Sashe 78
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maganar Marwa da Kawu Abba manya har sun shiga ciki amma ba'a saka rana ba. Cikin watan da zamu shiga Yallaɓai ya ce za a je a saka rana ita ma Marwa alokacin za ta koma makaranta ta ƙarishe semester ɗin ta. Koma da wani abu a zukatan su Anty Bahijja maganar da Kawu Abba ya yi ta rufe bakin kowa. Yan'uwan shi ko murna suke yi domin abin da suka daɗe suna jira ne sai yanzu ya tabbata. Shi ya sa ko kaɗan ba su damu ba su dai fatan alheri suke yi da fatan Allah ya sa albarka. Ta bakin Nene ta ce abin da muka daɗe muna jira ne mu dai ya furta ya na son wata zai aure ta kuma tun da har ya gani kuma ya na so za a nema masa kuma a aura masa. A cewar wasu ƴan'uwa daga can Rano wai Marwa ɗin an ce yarinya ce ta yi masa ƙanƙanta shi kuma ya ce tun da ita ba ta ce ya yi mata girma ba shima ko bai ga ƙanƙantarta ba.
Da Yallaɓai ke faɗa min abin da ke faruwa sai da na yi dariya a fili na ce Marwa ai ta wuce yarinya shekarata ta ashirin da uku ta ke ba, waɗanda ma ba su kaita ba an yi musu aure sun zauna ballatana ita? Yallaɓai ya ce shima haka ya gani amma shi sai ya danganta haka da cewa haushi ne bai nemi ƴaƴan su na nan Rano ba ya tsallake sun kuma rasa abin kushe shi ya sa suka ɓullo da haka. Ba su san Abba na dai-dai da su ba. Muna ta dariya ni da shi ni kaina ina jinjina masa ya na da dakiya sannan kaifi ɗaya ne in ya ce A to ko ruwa da iska ba su isa su saka shi ya sauya ra'ayi ba. Shi ya sa na sha faɗa ma Ya Aina da Marwa za su yi alfahari da wannan auran watan wata rana in sha Allahu.
Tuni na daina shan mganin asibiti. Na hannuna na ƙarewa na daina sha, ban kuma sake komawa asibitin ba. Gani na yi na daɗe ina amfani da na asibiti ba a samun abin da ake so ba sai dai sauƙi kam. Tun da al'adata na samu ya dai-dai ta. Sai kawai na watsar da na asibitin na fara shan wanda Inna Mariya ta kawo min kuma ina jin daɗin shi, ya na wanke mara kuma in na yi fitsari ko bayan gida ina ganin abin da na ke fitarwa da datti daga cikina. Na farko har ya ƙare na sake yi ma Inna Mariya mgana ta sake karɓo min har kuma a lokacin ban bari ta ji labarin abin da ya faru sanadin mganin ba, ko ba komai bai kamata ta ji ba, domin yadda zuciyata ta yi ɗaci na ta zuciyar sai ta fi tawa yin ɗaci shi ya sa ko da wasa ban taɓa gigin faɗa mata ba. Kuma na gargaɗi Amina itama na ce kar ta je wajen surutun ta ta kwashe ta faɗa mata ga abin da ya faru. Shi ya sa har lokacin ba ta sani ba kuma ba na fatan ta sani ɗin har abada.
****
*Saturday*
29May. 2016.
Yau asabar ɗin karshen maƙo ne. Jidda da Baby sun tafi Tahfez. Ni kaɗai ce a gida Yallaɓai ba anan ya kwana ba jiya ya na gidan Gimbiya tun da ta koma gidanta satin da ya kamata. A bakin mijinta na ke jin cikinta wata biyar har ya na faɗa min ya yi girma tun da har ya fito, ni in Yallaɓai na surutansa ba na biye masa iyaka kawai na kalle shi in abin Allah ya sauwaƙe ne na ce in kuma na Allah ya kyauta na ce na kama kaina. Tun da na fahimci ya na jin daɗin yin hiran matar da ni sai ka ce ni ina da matsala da hakan ne.
Yau akwai ranar iyaye daga makarantar su Jidda. Kuma Yallaɓai ya sani an aiko da takarda kuma head teacher na class ɗin su Jidda ta kira sa ta faɗa masa, kuma an tura a group na makaranta tun da ya na ciki. Nima clasa teacher ɗin su Baby ta faɗa min tun da ina da lambarta muna mgana in wani abu ya taso ta yi min mgana na ce za mu taho ni da Yallaɓai. Tun da duk shekara suna yi domin tattaunawa cigaban makaranta da yaranmu.
Yallaɓai ya fi zuwa ni duka duka bai fi sau biyu na taɓa ba, ko a jiya da ya zo yi mana sallama yaran sun tuna masa nima na yi masa mgana ya ce daga can zai shirya sai ya biyo mu tafi tare. Amma Yallaɓai tun 10 na safe na shirya na zauna ina zaman jiran shi har Saude ta zo sha ɗaya da wani abu na rana Yallaɓai bai zo ba kuma in na kira shi sai ya ce min ga shi nan a saman hanya.
Raina ya ɓaci na ga dai ba office ya je ba ya na gida amma kuma ya na ta raina min wayau. Ko daga Zaria ne a awa biyun da Yallaɓai ya kwashe ai kamata a ce ya sauka, har na yi zuciya na ɗauko jakata zan tafi saboda taron goma da rabi ne ga shi har an ci rabin lokaci kawai ina fita haraba gidan sai ga shi ya shigo ya na maiƙon wata farar shadda har da babban riga ta angon cin shi ce shi da Gimbiya. Baki na saki ina kallon shi domin ganin shi na yi ya na wani annuri kamar wanda aka yi ma albishir da kujeran makka sai da ya matso kusa da ni sannan na ji ƙamshin mai daɗi da sanyi dake tashi daga jikin shi. Ban ma san na saki baki ina kallon shi ba sai da na ji ya na faɗin.
"Na yi miki kyau ne Madam?
Ya faɗa ya na rufe min baki. Hannunsa na kaɓe daga fuskata ina jifansa da wata uwar harara.
"Afuwan Abar ƙaunata."
Ya faÉ—a har ya na É—aga hannuwa sama.
Kanar in yi tsaki sai kuma na fasa na wuce kawai na bar shi nan tsaye sai ya biyo bayana yana faÉ—in" Ba mu makara ba ki daina damuwa"
"Haba Yallaɓai in ka san lokaci za ka ɓata me ya sa ba ka ce mu haɗu a can ba?
"Mu haÉ—u can abin ai ya yi wani iri kuma? Gwara mu je tare zai fi ko?
Ya faɗa ya na kallona lokaci ɗaya ya na ƴar dariya. Ni ko na sake maka masa wata harara na fice daga gidan, motarsa a waje ya barta ce min ya ke yi ba zan rufe gida ba ne sai na ce Saude na ciki sai kawai ya jawo kofar. Yallaɓai bai faɗa min ya ɗauko Amaryansa ba na je da ƙarfina na buɗe gidan gaba da niyar shiga kawai sai na gan ta a zaune ta kame ta ci uban gayu gyale a kafaɗa har da saka wani glass baƙi a fuskarta. Sannan kamar yadda mijinta ya faɗa ne ga cikinta ko har ya fito ta cikin doguwar rigar da ke jikinta kamar ma ado ta ke yi da cikin. Tiƙashi.
Sai gani tsaye galala ina kallon ikon Allah. Ita ko da ta ganni ko a jikimta sai ma gilashin fuskarta da ta cire ta na faÉ—in"Â ina kwana Madam"
Na kasa amsawa sai Yallaɓai da na kalla lokacin da ya ƙariso yanayin kallon da na ke yi masa ne ya sa ya yi saurin cewa.
"Tare zamu je saboda da ga can zan sauke ta gidan Naja"
Kuma ya na gama faɗin haka ya buɗe bangaren direba ya shiga ni kuma ina tsaye kamar wata sakara. Dakyar na iya fusko numfashina sannan na iya matsawa baya ina matsawa ta saka hannu ta rufo ƙofar gaban da na buɗe. Duk sai na ji na muzanta har zan buɗe ƙofar gidan baya in shiga sai wata zuciyar ta hana ni. Wato su suna gidan gaba suna shan soyayya ni kuma ina gidan baya kamar almajira sai kawai na juya na zagaya ta can bangaren Yallaɓai ina zuwa sai ya sauke gilas ya na faɗin.
"Ki shiga mana ba ke kike ta faÉ—an mum makara ba?
Da idanuwana da suka kusa fallasa asirin da ke zuciyata na ce amma na danne ina faÉ—in" Ku je kawai"
"Ban gane mu je kawai ba "
Ya faÉ—a cikin mamaki.
"To ai na ga ba sai mun je mu biyu ba tun da ga Gimbiya ku je kawai ni ba sai na je ba."
Na ɗauka Yallaɓai zai matsa min sai na je amma ga mamakina sai kawai ya rausayar da kai ya na faɗin.
"Kin tabbata mu tafi bakomai?
Sai na gyada masa kai cikin ƙarin mamakin sa.
"Ku je kawai. Itama kamar uwa ce a wajen su Jidda."
"Gaskiya ne to mun gode da kara Maman Jidda."
Ya faÉ—a ya na kallon matarsa har ya na kashe mata ido. Ni ko kaina na kauda ina faÉ—in" Sai kun dawo"
Ina jin ta ta na faɗin" Allah ya sa" daga haka na wuce ko waigensu ban yi ba jakata na laluba na saka key na buɗe get ɗin domin in na na tsaya bugawa ɓata lokaci ne Saude na cikin gida kafin ta ji sai na daɗe. Haka na koma gida ina ƙara mamakin Yallaɓai ashe daman ni ya shanya ni ya na can ya na cin soyayyarsa bayan sun gama kuma ya tsaya jiranta ta shirya ni kuma ga ni shegiya ina ta zaman jiran shi kuma tsabar wulakancin namiji bai faɗa min tare suke ba sai dai kawai na je na ganta kuma ya na faɗin wani wuri za su wuce daga nan kenan sai dai na hau adaidaita na dawo gida. To ai Yallaɓai bai isa ya wulaƙantani ba in ma ya shirya na shiga gidan baya ne su suna gaba suna soyayyarsu sai dai duk abin da ya shirya ya koma masa. Tsabar ma daman ɗaukonin da za su yi kamar cikas ne gare su ina cewa su tafi gabaɗaya suka yi murna kamar daman ni ɗin lalura ce a wajen su.