Sashe 35
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina ta jiyo karatun ki É—azu."
Sai na mirmishi kafin na ce" Wai har kin jiyo?
Sai ta gyaÉ—a min kai kafin ta ce" Nima da na kasa barci, fitan ki na ji ya sa bayan kin fito da ga tiolet É—in nima na tashi na shiga na É—auro alwala na yi nafiloli."
Sai na jinjina mata kai ban yi mgana ba itama kuma sai ta ta da salla, Rahila daman sallar ta ke yi lokacin da na shigo. Fita na yi zuwa ɗakin su Jidda suma sun ta shi manyan sai yaran ne ke ta barci ni na ta da Baby ta na mutsike ido na ce ta shiga tiolet ta wanke ido ta yo alwala, na fita da cewa in na idar da salla zan dawo mu yi azkar, haka ko aka yi ina idar da salla na koma ɗakin yaran na tattara su gabaɗaya baƙi da yan gida har da su Saude, na ce mu fara karanta azkar da karfi a tare, bayan mun gama na ce kowacce ta ɗauko Qur'ani mu yi karatu. Ni ce fa har wajen bakwai na safe a ɗakin yaran sai da na yi musu karatu gabaɗaya har Marwa sannan muka shiga kitchen tun da ta ce min yau za ta je asibiti, ta re da saude mu uku muka ɗan gyara kitchen din sannan na ce su fere doya a soya sai kunu da za a dama a yi ƙosai Rahila ce ta fara tasowa ita ta karɓe ni daman kunin Saude na gyaran wake Marwa na fere doya.
 Daga baya har Sameena da Farida sun fito sai aka kama gabaɗaya aikin, kafin lokaci an gama tunda hannun da yawa. Mai son shan kuni ya sha in tea ne ga shi nan in ƙosai ne ga shi nan, in kuma doya ne duk dai ga shi nan bayan an gama karyawa sai suka gyara min gidan su Rahila kenan yara kuma Saude ta yi musu wanka su Jidda kuma da suke manya suka yi ma kansu. Ni kaina tun safe na yi wanka na saka cikin sabbin atamfofina, zuwa azahar kowa ya yi wanka ya shirya har na fara kewa aka ce baƙo raba duk yau ɗin za su ta fi su bar ni ni kaɗai daɗin abin ma yara sun samu hutun makaranta kaɗaicin ba zai yi min yawa ba.
Da rana Tuwo aka yi miyar agushi ina da sauran manshanu sai aka juye shi sai ƙashin naman ragon ragowan na jiya aka yi amfani da shi, akwai ma ragowan waina da safe Rahila ta ɗumama ta saka masa siga ta sha da kuni da safe, alele daman ragowan balaraba na kwashe ma sauran da za ta wuce gida na ce ta kaima yara ban bari abinci ya kwanan min a gida ba. Sai da aka ci abincin rana sannan Farida ta yi shirin tafiya tun da ta ce Tariq ya kira ta ya ce ta je Gwammaja daga can za su wuce Sameena ma can Gwamnajan za ta je shi ya sa suka shirya za su tafi tare. Na yi musu godiya ƙwarai da karamci na yi musu rakiya har haraba gidan muka rumgume juna ɗaya bayan ɗaya.
"Na gode sosai. Allah ya mai da ku gidajen ku lafiya."
"Haba. Bakomai a yi ta dai hakuri a kauda kai Allah ya zaunar da ku lafiya ya kaÉ—e fitina."
Farida ke faÉ—in haka ni kuma ina amsawa da Amin Amin, Sameena kuma hannuwana ta rike kafin ta ce" Matar Baba ni fa ba na jin ki, sannan Baba ma ya na sonki zuwan wata ba zai rage ki da komai ba in sha Allahu." Sai na yi mata mirmishi kafin na gyaÉ—a kai ina faÉ—in in sha Allahu.
Ga su dai suna na kusa da Gimbiya amma ni sun nuna min ƙauna ƙwarai kuma na yi ta musu godiya na kuma yaba da karamcin su.
Sun tafi ba daɗewa sai ga Hauwa da Munnira suka ce suma daga Gwammaja su ke, suka leƙo ni kafin su wuce gida har ina musu tsiyan ko daga gidan Amarya suke?
Munnira na tabe baki ta ce min" Wani gidan Amaryan! Allah ya kyauta. Mu ba ma mu ce za mu je ba, masu zuwa dai sun je tun jiya yau ma da na ji wasu na mganar komawa Anty Bahijja ta hana ta ce a bar Amarya da ango su huta kar wanda ya je domin ya dame su."
Cikin mamaki na ce" Topha. To su waye daman ke son zuwa?
"Can dai ahalinsu na Rano ne. Naja ce kawai aka ce za ta je itama sako za ta kai mata. Wai kar a dame su ki ji fa."
Munnira ta faÉ—a ta na kallona, muna zaune daman a falon yara ne sai kawai na jinjina kai kafin na ce" Ba shakka." Hauwa dai na gefe sai ta muskuta kafin ta ce" Su Ayshe tun safe suka koma É—azu da muka yi waya ta ce min tun jiya Anty Bahijja ta ce duk wanda ke son ganin gidan Amarya ya je a jiya domin in Ango ya shiga É—aki ba mai yi musu sintiri a dame su. Na ce kamar wata budurwa? Anty Bahijja akwai kambama abu wallahi."
Ina ta dai kallonsu amma ban yi magana ba, Munnira ta ja tsaki kafin ta ce" Ita ce uwar Gimbiyar ba ki ga alama ba? Gani na yi hiran ta su za ta iya dawo min da damuwar zuciyata ya sa na katse hiran su da tambayan ko a zubo abinci? Sai suka ce sun ƙoshi amma ƙila kafin su tafi su ɗan taba tunda tuwo ne, muna tare da su har Yamma, suna ma gidan Ya Muntari ya zo ɗaukan Rahila da yara. Na matsa masa sai da ya shigo har falon Yallaɓai muka gaisa na kawo masa ruwa ya sha har su Jidda suka zo wajen sa suna masa hira ya na biye musu, shi daman akwai son yara in dai yara ne haka za ka gan shi da su ya na biye musu ba ruwan shi.
"Ashe kuma kin samu abokiyar zama?
Ya faɗa ya na kallona, kaina na ƙasa sai na gyaɗa masa kai.
"To sai haƙuri Allah ya zaunar da ku lafiya ban da dai ɗaukan zuga."
Na ce in sha Allahu, har ya na min tsiya wai Allah ya ƙara min haƙuri domin ya san halina ba ni da haƙuri.
"Kai Ya Muntari."
Na faɗa ina ƴar dariya, shima dariyan ya ke shi da Rahila ya na ce min ai ya san halina, kamar kar Rahila ta tafi amma ina ji ina gani ta wuce gida ita da yara ni da Amina har waje muka raka su, da Amina ta so ta je Ɗorayi ta kwana yau na marairaice na ce ta bari gobe da safe don Allah sannan ta yarda ta zauna na ce sai ma ta tafi tare da Saude kawai. Su ma su Hauwa suna yin sallar mangariba suka yi min sallama suka wuce mun rabu akan zan bi su har gida na yi musu bangajiya sai gida ya rage daga ni sai Amina sai Saude sai yara.
Nima sallar mangariban na yi sannan na natsu a ɗaki wayata tun safe ta na saman gado ban bi ta kanta ba sai da na gama azkar sannan na tube hijabin jikina na yi zaune gefen gado sannan na jawo wayar ina ganin an kirani, da ya ke a silent na saka wayar kuma ban bi ta kanta ba. 7 missed calls aka yi min Yallaɓai huɗu ya yi min sai Anty Zabba da ta yi min guda biyu sai wata lamba da ban san ko ta wacece ba sannan ga sako na an turamin tun kafin na buɗe jikina ya ba ni Yallaɓai ne shi ya sa ban yi ma rawan jikin buɗewa ba, sai da na kira Anty Zabba muka yi magana ita ke faɗa min ta ga hotunammu ni da Yallaɓai su Suwaiba sun ɗora a waya mun sha kyau.
"Sadiya gaskiya kin burgeni ba domin kar a ce na so ki na ƙi amarya ba. Da na ce ko da ranar auranta ne amma kin fita kyau."
Ina ta dariya na ce" Kin ko so ni Anty Zabba. Amma ina ni na fita kyau?
"Allah da gaske na ke yi. Kun yi kyau sossi dukkan ku. Allah ya ba ku zaman lafiya da hakuri da juna."
Ba mu jima muna mgana ba muka yi sallama, ni ban ma da hotunan ban ko hau online ɗin ba ballatana in gani, ba na ma som hawa domin na san sun ta ɗora na Gimbiya da Yallabai ni kuma ba na son ganin abin da zai ɓata min rai shi ya sa na haƙura da kunna data sai ƙura ta lafa.
Sai da na kira lambar da aka kirani na ga ba a ɗauka ba sannan na duba saƙon Yallaɓai, saƙon har guda biyu ɗaya da safe ne ya turomin wajajen goma na safe ɗayan kuma da yamma nan ne, kamar yadda kiran na shi suke a jere. Biyu da safe biyu nan kuma da yamma nan ne ya sake kira.
"Good morning My Darling Wife! Kun ta shi lafiya? Ina kewar ku. Ki gaida mini da Jidda da Baby."
Sai ÆŠayan kuma cewa ya yi.
"Sadiya ta kuna lafiya ko? Gobe in zo na duba ku? Na kira ba ki ɗauka ba ko har yanzu akwai baƙi ne a gidan?
Hmm! Kawai na ce a ƙasan maƙogwaaro na saboda na kasa ma mgana. Wai My Darling Wife Yallaɓai ne har da sauya min suna mai daɗi haka, wai munafunci irin na ɗa Namiji ya kwana da wata macen amma yana ce min wai ya yi kewar mu. Sannan tambayarsa ya zo ya duba mu sai da na ja mata tsaƙi, to yaushe namiji yaushe ya fara neman izinin in zai yi wani abu? Lokacin da ya yi auran ai bai gaya min ba. Sai na zuwa duba mu ne zai turo min wani munafunci, da na so na yi banza da saƙonni ne sai na fasa na rubuta masa gajeren saƙo ina yi ina hararan wayar kamar shi ne a cikin ta.
"Muna nan lafiya. A'a ka yi zaman ka kawai ba gobe ba."