe ni ban sani ba. Kuma mai nauyi ne domin har sai da Yallaɓai ya tashe ni da asuba bayan ya dawo masallaci ya ga ban tashi ba, ban ce masa ina hutu ba sai kawai na tashi na shiga tiolet. Da safen nan da na gaishe shi a daƙune ya amsa kamar na yi masa wani abun nima ko ina ganin haka na kama kaina. Ina ma fama da kaina marata kamar za ta cire saboda yadda ta yi min nauyi sosai.

Daƙyar na yi ma su Jidda breakfast suka tafi makaranta. Shima dai tea kawai ya sha ya yi wanka ya fita ya bar ni ina ta mutsu mutsun ciwon mara sai da Saude ta zo ne na saka ta dafa min ruwan zafi da Hulba na ɗan sha sai maran ya ɗan yi min sauƙi. Sake kiran Dr. Aisha na yi shima ɗin ba ta ɗauka ba, sai na yi mata uzuri tunda ita likita ce mai harka da jama'a ba lalle ta na da lokaci ba sai kawai na yi tunanin ya kamata gobe na shirya na je asibitin matsalan ba lalle ne ma in na je a goben na samu ganin Dr. Aishan ba.

Haka na yini a gida kwance ban da lafiya. Ban kuma kira kowa ba yadda Yallaɓai ya fita bai iya tambayata me ke damuna ba saboda ai ya ganni sukuku shi ya sa nima ban neme na faɗa masa ba. Kuma tunda ya fita bai kirani ba nima ban kira shi ba, girki ma Saude na saka ta dafa kafin ta tafi ni a ɗaki na yini ina shan ruwan zafi domin na gasa marata. Sai can da yamma na ga saƙon Dr Asha ta ce bakomai na cigaba da shan mgani kaɗan kaɗan komai zai dai daita ciwon maran kuma da na ke yi sakamakon na kan ɗan daɗe ban yi al'ada ba ne kuma cuta ne a acikin jinin da ya ke fita shi ya sa zan ɗan riƙa fuskantan ciwon mara a farko farko amma ta ba ni tabbacin in na cigaba da yi duk wata zuwa nan gaba kaɗan ba zan riƙa fuskantan haka ba. Itama ta ce na riƙa shan ruwan zafi a kai a kai in sha Allahu zan samu sauƙi kuma na samu ɗin Alhamdulillah tunda har na samu na yi wanka a daren na sauya kaya sai dai fuskata duk ta kumbura har da ma kafafuna sai da na ɗan shafa mata man zafi.

Yau ma Yallaɓai sai around 11 na dare ya shigo gidan. Yara har sun yi barci nima na fara barcin marata ne ya ƙulle sai na tashi na shiga tiiolet a lokacin ya shigo gidan. Yadda na iske shi zaune ya na duba wayarsa fuskar ba alamun rahama ya sa ban neme shi da wata mgana ba bayan sannu da zuwa.

"Yauwa."

Haka ya amsamin kamar na yaɓa masa wata mgana mara daɗi. Sai na yi shuru ina ƙoƙarin danne zuciyata.

"Abinci fa?

Bai kalleni ba hankalinshi na kan wayarsa ya ce" No am ok."
Sai kawai na wuce na koma na kwanta na rufe ƙafafuwana zuwa cikina da bargo na juya masa baya ina ƙoƙarin danne tasowan wani ƙunci daga ƙasan zuciyata.

"Ba ki je Gwamnaja ba yau?

Ya tambayeni, ina daga kwancen na amsa masa da cewa E ban je ba.
Sai na ji shuru sai ni ce na juya ina faɗin" Ai na ga Nenen ta ji sauƙi sosai."
"Ta ji sauƙi Alhamdulillah."
"Allah ya ƙara mata lafiya."
Ya amsa min da Amin Amin daga nan ya tashi ya fice nima na juya na gyara kwanciyata ina ƙoƙarin danne komai na nuna komai ba komai ba ne daga saman fuskata amma a ƙarƙashin zuciyata kwata kwata ba daɗi.
 
Washegari da safiyar Talata ya na gida bai fita da wuri ba yana ta aiki a laptop ɗin sa ni kuma ina cikin ɗaki a kwance. Yadda bai tambayeni me ke damuna ba, nima ban faɗa masa komai ba ai ya na da hankali tun da ya ga ina kwanciya ai ya san ba lau ba, amma mutumin nan ko a jikinsa sai ma wanka da ya yi ya shirya cikin manyan kaya ya fice ya bar ni kwance cikin yanayi mara daɗi. Ban taɓa tunanin akwai wata rana da Yallaɓai zai ganni kwance bai fara rawan jikin tambayana lafiya na ke kwance? Me ke damuna? Amma yau sai ga shi kwana biyu ina kwance ban ji daɗi ya fice ya bar ni ko a jikinsa lalle na fara yarda ina da abokiyar zama. Ba ni kaɗai Yallaɓai ke da shi ba, shi ya sa yanzu ba zai cika damuwa da ni kamar a baya ba. Sannan na lura da wani abu tun kwanciya Nene asibiti bai neme ni ba sai ranar da ta dawo gida shima tun daga ranar har yau bai ƙara nema na ba, ni da na san Yallaɓai da bama ɓarnan ruwa muhimmaci amma yanzu kwata kwata ba ya nuna sha'awar haka, ko na daina burge shi ne ban sani ba? Wata zuciyar ne ta faɗa min cewa yanzu ba da ba ne ya na da wata matar, in ma ni bai neme ni ba ita ba zan ba da tabbacin bai samu natsuwa daga wajenta ba.

Ina kwance ina tunanin nan sai ga kiran shi, ina ɗauka bayan mun gaisa shima gaisuwan ni na gaishe shi ya amsa sai ce min ya yi na shirya na je Gwammaja na sake duba Nene ni kuma ban ce masa komai ba na ce to. Na ɗauka zan ɗan rarrafa na je amma kuma sai na kasa gabaɗaya jin jikina na ke yi kamar ba nawa ba, sannan ni ba na so ma ina fita in ina cikin wannan yanayin ganin dai ba zan samu zuwa ba ya sa na yi ƙoƙarin neman wayar Yallaɓai na faɗa masa ban da lafiya amma ban samu wayarsa ba, ban yi tunanin rashin zuwan nawa zai iya zama matsala ba, ban kuma taɓa tunanin Yallaɓai zai iya min fahimtar a bai bai ba.

Ranar Saude ma ba ta zo ba ta je makaranta Marwa na kira ta ce tana asibiti sai 2 na rana za ta dawo sai na ce ta biyo ta gidana ba na jin daɗi. Ita ta zo ta gyara min gida sannan ta yi ma su Jidda girki, ita da kira Ya Aina ta faɗa mata cewa ta na gidana ba na jin daɗi har ta ba ni ita ma muka gaisa ta na faɗan ban da lafiya amma ban faɗa ma kowa ba? Sai na ba ta haƙuri da cewa ba wani ciwo sosai ba ne shi ya sa ban ɗaga musu hankali ba, ita kuma Ya Aina ta kawo maganar cewa daman kwanan biyun nan duk kowa ya ji ni shuru na ce ina nan lafiya ba wani abu ba ne mai tsanani kar ta ɗaga hankalinta. Mun rabu da cewa Marwa ta kwana nan tun da ban ji daɗi na ji daɗin haka tun ballatana da Marwa ta ce Gobe ta na da hutu sai jibi ta ke da aikin dare sai na ji daɗi ko banza za ta ɗebemin kewan zaman gidan ni kaɗai.

Yallaɓai da wuri ya dawo wajen tara na dare. Sai kuma ni da kaina na zauna ina nazarin wani abu. Kwana biyu ya ke yi in ya fita ya na kaiwa dare a Gwammaja kwana biyu kuma sai ya riƙa dawowa da wuri kuma har ya ci abinci sai zuciyata ta zargi kamar ya na raba mana kwana ne ni da Gimbiya duk da ta na can Gwammaja, saboda sai na ga kamar tsarin da ya ke bi kenan ban yi masa maganar rashin zuwana can Gwammaja ba nima kuma bai yi min ba kuma ko da ya ga Marwa a gidan bai damu da ya ji dalili ba sanin daman ai yar gidana ce ta na zuwa sosai shi ya sa hankalin shi bai kawo masa wani abu ba.

Allah sai ya taimakeni washegari na tashi garas kamar ba ni ba, Marwa ta na nan sai yamma ta shirya ta tafi asibiti. Ranar dai mun yi azkar tare da su Jidda har na yi musu karatu ban dai ɗauki Qur'ani ba ne tunda ba ni da tsarki. Domin na ƙara samun tabbaci a kan sabuwar daɓi'ar Yallabai ya sa ban yi barci da wuri ba kuma illau ranar ma da wuri ya dawo na gabatar masa da abinci ya ci ya yi wanka, sannan sai ya jima ya na aiki a loptop har na yi barci na bar shi bai gama ba, washegari na sake zura masa ido sai ya maimaita abin da ya tsara bai shigo gidan ba sai sha ɗaya da rabi na dare ta ma gota ban yi barci ba a raina daman na kudri niyya sai na yi masa mgana saboda a daran na kira Nene na gaisheta na ba ta haƙuri na ce ban ji daɗi ne shi ya sa ba ta ganni ba sai ta yi min sannu ta ce ba ta sani ba domin ba su yi maganar da Tafida ba.

A lokacin na ji maganarsa a ɗakin Nene da na wasu amma ban ɗauki muryan kowa ba sai na shi, kuma a lokacin ko tara bai yi ba kenan a can ne ya ke kwashe lokaci mai tsawo shi a dole mai Mata kawai sai na saka a raina sai na yi masa mgana. Gwara ya riƙa kwana a can duk ranar girkin Gimbiyar in Adalcin ya ke son ya kamanta dakyau, ni ba ma wani amfani ya ke yi min a gidan ba, gwara ya riƙa tsayawa can ya na kwanan shi zai fi sauƙi da wannan ciccin mganin da ya ke dawowa gida ya na yi min ba tare da na san laifin da na yi masa.
Chapter 46 · 0% Book details