← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 89

Sashe 84

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  A yanzu da na ke da matakin shekaru talatin da bakwai a duniya. Yallaɓai kam ya haura arba'in ya kama gidan Hamsin amma daga ni har shi in ba mun faɗi shekarun ba, ba mai sanin haka saboda mun mori jiki sannan ga jin daɗi musamman shi da ya ƙara zama babban mutum sosai. Ni kuma har gobe ban daina gyara jikina ba, har kuma zuwa lokacin ban ƙara samun ciki ba shekaru goma kenan tun ina mganin asibitin da na gargajiya har daga ƙarshe na haƙura na yi shekara ban ƙara shan wani mgani ba, daga na hausan har na gargajiya. Na fauwalama Allah duka lamuran shi duk kuma abin da ya yi min to dai-dai ne. Ba zan ce a shekarun ukun nan da suka gabata ba mu yi ta samun matsala da Yallaɓai ba mun samu sosai, sai dai wani abun kana barin shi ya wuce domin a zauna lafiya. Tsakanina da Gimbiya sama sama kamar baya ta na gidanta ina gidana amma duk da haka bai hana ta makirci da kissa ba.

Tun haihuwan Khalipa na fahimci ta na da son kanta sannan makira ce. Ita ta ɗauka ni ban iya makircin ba ne shi ya sa ba na yi mata. Na iya kawai dai ni ina zaune da ita da zuciya ɗaya ne. Ina mamakin kishin da ta ke nunawa a kan Yallaɓai ta manta ni ce matar shi ta farko daga baya ya aureta amma yadda ta ke nunawa kamar ta fi ni kishi ne. Tun da khalipa ya isa fara tafiya ko na ce ya fara cin abinci duk in da Yallaɓai zai je tare su ke zuwa kamar ɗan gwal. Da ya zo ya fara tafiya kusan in dai Yallaɓai na gidana shima ya na gidan tare da uban. A cewar shi ya saba da shi ko ita Gimbiyar bai saba da ita kamar yadda ya saba da Yallaɓai ba shi ya sa ko yaye a gidana ya yi rabin yayen shi, da sunan ga su Jidda sannan kuma Khalipa ba ya kwana a kusa da kowa sai a jikin Baban shi. Kawai dai a takaice regular costumer ne shi a gidana. In Yallaɓai na gidana to shima ya na tare da shi in kuma ya na wajen Gimbiya to shima ya na can. Abin haushi ma da takaici sai a tsakiyarmu ya ke barci, ko an kai shi ɗaki su Jidda ya na barci da ya farka muna cikin barci za mu ji kukan shi dole sai a jikin uban ko a kusa da shi zai kwanta. Ni lokacin da na reni ƴaƴana ni kaɗai na sha wahalata amma ni gashi ta haifa ta bar ni ina shan wahala,  ga shi yaron ba ya jin mgana ga mugun wasa ga ƙarfin tsiya har Baby yanzu gagaranta ɗauka ya ke yi. Sai Jidda tun da ita kam ta zama ƴan mata kusan shekaru biyu da fara period ɗin ta. In na yi magana Yallaɓai ba ya bi ta kai sai ya ce yaro ne duk ranar da ya ke gidana tare da yaron nan muke kwana a kan gado ko ƴaƴana ba su yi min haka ba, sannan mgana kaɗan in na yi a kan Khalipa sai Yallaɓai ya juya min mgana ya ta so min shi ya sa na saka masa ido a yanzu haka a cikin yanayin da muke kenan na gaji matuƙa ba ni da lokacin sakewa da mijina Khalipa na naniƙe da shi wanka ne kaɗai ba ya bin sa amma ko masallaci tare su ke zuwa.

A lokacin da ya dawo daga Saudiya na ga uwar tsaraban kayan wasan da ya kwaso musu sai da na yi magana da cewa Yallabai hala dai ba ibada ya kai ka saudiya ba. Siyan kayan wasa ka je yi ko?
Ai daga wannan maganar ya fara min masifa wai ina mgana ba ta taunawa ko Baby ai ba za ta yi wannan mganar ba, sai da na yi nadamar yi masa mgana kwana biyu ya yi ya na gaba da ni. Daga faɗin gaskiya domin jaka ce shaƙe da kayan wasa ba dole na yi tunanin daman abin da ya kai sa ba kenan ni kaina gidana ga su nan da yawa ballantana gidansu da Jidda ta ce min ɗaki ne guda da kayan wasa na khalipa da Anwar. Na yi ta haƙuri ina kauda kaina yanzu haka Gimbiya sunan da su  Anty Bahijja ke kiranta da shi shi ne Uwar maza. Shekaranjiya ma mun haɗu gidan Naja suna ta haihu ana ta yi mata kirari da Giwar gidan Tafida uwar maza mace mai kashin arziƙi domin a cewarsu tun da Tafida ya aure ta ya ke ta ganin buɗi na arziƙi ni dai ban tanka ba tun da daman ai tun bayan faruwan lamarin nan sun sanni na san su, shi ya sa in suna abin su ba na biye musu suma kuma sai dai habaici da shakuɓe amma ba sa yi da ni kai tsaye.

Munnira ce ma ta ce ita uwar mata ba uwa ba ce? Anty Maimuna ta ce uwa ce amma uwar maza ita ce da gida. Sai da muna adaidaita za mu tafi gida ni da Hauwa bayan mun rabu da Munnira ta ke min mgana wai kar na damu da mganganunsu ni ko sai na ce yau a ka fara? ai sun daɗe suna fadin haka ban taɓa nuna na damu ba, ita kuma Gimbiya ta na hura hamci ta na iyayi ita matar arziƙi ni ko na ce in ma tsiyar ce to Yallaɓai ne ya shafa min tun da ni kam da arziƙina ya aure ni ya tsiyata ni yanzu da ya samu duniya sai suka manta. Yanayin rayuwa ya sa na daina ma damuwa da wasu manganganun saboda ai jiya ba yau ba ne.  Kuma girma ya ƙara kamani da ya sa lamarin ya zame min jiki ba komai in na ji ko na gani na ke mgana ba amma tabbas an kusa kai ni bango akan lamarin Khalipa na zura ido na yi kara na yi kawaicin duk a banza ko ƴaƴana suna tasawa na ke daina kwana da su ballantana ɗan kishiya. A raina na ji ko me zai faru sai dai ya faru amma sai na yi ma Yallaɓai mgana.

****

Tiolet na shiga na kama ruwa sannan na fita falo. Jidda ce kawai ke gida ba ta jin daɗi Baby kuma ta tafi Tahfeez. Falon su Khalipa duk ya kama kaca kaca da shi ya watso min fillows ɗin kujera a ƙasa. Jidda na falon ta na karatu a ipad ɗinta tun da Abbansu ya ce a wannan shekaran za ta yi jarabawar fita da Jamb.

"Jidda kina zaune Khalipa ya hautsina min falo haka?

Sai ta ɗago ta na kallona kafin ta yatsina fuska ta na faɗin" Na gaji da gyarawa ne Umma da na gyara sai ya ƙara watso su."
Hararanta na yi kafin na ce" To ni ne kike so na kwashe? Ina mgana na ji ina taka ruwa na fara mata faɗan ta bari ya jiƙa min gida sai ta ce wai ita ba ta sani ba.

"To ke za ki yi min gyara gidan  ko yarinya."

Na faɗa ina shiga falon Yallaɓai nan ko sai da na kusa kuka ya watsa duka kujerun dining sannan na iske shi ya na feshe kujeru da ruwan bindigarsa ai saboda takaici ban san lokacin da na masa tsawa ba, kuma ga shi ba shi da tsoro, ke gizau Jidda na ƙwalama kira ta na zuwa na ce ta natsar da shi kuma ta gyara min gidana ko ranta ya ɓaci.

"Umma wallahi na hana shi ya ƙi bari ne."

Na wuce ina mai jan tsaki kafin na ce" Wannan ke ya shafa. Ni dai na fito na ga gidana ya yi tsab ya na tashin ƙamshi."
Kitchen na shiga na haɗa tea daman akwai ruwa a fulas na dawo falon na zauna. Ina jin su ta na gyarawa ya na ƙara ɓatawa ita kuma ga shi ba ta da zafi shi ya sa ya ke ba ta wahala da Baby ce da yanzu an fara kokuwa. Da na ga ba zai bari ba sai na fito da bulalata na na nusa masa na ce ko ya natsu ko na zane shi, bai ko natsun ba sai da na chau la masa biyu sannan ya fara kuka daga nan sai barci shi ne fa Jidda ta samu ta yi min gyaran gidan. Ita ba ruwanta ta na son aiki ga wacce sai na yi da gaske ta ke aiki nan Baby in na yi magana sai Yallaɓai ya ce ai gado ta yi kuma daman an ce magaji ai mafiyi ina jin haka zan yi shuru. Allah sarki Saude ita na ke tunawa in su Jidda na makaranta aiki ya yi min yawa. Tuni an yi mata aure shekara ɗaya kenan a jigawa yanzu haka tsohon ciki gare ta. Duka masu zuwa su tayani aiki yanzu suma sun kama ɗaku nan kansu. Jidda dai ke ƙoƙari domin in dai ta na gida ba na aiki girki kam ba abin da ban koya mata ba.

Yau Yallaɓai a gidana ya ke amma gobe zai koma gidan Gimbiya. Sai dare ya shigo gidan ya ce min ya ɗan tsaya a Gwammaja ne, da ya ke Nene yanzu ta samu lafiya sai dai ɗan ciwon kafa da ke matsa mata lokaci bayan lokaci haka. Ko da ya dawo Khalipa ya yi barci amma kamar ana masa wahayi da ya ji muryan ubab zai tashi nan fa ya maƙale masa har cikin gaurancinsa ya ke faɗa ma uban wai na dake shi, shi kuma ya ce ka yi ma Umma laifi kenan ko?

"Ɓarna ya yi min bayan na saka Jidda na gyarawa ya ƙi barin ta ta yi aiki shi ne na yi masa bulala biyu."

"Kai sarkin rigima ba za ka daina yi ma Umma ɓarna ba ko?
Chapter 84 · 0% Book details