Sashe 57
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Maman Farko ce kawai ta sakar min fuska to sai Yallaɓan amma Anty Bahijja ina gaishe ta ma kamar ina faɗa mata cuta a daƙune ta amsa ni. Na zo na iske an kai Gimbiya ɗakin hutu an yi mata kuma alluran barci amma ba su fara ba da izinin a shiga a ganta ba.
Muna asibitin Anty Bahijja ta kira mutane ba adadi ta na faÉ—a musu Gimbiya na asibiti ina ga ko suna tambayan ta cikin ne? Sai ta É—aga murya ta na faÉ—in.
"Ciwon mara ne ya turƙeta. Cikin na nan ba abin da ya same shi amma sun ce za su ba ta bedrest ta huta sosai."
Ni dai ina gefe zaune kusa da Maman farko Yallaɓai ya tafi gida ya je ya yi wanka ya dawo. Ita Nene da Maman farko suka yi waya ta na faɗa mata halin da ake ciki, bayan sun gama ne ta kalle ni zaune da kwandon da na sako kayan tea da ruwan zafi a gabana kamar wata marainiya sai ta kira sunana na ɗago ina amsawa.
"Sannu da ƙokari Sadiya."
Sai na amsa ina jinjina mata kai. Ai dole ta gaisheni na zo asibiti na yi zaman dabas saboda kishiya amma sai na duba Yallaɓai da ita kanta Gimbiya sai na saka a raina zan yi domin Allah domin kirkinta saboda ana ganin ban zo ba kafin kowa ya yi magana Anty Bahijja za ta fara yi da ni. Kafin kace kwabo an cika asibitin nan ni dai bayan azahar na koma gida tun da har lokacin ba ta farka ba kawai sai na yi musu sallama na koma gida Yallaɓai kuma ya dawo asibitin amma ya sake fita ya ce akwai mutane a office suna jiran shi sai da ya dawo da daddare ya ke faɗa min Gimbiya ta farka jikinta da sauƙi.
"Allah ya ƙara mata lafiya."
"Amin Amin."
Sai na kalle shi ganin ya yi wani shuru haka ya na cin abinci sannu sannu.
"To wa zai kwana da ita?
"Maman farko aka bari da ita."
Sai na jinjina kai ban yi magana ba amma a raina sai na ɗauka ai Anty Bahijja ce za ta tsaya ta kwana yadda ta ke nuna kamar ita ce ta haifi Gimbiyar ma. Washegari ma da safe yara na tafiya makaranta tare muka tafi asibitin da Yallaɓai ni na kai ma Maman farko abin karyawa har muka iske Gimbiyar ta na kwance amma idanunta biyu.
"Sannu ya karfin jikin?
Ta na ɗan mirmishi ta ce" Da sauƙi Madam ina su Jidda? Sai na ce suna makaranta amma sun ce a gaisheta ta amsa ta ɗan yamutsa fuska. Ni da Maman Farko waje muka fita muka ba su waje muna ta ma hira da ita. Ta ce min ai ta ji sauƙi matsalan ba ta son cin abincin Tea kawai ta sha jiya kuma a jiyan ta amayar dashi.
"Topha. Subhanallah to yanzu me ta ke son ta ci?
"Ban sani ba. komai a ka ce sai ta ce ba ta ci. Laulayin ta mai zafi ne sai dai fatan Allah ya sa a rabu lafiya."
Na amsa da Amin Amin ban wani daɗe ba. Amma dai anan Yallaɓai ya bar ni ya tafi office ni kuma zuwan Anty Maimuna ya sa na yi musu sallama na koma gida da daddare ma na yi girki na ce Yallabai ya ɗauka ya kai ma Maman farko bayan ya je ya dawo shima ƙorafin da ya ke yi min kenan na rashin cin abincin Gimbiya sai na bashi shawaran ya samu likita da mganar. Ɗayan washegarin da safe ban koma ba shi kaɗai ya tafi da abin karyawa bayan ya dawo ne ya ce likitan ya ce masa ya tambayeta ko akwai wani abin da ta ke so ne in ta faɗa sai a dafo mata shi a kawo mata, ya na faɗa min ta ce ita faten tsaki ta ke so mai yakuwa.
"Ikon Allah.."
Na faÉ—a ina kallon shi.
"Wallahi wai fanten yakuwa."
Ina Æ´ar dariya na ce" Ina ko da bushasshiyar yakuwa da mai kitsona ta kawo min tsaki ma kamar ina dashi."
Sai ya kalleni nima shi na kallah ban yi magana ba saboda na ga kamar ya na so ya yi magana.
"Yallaɓai."
"Uhm"
Ya amsa a ƙasan maƙoshi ya na zaune a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ni kuma zaune na ke a hannun kujeran.
"Mene ne? Ko kana son wani abu ne?
Domin sai na ga kamar ya na so ya yi magana amma kuma ya kasa furta abin da ke zuciyarsa.
"In roƙe ki alfarma?
Sai na gyaɗa masa kai kafin na ce" Ba alfarma tsakaninmu Yallaɓai sai dai mutumtatawa da martabawa. Ka yi umarni kawai zan yi maka duk abin da kake so in dai bai saɓa ma shari'a ba."
Kai ya jinjina kafin ya ce" Ina so in ce ki taimaka ki yi ma Daugther faten don Allah sai kuma na ji kamar ina jin kunyar ki "
Ya faÉ—a ya na kallona nima shi na kallah amma ban yi magana ba.
"Don Allah Sadiya ta."
Sai na basar ina Æ´ar dariya kafin na ce" Haba miye na wani don Allah? Zan yi mata in sha Allahu."
"Na gode. Allah ya yi miki albarka Abar ƙaunata."
Na amsa da Amin shi kuma sai ya ja hannuna ya na sumbatata. Bai jima ba ya yi min sallama ya fita har a cikin zuciya ban ji kishi ko wani abu ba da zuciyata ɗaya na yi ma Gimbiya faten nan da yamma yara suna dawowa makaranta na ce su shirya tare da su za mu je asibitin su gaishe da Antyn su saboda in dai na je sai ta tambaye su. A waya na kira shi na ce ya dawo da wuri na gama sannan mu tafi da yara asibiti tun a cikin wayar na ji muryan shi cikin farinciki bayan kuma da ya dawo bakin sa ya ƙi rufuwa. Bini bi ni sai ya yi ta min godiya na ce kar ya damu ai mun zama ɗaya.
A daran muka je asibitin ni da shi da yara na kai mata faten mun iske ma Maman farko da Nene wanda suka zo tare da Hajiya da Musbahu anan ne na ji suna hiran mutanen Rano sun zo amma ba wacce ta kwana sun ce komai Gimbiya ta ke bukata ta samu ba amfanin zaman su ni ko a raina na ce ba shakka ita da ta ke da uwa a gindin murhu ai ba ta da matsala. Gimbiya ta ji daɗin faten nan ta sha da yawa ta rage ta ce na safe ne har da Nene a masu yi min godiya saboda Yallaɓai ke ba da labarin ya na zuwa ya faɗa min Gimbiya na son fate sai na ce ina da tsakin da yakuwa na kuma ce zan yi.
"Sannu Sadiya kin kyauta."
In ji Mimisco.
"Ai Sadiya ba ruwanta nima nan kullum safiya ita ke fara kawo min abin karyawa da daddare ma za ta ba ma Tafida ya kawo min kuma sannan kullum sai ta zo asibitin nan."
"Gaskiya ta kyauta. Allah ya ƙara muku zaman lafiya."
"Amin Amin."
Aka amsa gabaÉ—aya. Nene ce sai daga baya ta yi magana bayan na yi mata gaisuwan ta na dabam ina tambayan jikin ta.
"Jiki da sauƙi na gode Sadiya da kulawa."
"Allah ya ƙara miki lafiya."
Ta amsa da Amin kafin ta ce na sunkuyo sai na duka a gabanta abin da ya sa hankalin waÉ—anda ke É—akin ya dawo kan mu kenan
"Sadiya."
"Na'am."
Na amsa ina mai kallonta kawai sai ta bubbuga kafaÉ—ata ta na faÉ—in" Na gode Sadiya. Daman na faÉ—a miki ina da kyakyawan tsammani a kan ki sai gashi ina ta ji da ganin abin da daman na yi tsammani daga gare ki."
Mirmishi kawai na yi ba tare da na yi magana ba sai kawai ta ƙara dan buga kafaɗata kafin ta ce.
"Allah ya yi muku albarka gabaÉ—aya."
Na amsa Amin a hankali suma na ɗakin suka amsa da Amin Amin sannan na tashi. Ina ɗagowa muna haɗa ido da Yallaɓai sai ya yi min mirmishi nima na mayar masa. Gimbiya kuma ta na tare da Baby a saman gadon suna ta hira.
"Ke Baby sauko kar ki danne Antyn ta ki mana."
Na faɗa ina kallon su da sauri Gimbiyar ta ce" Ƙyaleta ai ba ta matse ni ba."
Maman farko na dariya ta ce" Ina ruwan Maimunatu ba ruwanta dai ba irin Jidda ba ce ita akwai baki "
Mimisco ta ce" Jidda Tafida ne in suka so hira suna yi in suka so miskilanci suna yi. Baby kuma ta wani bangaren Sadiya ne ta wani bangaren ta É—auko hallayan mai suna domin Maimu ma akwai surutu."
GabaÉ—aya muka yi dariya kuma haka É—in ne, domin Anty Maimuna akwai mgana ita Anty Bahijja shisshigi ne da saka ido, muna asibitin har wajen goma har su Nene ma sai da suka riga mu tafiya da za mu tafi Gimbiya ta kalleni ta na faÉ—in" Na gode Madam. Faten ya yi daÉ—i"