← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 89

Sashe 29

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To na aiko shi ya sanar da ke yau akwai walima a Gwammaja"
Mamakin ta ya kamani to in akwai walima ina ruwan Sadiya a ciki?
"Bai sanar da ni ba, amma na ji a bakin mutane."
Ba ba ta amsa a saukaƙe domin raina har ya fara ɓaci, ban yi ma ƙaninta bore don zai ƙara aure ba, amma ba shi zai ba ta damar ta zagayo ta na ƙokarin ci min mutumci ba, ba yayar mijina ba ko uwarsa ce zan nuna mata na san darajan kaina, sannan komai ya tsaya a muhallinsa zai fi alheri gare mu gabaɗaya.

"Duk É—aya. Ki shirya ki zo kema a yi walimar da ke. Karfe huÉ—u ce kuma wa'azi ne za a yi muku kan zaman aure da zamantakewa."

"In shirya in zo kuma?

"E."

Ta ba ni amsa a takaici ina ta jin hayaniya ƙila ma ta na Gwammajan ne a gaban Gimbiyar da sauran su an saka ni a seaper za a ci min zarafi, cije leɓena na saka na yi, a ina tunani a cikin raina matar nan ba ta sanni ba ne, Ma'u ba ta ba ta cikakken labarin ni ni ba na barin ta kwana, kuma wanda ya ce da ni kule wallahi komai girman shi sai na ce da shi cas sai dai a yi wacce za a yi.

"In ji wa.?

Nima na tambaya a takaice, cikin fusata ina jin ta daga cikin wayar ta na faÉ—in" In ji ni, ko ban isa ba ne."
Mirmishi na yi yadda zan kunnata kafin na ce"Ba maganar isa ba ce. Ko shi ƙanin na ki da na ke zaune domin shi ya ce na je zan ga ya masa ya yi hakuri ba zan je ba, ke ma kuma haƙurin zan ba ki ba zan samu zuwa ba, domin ni a lokacin aurena na yi walima kuma an yi min wa'azin aure da zamantakewa, bayan haka kuma Iyayena ba su kawo ni haka ba sun yi min shekara goma sha biyar da aurena kin san sai dai na zaunar na karantar da wani ba dai ni na zauna ana karanta min wani abu akan aure da zamantakewa ba wallahi."

Na faÉ—a kai tsaye kuma ko a jikina. Ina ji ta yi shuru kafin ta ce"Me kike nufi Sadiya?
"Abin da na ke nufi shi ne ba zan zo ba. In ina bukatar walima na shiryata a gidana mana? Sannan ni ba na bukatar walima da wa'azi ita dai wacce ta ke bukatar wa'azin ba ka ga shi kin kira za a yi mata? Me ya sa za ki gayyace ni cikin sha'anin da ni na riga na girme shi Anty Bahijja?
Magana na yayyaɓa mata kuma na san sun yi mata zafi shi ya sa muka gama wayar kowa ran shi a ɓace.

"Ba wani kin girma. Da ɗan abin da kika sani na cikin cokali kike cika ma mutane baki! Ke dai kawai malama zafin kishi ba zai bar ki ki zo ba ne. Kuma sai haƙuri Gimbiya zama daram a gidan Tafida in sha Allahu.'

Ni kuma sai na maida mata da cewa" Nima ina fatan su zauna tare har mutuwa. Kuma kishi ai halas ne in ma ya hana ni zuwa na yi dai dai. Amma ga saƙo ki faɗa ma ita Gimbiyar ta ki, ta yi hakuri domin ni na ci na rage na ba ta saura kin ga kuwa komai na lalacewan giwa bai kai in ta mutu kiyashi ya ja ta ba, a macen ta ma tana da ƙima da daraja."

Sai ta kama faɗa ta na faɗin wai na yi mata rashin kunya, wai sai ta faɗa ma Tafidan na ce me ya sa ba ta yi masa recording ba, na kashe wayata na barta ta na bambami ita kaɗai. Ina dalili mata ta bar ni da kishiyar da aka yi min kawai ta kirani za ta ɗaga min hankali, saboda yanayin da na ke ciki in na tuna gobe zan fara Raba Yallaɓai da wata macen duk sai na ji na rikice, ga jama'a a gidan shi ya sa na ke kannewa, saboda abu kaɗan za ka yi sai a tafi da kai a baki ace zafin kishi wance ba ku ga abin da ta ke yi ba shi ya sa da na ji abu ya taso min zan ta kiran sunan Allah. Balle ma Amina a nan gidana ta kwana kuma na ji daɗi kwarai da ita da Marwa muka raba dare muna hira, Yallaɓai ma jiyan ba da wuri ya shigo ba kuma ma bayan ya shigo abincinsa kawai na bashi ya ci ya shige ciki na dawo wajen su muna ta hira a ɗakin su Jidda.

Amina ta zo mini da turarukan wuta masu ƙamshi ta ce a wajen ƙanwar mijinta ta siya a maiduguri ta ke aure an haɗo min har da kwallacha, fa humra ma su kyau da ƙamshi, shi ya sa saboda su na ke ɗauko mirmishi na aza a saman fuska, dalilin da ya sa ko da muka yi kaca kaca da Anty Bahijja a waya da na fito falo ban nuna musu ba tun safe suna ta ɗan ta ya ni gyara gidan ne, da goge goge ita da Marwa sannan ga Firdausin Yaya Balki da Amina ta kira ta a waya ta ce ta turo ta ta ya mu aiki, ni ba domin ita ba ba ma wanda na yi tunanin kira, sai Jidda da ke kama musu wani abun Baby kuma sai tsalle tsalle ita murna ma ta ke yi Anty Gimbiya Abba ya ce za ta dawo gidansu da zama Allah na tuba shi yaro ina ruwan shi.

Can wajen azahar sai ga Munnira ta zo daman ita na ce kawai su je gidanta ita da Hauwa da Amina goben su soye waina ni kuma sai na yi miyar anan gida. To kayan waina ta zo na haɗa mata sai kuɗin icce na ba ta da na niƙa da sauran abin da za a bukata da wuri ta koma gida amma ta ce min za ta dawo anjuma na je rakata haraban gidan ta ke min maganar walima.

"Ku na Walima a Gwammaja fa yau, ɗazu Anty Bahijja ta kirani wai duk mu zo saura mu ƙi zuwa tunda an ce tun satin nan gidan ki muka tare."

Daman baƙin cikinta suna zuwa gidana ta so ne a bar ni kaɗai kamar mujiya na ko gyara tsayuwa na ba ta labarin nima yadda muka hau sama muka faɗo Munnira ta ba ni hannu muka ta fa ta na faɗin" Kin biya ni Sadiya. Kin biya ni fiye da zato na a kanki. Ki ji wulakanci ta na so ki kwashi jiki ki je ta wulakanta ki mana."

"Ai ko sai dai ita ta wulaƙanta amma ni na fi ƙarfin ta wallahi."

Haka na faÉ—a ina huci Munnira na dariya, mun rabu ta ce min wallahi itama ba za ta je ba sai dai Hauwa ta je, kai tsaye na ce" Hauwa za ta je mana. Kin san tsoron su ta ke ji."
Kamar daman na sani tafiyan Munniran ba daÉ—ewa sai ga Hauwa, da farko ba ta faÉ—a min ma za ta je wajen walima ba sai daga baya wai ta na faÉ—a min Anty Bahijja ta kira ta ta ce ta zo, ni ko mirmishi na yi kafin na ce" Bakomai Hauwa sai kin dawo."

Saboda ni na san za ta je domin ta na jin tsoron kar ba ta je ba Anty Bahijja ta yi mata faɗa. Hauwa dai har yau ta kasa sama ma kanta ƴanci ni ko da na ke amarya a baya ban zauna wata shegiya da sunan yayar miji ko ƙanwarsa ta ta ka ni ba, kowa da matsayin shi, iya girmamawa ina ba su amma fa ba zan zauna ina jin tsoron su kamar na bauta musu ba, ba kuma su ke aurena ba ballatana su riƙa ba ni umarni ina bi cikin rawan jiki ba a baya ma ban yi haka ba ballantana yanzu da shekaru suka tura an riga an gogi jigida kowa ya san kowa.

Zuwa bayan La'asar ba kowa a gidan daga ni sai Amina sai Marwa da Firdausi da Saude sai yara sai can ne Ya Balki ta zo, da yamma Yallaɓai ya aiko Musbahu da kayan miya da sauran cefane sai Ya Balki ta karɓi gyaran Miyan kafin ma ta fara sai ga Ya Aina ta zo sai suka haɗu gabaɗaya suna yi Amina kuma sai ta dau naman ta na tafasa gefe ɗaya kuma ni ina dafa zoɓo saboda na ce a yi saboda mutane duk da Yallaɓai ya saka an kawo mana lemun kwali da ruwa amma ni ina so ne shi ya sa na ce a yi, daman kuma daga Yashe an ba mu ganye zoɓo ni da Rahila itama sai mangariba ta shigo da ya ke ta sha tsiya a wajena na ce sai ta kwanan min da ko shirin kwananta ta zo tare da yaran, sai ɗan iface ifacen yaran ya ƙara ɗan raya gidan hayaniya da hada hada ya sa na ji zuciya ta yi sauƙi ina ta harkokina.

Wajen bakwai da wani abu na yamma mai ɗinkinmu ya kawo mana kamar sun haɗa baki tare suka ƙwankwansa min gida da mai wanki, kayan Yallaɓai ne sai nawa, na yara daman kananun ni na ke wanke musu sai atamfofinsu ne da less na ke saka su a wanki ghana guda ne da kaya ya ce min Yallaɓai ne ya kira shi ya ce a kawo kayan, su Saude na kira suka kama min kayan zuwa cikin gida ina shigowa Amina ta kawo mini waya ta ce Yaya Auwal ne ya ce ya na ta kiran waya ta a ba na ɗauka sai a lokacin na tuna ta na cikin ɗaki na baro ta.
Chapter 29 · 0% Book details