Sashe 42
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma an ta siyan Hijaban duk da na ɗan yi kyattuka da wasu. Na ɗaukan ma Saude da Marwa. Sauran kuma na tallata ma su Ya Aina da su Ya Hamza kuma duk sun siya ma matansu. Sannan har group ɗin makarantarmu na shiga na yi musu talla har mutum uku sun aiko da kuɗi sun siya sun kuma aiko har gida an karɓan musu. Duk da mun ɗan samu saɓani da Anty Bahijja amma tuni na yi mata na ƴan duniya da kaina na kira ta na yi mata tallar Hijaban sai ta fara min faɗa wai na gama yi mata rashin kunya zan neme ta yanzu. Ina dariya na wayance da cewa.
"Haba Babbar Yaya. Wace ni Sadiya ai ban isa ba. Rashin fahimta ce. Ke ce ba ki fahimce ni ba."
Sai kawai ta ce min" Ni Yar mijin ki ce ba ƙanwarsa ba Sadiya ya kamata ki riƙa tuna haka."
Nan dai na samu na basar da mganar na tura mata tallar Hijabai kuma sai da ta siya ma ƴaƴanta haka itama Anty Maimuna ita sai gashi ta na gaya min Nene ma ta nuna mata wanda na bata da wanda Tafida ya siya mata. Itama ta siya ma kanta da yaranta, Mimisco babban harka ta yi min tambaya na kawai ta yi guda nawa suka rage? Na ce 15 suka rage na manya goma na yara guda biyar kawai ta ce na saka mata acct ɗina da farashin za ta saka min kuɗi sannan za ta aiko direba ya karɓa. Da ina mata godiya sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce.
"Haba Sadiya ku fa namu ne. Dole mu zama masu ƙarfafa muku gwiwa."
"Na gode Mimisco Allah ya ƙara ma rayuwa albarka."
Ta amsa min da Amin Amin sannan muka yi sallama kuma ba daɗewa Ina tura mata acct ɗin sai ga kuɗina ya shigo na daka tsalle ina murna. Tuni na kira Khaleesat na faɗa mata sai ta ce za ta tura min lambar ƙanwar na ta mu yi magana ita za ta haɗa ni da mai saida yadiddikan hijaban kawai da shi zan dinga magana da na siya kawai aiko min da shi direct ta hannuna kawai zai yi, sai na ce hakan ma ya yi. Ina ta murna na siyar da Hijabai na kuma ina fatan wannan sana'ar da na fara Allah ya sa ta ɗaure min ta kuma ta riƙe ni, na yi ma kowa talla amma ban da Ma'u domin ni ban ma faɗa mata ba, ba kuma na saka wani abu a raina ba ne a'a kawai dai ban faɗa mata ba ne amma a raina na saka cewa in aka ƙara saro wasu zan yi mata talla bakomai in ma ta na da wani aniya a cikin ranta ne Allah ya mayar mata da sharrinta.
Khaleesat na tura min lambar ƙanwarta Madina na kira ta muka yi mgana ita ta haɗa ni da shamsu mai yadin hijabai na sabon garin zariya. Shi kuma ya haɗa ni da mai ɗinkin Hijaban anan kasuwar ya iya sosai domin shi ma ya ɗinka min na farko na biyun ma bayan duk na tura masa kololin da kuma adadin yadinka ya ce za a ɗinka nan da kwanaki biyu za su iso hannuna. Amina ma mun yi waya ta ce za ta tallata min in ana so anan Kaduna za ta yi min mgama sai na riƙa aiko mata da shi ta na siyar min aiko na ji daɗi har a cikin raina tuni na fara jin gwara na manta da rayuwar Yallaɓai da Amaryansa na kama sana'ata domin shi ne alherina.
****
Alhamdulillah kawai zan ce domin har Hijaban da aka sake kawowa sun ƙare. Gimbiya ta sake min ciniki guda huɗu ta siya sannan ta ƙara siya ma su Jidda. Kuma ta yi min talla a can wajen aikinsu kusan ma rabin Hijaban daga ɓarayinta suka ƙare. Nima saboda jin daɗin haka har kyauta Hijabi na ba ta guda ɗaya na yi kuma mata godiya ta ce bakomai an zama ɗaya shima Yallaɓan na faɗa masa da cewa ya ta ya ni yi mata godiya sai jin daɗi ya ke yi an yabi Amaryansa tun ina mamakin Yallaɓai ni fa yanzu har ya zame min jiki ma.
 Duk da ba wani sakar mata na ke yi ba. Ni dai ban taɓa takawa gidan ta ba amma ni tana yawan zuwa za mu gaisa a zauna ana hira sama sama na ke saka baki, saboda ni na kama girmana ban zaƙe ba ban kuma tusa kaina ina daga gefe gefe dai. Amma ita da yara kam ban isa na shiga tsakaninsu ba tun kafin auran ta da Yallaɓai daman ta shaƙu da su sannan komai ta samu su ne tun a baya ballatana yanzu da ta ke auren uban su. Komai ta samu su ne kuma na yarda ya na siyan mata daraja da ƙima a wajen Yallaɓai ya kuma saka ya ƙara sonta domin in dai ta kawo min wani ko ni ko yara haka zai ta washe baki, wani lokacin ma saƙon shi ya ke kawowa ya na faɗi ya na nuna farincikinsa.
Ba ta zuwa hannu rabbana. Ko ta yo girki ko ta soyo nama ko kaza ko kayan fulawa haka dai. Su kuma su Jidda wani riborn da kayan kwalliya duk ta ɗauke min duk ita ke siya musu. Ni ban taɓa cewa komai ba sai godiya kayan wasa kam har suna yi musu yawa ta siya musu yan kanti ta kuma ɗinka musu duka dai, yadda ta ke kyautatamin da ƴaƴana in na fara wata mgana sai a ce baƙin ciki ne ko ba ni da haƙuri shi ya sa na koma gefe na yi bakam kawai ina lura da komai, in suka zo tare haka za ta yi ta wannan karera yan ita wai mai miji, ta na wani maƙale murya tana kiran Daddy shima ya na wani kiranta Daugther tun ina mamakin su har na koma na daina kawai ni dai sai ido domin ni ba wani munafuncin namiji da ban sani ba, sannan makircin mata ma ai mun gan shi kala kala so daga ita har shi ni sai dai kawai na kalle su.
***
Yau Asabar Yallaɓai a gidana ya ke bayan ya dawo daga kaduna a ranar da daddare wanka kawai ya yi ko abinci bai tsaya ya ci ba ya ce Jidda ta zo ya kaita can gidan.
Muna zaune a falo ni da ita da Baby, ban yi magana ba kuma ko É—ago kaina ban na kalle shi ba ina zaune ina yanke kumbana sai da na ji ya ce.
"Ki haÉ—o kayan da É—an yawa Jidda."
Sai ta kalle shi, nima na É—ago ina kallon shi amma ban yi magana ba.
"Abba can zan koma?
Sai ya girgiza kai kafin ya ce" Ba daÉ—ewa sosai ba. Umman ta ku ba ta jin daÉ—i ne kwana biyu shi ya sa."
Yadda ba ni ya ke faɗa mawa ba nima ko sai na yi kamar ban ji ba amma kuma a ƙasan raina na ji kamar Yallaɓai ya wuce gona da iri. Ni fa na haifi Jidda amma sai ya riƙa nuna min kamar Gimbiya ce uwar ta ba ni ba.
Ina zaune ina kallon ikon Allah, har Jidda ta haɗo kayanta da yawa a ƙaramar jakar ta. Baby kuma na wajen Yallaɓai ta riƙe mai hannu ta na faɗin itama za ta je, sai ya kalleni kafin ya ce" Zan ta fi da Baby in zan dawo sai mu dawo tare."
"Sai kun dawo."
Haka na faɗa ba tare da na ɗago na kalle shi ba, Jidda ta ce min Umma zan tafi? Itama ban kalle ta ba na ce sai ta dawo. Kuma bai saka Yallaɓai ya kalleni ya yi min wata mgana ba. Ina zaune har suka fice ya na riƙe da Baby da shi da kansa ya sanya mata hijabin jikinta suka fice suka bar ni, na yi ta ƙoƙarin na danne amma na kasa sannan ga shi tun wajen takwas da wani abu suka fita ba Yallaɓai ya dawo gidan ba sai goma da rabi kuma ya bar min abinci ya yi kwantai na yi masa ta yi ya ce min cikinsa ya cika tea kawai zai sha da haushi ya kamani na yi wucewata ɗaki a raina na ce sai dai ya koma can Gimbiyar ta baka ko kuma ka shiga kitchen ka haɗa da kanka.
Bayan na kwantar da Baby a ɗaki na yi mata addu'an barci na koma ɗaki na yi shirin kwanciya na kuma yi kwanciyata shi ya na can falo ya na aiki a system ina ga ya na ta jiran Tea ne ya gaji ya ga ban kawo ba ya miƙe ya nema ma kansa mafita. Ni dai ko da ya dawo ɗaki na yi barci sai da asuba ne ya ke ce min wai jiya sai ya ji ni shuru?
"Barci ne ya É—auke ni."
Haka na faɗa masa kai tsaye. Na kuma haɗe raina, kamar ya fahimta ne sai bai ƙara min mganar ba, ni fa bai faɗa min baki da baki Gimbiya ba ta da lafiya ba kuma ni ban tambaya ba, sai Munnira ce da ta kirani a waya ta na faɗa min wai ko ciki ne da ita? Sai da gabana ya faɗi amma ban nuna mata ba na ce ban sani ba gaskiya. Ni ban je ba saboda wanda ya ijiyeni bai faɗa min ba, bai kuma ce na je ba nima ban tusa kaina ba shi a tunanin shi ai na ji ya na faɗa lalle Yallaɓai ya manta halina ne shi ya sa.
Har Hauwa ta je ta dubata ta biyo gidana ta na gaya min gida cike can ta bar su Anty Bahijja da Anty Maimuna.
Ita ce ma na buÉ—e ma baki na tambayeta me ke damun Gimbiyar?
"Ciwon kai. Sai maleria da ya saka jininta ya hau sosai."
"Allah ya ba ta lafiya."