← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 89

Sashe 18

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ƙara kiran sunana na amsa ina kallonta sai ta nuna kanta kafin ta ce" Kin san kishiyoyi uku Marigayi mahaifinsu su Tafida ya auro kafin rasuwarsa? Ba ta damu da mganata ba ta cigaba da faɗin" Zan faɗa miki wani sirrin da ban taɓa faɗa ma ko ƴaƴana ba. Ina yar yarinyata ya ƙara aure a lokacin cikin maimuna ƙarami ne a jikina. Maman farko da kike gani bashi ita a ka yi abokin mahaifinsa ne ya bashi ɗiyarsa. Da maganar da auren tsakani wattani huɗu ne, amma ya kasa faɗamin saboda ya na tsoron tashin hankalina gashi ina da ciki kar wani abu ya samu cikin jikina kar na ɗaga hankalina wani abu ya same ni ya sa bai iya faɗamin da kansa ba sai amininsa marigayi Tafidan Rano ne ya zo ya same ni ya sanar da ni a lokacin sai da ya kalleni kafin ya ce" Hauwa'u ki godema Allah kin yi dacen samun nagartatten mijin da ya ke gudun ɓacin ranki da tashin hankali. Yususa ya ƙi sanar da ke labarin  matar da aka bashi ne saboda ba ya so ya tashi hankalinki wani abu ya same ki, ya na jin kunyar ki matuƙa duk da ba haramci zai yi ba, a lokacin ya ce min Hauwa ba duka maza ne irin Yunusa ba, ba duka maza ke iya jin kunyar matansu kamar yadda Yunusa ke jin kunyarki ba ya sake sanar da ni cewa ba duka maza ke tsoron tashin hankalin matansu ba, saboda haka ki daure ki kuma yi haƙuri ki ba ma mijikin goyon baya kar ki ɗaga masa hankali, ki yi masa alfarman guje ma tashin hankalinsa kwatanƙwacin yadda ya guje ma na ki."
Sadiya tun daga waɗanan kalaman da ya yi mini har ya bar duniya da gangan ban taɓa ɗaga masa hankali ba, in ma na ga hankalin shi ya ɗaga ni ce zan zama sillar kwantar masa da hankali, har ya yi duka aure aurensa ban taɓa ɗaga masa murya ba, na yi hakuri na danne saboda wannan nasabar da Ubangiji ya yi min a zuciyar mijina ba na so na bashi kunya. Na ci riban hakurina na zauna lafiya da shi da matansa tun yana rage ni ce giwarsa a cikin gida da waje har kuma ya koma ga Allah hakan bai sauya matsayina a wajensa ba sai ma ya ƙara hauhawa ninƙi ba ñinƙin, faruwan wannan lamarin ya sa kawai in na kalli Tafida sai na ga kamar na ga makwafin mahaifinsa ne a tare da shi, Sadiya ba wai ina faɗa miki wannan ne saboda tausan baki ba. A'a ina faɗa miki ke ma Allah ya yi miki wannan nasibin. Ba kowacce mace ba ce za ta samu miji na jin nauyinta ba, ba kuma kowace mace ba ce ke samun darajawa da mutumtawa a wajen mijin auranta ba. Ba kuma kowacce mace ke iya samun namijin da ke gudun tashin hankalinta da damuwarta ba. Ke Allah ya baki wannan nasibi na kawo miki wanman labarin ne saboda na ankar da ke wasu abubuwa guda biyu zuwa uku."

Ta ƙarishe faɗa ta na kallona. Na kuma natsu na ba da duka hankalina a kanta ina sauraranta.
"Sadiya."
Na amsa da "Na'am Nene."
Sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce" Kin ga duk sanyin halin Hauwa na sha yin shari'a tsakaninta da muttaƙa."
Ido na zaro ina kallon Nene sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Ba tonon asiri ba ne Sadiya Nasabar da Ubangiji ya yi miki na ke son ƙara tunasar da ke. Sadiya tun auran ku da Tafida bai taɓa kawo min ƙaran ki ko da rana ɗaya ba. Bai taɓa zama ya kushe ki ba sai dai ya yabeki, ke ma haka ba ki taɓa kawo min ƙaran Tafida ba,duk da na san kuna samun matsala domin babu auran da  bashi da matsala sai dai ku binne shi ku kaɗai ba tare da sanin kowa ba. Sadiya wannan ma wata Nasaba ce da Ubangiji ya yi miki, kuma a cikin idanuwana ina karrama wannan ƙimar ta ki."

Sai na ji kaina ya yi girma cikin alfahari Nene ba ta bani damar mgana ba ta cigaba da faɗin" To ba na so saboda wata ta zo ki sauya Sadiya. Kin zama turken gidan Tafida duk matar da ta zo daga bayanki sai dai ta ɗora igiyanta a kan wannan turken da kika riga kika kafa shi Sadiya. Kar ki sake da wannan matsayin da Allah ya ba ki na uwargida kan gida, kar ki yi sake da shi ya tashi a banza. Akwai zafi amma ki daure ki gani ƙi ƙi gani, ki ji kuma ki ƙi ji, a zo a gaya miki ki toshe kunnen ki in kika yi haka za ki zauna lafiya, ki ba ma mijinki dama damar da ya ke so daga wajen ki, ki yi ta addu'an zaman lafiya da salama Sadiya wallahi tallahi ba Saudatu ba ko Tafida bai isa wata rana ko halin su na maza ya motsa masa ya tozartaki ba saboda kin tsare mutumcin kan ki, na san Saudatu ke ma na san ki Sadiya in kuka yi hakuri za ku ba da shaidar kyakyawan zurua anan gaba. Ina roƙon ki  da ki riƙe wannan nasabobin da na sanar da ke Ubangiji ya yi miki, ko an yi miki wani abu in kika tuna su sai ki danne zuciyarki ki yi haƙuri in kika yi haka tabbas wata rana sai kin  ci riba in sha Allahu."

Kamar hadda haka na haddace kalaman Nene a cikin kaina kuma cikin ikon Allah da kalamanta sai na ji zafin da ke cikin zuciyata ya na raguwa. Ina jin haushin ta da na fara ji ita da Yallaɓai ya na raguwa. Duk da an ce tsakanin miji da mata sai Allah gaskiya ne zan kalli Nasabar da na ke da shi a wajen Yallaɓai na lulluɓe duka sharrinsa a gareni kamar yadda shima ya ke kallon alherina ya lulluɓe sharrina ba kuma wai domin ba ni da shi ba, kowani ɗan adam ya na da na shi alherin kuma ya na da na shi sharrin.

Sai kawai na kalli Nene ina murmishi kuma tabbas murmishi daga ƙasan zuciyata ya fito ba a iya saman leɓena ba ne.
"Na gode Nene. Kuma na yi miki alkwarin ba za ki ji saɓanin tunanin da kike da shi a kaina ba in sha Allahu."
Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Amin. In sha Allahu na gode nima da samu abin da nima na yi tsammani daga wajen ki. Na gode Allah ya yi muku albarka Allah kuma ya zaunar da ku lafiya ya kuma kaÉ—e fintintunu."
Na amsa mata da Amin Amin sai ta ce za ta wuce amma kafin nan na yi ma Yallaɓai mgana kafin ta wuce, ni na tashi na leƙa falon da suke zaune shi da Musbahu na kira shi muka dawo tare wannan karon kasan cafet muka zauna ni da shi gabaɗaya ta kallemu kafin ta ce.

" Na ƙara tunasar da Sadiya abin daman ta riga ta sani na auranka da Saudatu. Tafida sauran aikin na ka ne, ka zauna da matarka ku yi mgana ku fahimci juna ku tattauna rayuwarku tare. Dukkanku ina fatan tsamanin abin da na ke tsammani daga gare ku. Allah ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna. Dukkanku da ku da yayanku Allah ya yi muku albarka gabaɗaya."
Muka yi ta amsa mata da Amin sannan ta yunƙura ta miƙe ta na faɗin" In ina da rai wata rana ina fatan alheri ya sake dawo dani gidan ku."
Muka ƙara amsa mata da Amin. Yallaɓai ya shiga ƙwalama Musbahu kira ni kuma na je na kwaso mata takalmanta na jera mata ta zo ta saka ta na faɗin" Allah ya shi albarka. Allah ya ba ku zaman lafiya."

Ni na buɗe mata kofa muka fita har haraba sannan sai ga Yallaɓai da Musbahu, sun fito na buɗe mata gaban mota ta shiga sannan na rufe ina ɗaga mata hannu Yallaɓai kuma ya tafi buɗe musu get har Musbahu ya fita da mota na ga ya tsaya Nene na mgana da Yallaɓai ta window na ga ya na gyaɗa mata kai sannan suka wuce shi kuma ya rufe get ɗin ina tsaye na harɗe hannu a kirji ina kallonsa sai yanzu da na ƙare masa kallo na fahimci ba ni kaɗai na yi raman tsaye ba Yallaɓai ma duk ya rame sai karan hanci kamar bashi ba.

Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji yana shafa kumatuna sannan na fahimci ya ƙariso kusa da ni.

"Ya dai?

Ya faÉ—a ya na kallona sai kawai na sauke ajiyar zuciya.
"Bakomai."
Na sauke hannayena na juya zan tafi sai ya riƙo hannuna na dama, na juyo ina kallon shi.
Sai kawai ya wuce gaba ya na riƙe da hannun nawa, nima ban kwace ba sai na bi bayan shi. Bai direni ko'ina ba sai a kan kujeran mai zaman mutum ɗaya shi kuma sai ya durkusa a gabana ya na mai riƙe duka hannayena biyu a hannayensa ina kallon shi ya na kallona sai na ji rauni ya na kama ni. Zan iya fashe masa da kuka sai na yi saurin kauda kai, shi kuma sai ya kai yatasun hannuna ɗaya bayan ɗaya a bakinsa ya na sumbata. Kallon sa na ke yi da duka zuciyata ina jin ta na sake buɗewa a karo na biyu na yarda da kaddara wataƙila zantu kan Nene ne suka farkar da ni, wataƙila ba za ta ga laifina ba domin itama ai ta san kishi ta kuma ce ya na da zafi sai an daure.
Chapter 18 · 0% Book details