← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 89

Sashe 88

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta faɗa kafin ta juya, shi kuma sai ya rufo ƙofar ya ɗauko Khalipa, ina zaune sake da baki ina kallon abin mamaki yau ɗin ma wataƙila kamar kullum ya fara barci ne aka kai shi ɗakin su Jidda shi ne ya na farkawa ya ga bai ga Uban ba shi ne ya saka musu kuka.
Na kasa magana ganin Yallaɓai ya kwantar dashi a tsakiyar mu, har ya na lulluɓe shi da bargo.
Zuciyata ta ciwo ni yau ko ɗana ne sai na yi maganinsa ballanta ɗan kishiya. Ina iya ƙoƙarina amma yau kam an zo ƙarshe.

A fusace na miƙe sanye na ke da doguwar rigar barci hulan kaina ma ta saɓule. Kitson kaina shiko ne har ya ɗan fara ma tsufa tun da ban yi kitson bikin nan na Rano ba.

"Me hakan ke nufi Yallaɓai?

Na faɗa ina kallon shi, ƙoƙarin kwanciya shima ya ke yi kafin ya ce" Zai kwana tare damu. Me ya sa kike tambaya?
"Saboda ban gane ma'anar abin da kake yi min ba."
Sai ya kalleni kafin ya ce" Me ye ba ki gane ba? Kwanan Khalipa tare da mu?

"E."

Na faɗa afusace saboda na fara harzuƙa ma da tambayoyin shi.

"Miye a ciki? Ai ba yau aka fara ba ko? Kin san ai Khalipa ba ya iya barci sai tare da ni ko can gidan ne ita kanta Daugther ta san haka."

Ya na gama faÉ—in haka ya koma ya kwanta ya na faÉ—in" Ki rage mana haske."
Sai na ga yaron ya yi shuru Yallaɓai na kwanciya ya wani maƙale shi, baki na saki ina kallon shi, na ma kasa magana amma na ji a raina yau dai sai dai Yallaɓai ya zaɓa ko kwana da ni ko kwana da ɗansa.

"Yallaɓai ni ce zan fita na bar maka ɗakin ko kai da ɗanka ne za ku fita ku bar min ɗakina?

Na faɗa kai tsaye ina kallon shi, sai ya yi shuru bai motsa ba. Ina ganin haka a fusace na fizgi filo na kuma janye bargon da suka rufu da shi da ƙarfi ina faɗin" Zan bar muku ɗakin."
Sai kawai na ga Yallaɓai ya miƙe a fusace ya riƙe bargon da na fizge ya na faɗin.

"Sadiya me kike shirin aikatawa haka?

"Abin da ka ji ka gani mana "

Na bashi amsa a fusace saboda raina tuni ya gama ɓaci. Kawai sai ya fizge bargon ya shimfiɗa ma Khalipa. Yaron ya lumshe ido ban sani ba ko barci ya ke yi, har gabana ya tako ya na kallona kafin ya ce.

" Sadiya yaushe kika koma haka? Yaushe kika zama haka?

"Yaushe dai ka zama haka dai Haba ba ka yi min adalci. A ina ne aka ce dole sai da yaro zamu riƙa kwana? Ko ƴaƴana ka fi kowa sani suna shekara uku da wani muke raba shimfiɗa da su. Me ya sa shi ba za ku koya masa hakan ba?

"Na faÉ—a miki a can ma haka ya ke. Ba ki ga yaro ba ne? Zuwa gaba zai daina."

"To ni ina ruwana da can ma haka ya ke yi, ai can ɗin in ya yi wajen uwarsa ne, haba ni fa na gaji na yi kara na yi kawaicin amma ba ka gane ba. To daga yau ta kau in za ka kwana da ɗan ka, ka sauya ɗaki ko ni na bar maka daƙin gabaɗaya amma ba zan ƙara kwana da Khalipa ba."

Har na gama faÉ—a na ya na kallona. Sai kawai na ga ya yi mirmishi kafin ya ce" Ba sai kin bar mana É—akin ba, tun da É—akin ki ne mu za mu fita mu bar miki É—akin."

"Beter."

Na amsa masa ina girgiza jikina.

"Amma kin ban mamaki, ban taɓa tunanin haka kike ba Sadiya. Ashe gudan jinina ba jinin ki ba ne? Ashe Khalipa ba ɗaya ya ke da Jidda da Baby ba?

"ÆŠaya suke domin ko su ba ka ga ina kwana a gado É—aya da su ba."

Hannu ya ɗaga min ya na cigaba da faɗin" Sai yanzu na gano ki. Baƙin ciki kike yi a kan yara nan Sadiya ba tun yau ba, sai dai ban saka abin a raina ba saboda ina ƙaryata hakan sai ga shi yau kin tabbatar min.'

Ya faÉ—a ya na kallona sai nima na kalle shi cikin mamakin kalamansa.

"Baƙin ciki? Baƙin cikin me?

A fusace ya ce" Baƙin ciki Daugther ta na haihuwa ke ba kya yi shi ya sa kike jin haushin su Khalipa ashe duk ƙarya ce da kike faɗin ƴaƴana ƴaƴan ki ne? Ashe duk yaudara ne? Tir wallahi kin ban kunya sannan kin ba ni mamaki "

Na ma kasa magana sai nuna kaina na ke yi amma na kasa mgana.

"A kan ƙaramin yaro kin kasa ɓoyo kishin ki da baƙim ciki Sadiya. Ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba amma ba zan ce miki komai ba sai na gode."

Ya juya zai wuce bakin gadon na sha gaban shi da sauri ina nuna kaina kafin na ce" Ni ce yau ka ke kira ina baƙin ciki da ƴ'ayan ka Yallaɓai?

"E baƙin ciki kike yi in ba baƙin ciki ba me kike yi! To ki sani ba ni na ce ki je ki yi planing ya ba ki matsala ba sannan ba Daugther ce ta kai ki ta baro ba, ke kika kai kan ki kika baro saboda haka ki daina zargin kowa sai kanki, haihuwa yanzu Daugther ta fara ƴaƴa kuma ba ki da hurumin tsanar su kuma ba ki da hurumin hana su zama gidan nan domin gidan na uban su ne ba na ki ba "

Kafin Yallaɓai ya gama mgana ƙafafuwata sun kasa ɗaukata sai ga ni zuɓe a kasa. An ce kuka rahama ne sai yau na fahinci haka domin na kasa kuka, ina kallon Yallaɓai baki buɗe na ƙasa mgana amma kalamansa na shiga kaina suna kuma min amsa kuwwa!
Ni yau Yallabai ke ma gorin haihuwa? Ni yau Yallaɓai ke cewa ni na kai kaina na ɓaro?
A gaban idanuwana ina bin shi da kallo ya ɗau Khalipa suka bar min daki. Ni ce yau na zama yar baƙin ciki a wajen Yallaɓai ya kira ni da kowani suna sannan daga karshe ya ce nan ɗin ba gidan ubana ba ne gidan shi ne.

Na so na yi kuka amma na kasa zuciyata na ƙuna. Baƙin ciki da takaici sun cika min zuciya anan wajen na haɗe kaina da gwiwa na saki kuka amma ba hawaye ina kuka amma kuma zafin da ke zuciyata sai ƙaruwa ya ke yi, har da ihu na yi na kwanta ina birgima amma ban ji ko ƙwatan abin da na ke ji a ƙasan zuciyata ya ragu ba. Barcin da ban koma ba kenan idanuwana biyu a ka yi asuba yadda zuciyata ta soye haka idanuwana suka soye suma.

Ina jin fitan Yallaɓai masallaci da dawowar shi, duk ina zaune na kasa tashi domin sai na ji gabaɗaya jikina ya yi min wani irin nauyi kamar ba nawa ba na kasa tashi ballanta na shiga tiolet na kama ruwa na zo na yi sallah. Ban iya motsawa ba sai shidda saura na safe na iya miƙewa ina jin kaina ya yi min wani irin nauyi, ina riƙe da shi na shiga tiolet na kama ruwa sannan na yo alwala na zo na yi sallar asuba sai bayan da na yi sallar ne ina jan casbaha na ji hawaye na gangaro min saman kumatuna ban san adadin lokacin da na ɗauka ina kuka ba, Allah ya sa na sakaya ƙofar bedroom ɗin na ji Jidda ta zo ta na bugawa lokaci ɗaya da kiran sunana amma na kasa motsi ina zaune kamar status amma kuka na ke yi hawaye na sauka wasu na korar wasu. Ina jin gwara dai na yi kukan kar baƙin ciki ya kashe ni Yusuf Inuwa ba shi da asara.

Ni yau Yusuf zai kalla ya kirani yar baƙin ciki kalmar ta fi baƙantamin rai amma lokacin da ya yi min gorin haihuwa sai na ji komai ya tsaya min cak. Lalle na yarda da kalmar nan da hausawa ke yawan faɗin namiji ƙanin Aljali, namiji ba ɗan goyo ba ne ni Sadiya Sulaiman Yashe ni Yusuf Inuwa zai kalla ya ce ina baƙin ciki da y'ayan shi kuma har ya na ce min haihuwa yanzu Gimbiya ta fara wato sai dai na mutu sannan har ya na min gorin gida. Kuka na yi ta yi kukan abubuwa da dama ne, na ji gabaɗaya gidan ya yi min wani irin ƙunci ji na ke yi ko numfashin da na ke shaƙa a gidan ma gurbattace ne.

Na daɗe a cikin ɗaki, har wajen goman safe na ji fitan yara zuwa makaranta. Ina zaune a in da na yi salla ina kuka Yallaɓai ya yo wanka ya shigo ya sauya kaya bai ce min ba ni ban ma kalle shi ba amma na san ya ji yadda na ke jan hancina da macijana ya toshe min saboda kuka a haka ya sa kai ya fice shi da ɗansa. Ya jima da fita sannan na miƙe ina jin kamar kaina zai rabe gida biyu ga wani maƙaƙi da ke damuna a maƙoshina.
Chapter 88 · 0% Book details