← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 89

Sashe 31

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yallaɓai ya ɗauko ni a motarsa misalin tara na dare. Ina gidan gaba mai zaman banza amma kuka kawai na ke yi. Yallaɓai na ta kiran wayata ban ɗauka ba, wayar na cikin jaka sai ya kira ta Alhajinmu shi ya ce ya zo ya ɗauke ni, ni dai bayan Alhajimmu ya gama min nasiha ya sallame ni na fito Yallaɓai ya shiga ciki kuma ya ɗan daɗe sannan ya fito ni dai ina kuka na baro gidan Datti har bakin mota ya rakamu sai faɗi ya ke yi" Ya Sadiya kamar Alhajinmu ya saka miki duka?

Ya faɗa ya na dariya Yallaɓai ne ya kula shi amma ni kuka kawai na ke yi, saboda ma kar Yallaɓai ya ji kansa ya yi girma ina kuka saboda auran shi mun kusa isa gida ina share hawayena na kalle shi ina faɗin" Mama na tuna. Mutuwar ta ce ta dawo mini kamar sabuwa."

Bai ce komai ba sai ma kai da ya girgiza ya riƙe hannuna guda ɗaya da shima hannunsa ɗaya ya na faɗin" Na gane. Ki yi ta mata addu'a kin ji ko? Allah ya yi mata rahama."
Na amsa da Amin ina jinjina kai, mun shiga gida tara da rabi da wani yara duk sun yi barci har da Faridan Tariq ma ta yi barci Rahila ce kawai da Amina zaune a falon yara suna kallo, sai ga mu mun dawo suka yi mana sannu da zuwa, Yallaɓai ya shige ciki ni kuma na zauna wajen su yadda ba su tambayi me ya faru a can ɗorayi ba, nima ban faɗa musu komai ba, zama muka yi muna ta hira ni tea ma na sha saboda cikina ya warware. Yallaɓai ma tea ɗin ya sha ya na dai can ɗaki mu kuma muna falo muna hira an tuna da ana ta dariya da shewa su suka ɗeɓe min kewa sai wajen ɗaya saura na dare muka je muka kwanta.

Faridan Tariq daman ɗakin dake gefen namu ta sauka ita da Amina Rahila kuma sai ta ce ta kwana ɗakin su Marwa ina da katifa yara ta kasa sai Marwa da Saude daman sun shimfiɗa sun kwanta sauran yaran kuma sun kwanta tare da su Jidda. Ni kuma na shige ɗakin mu na kwanta gefen Yallaɓai da har ya yi barci ma.

*****
Asabar.
28. Dec 2015.

Ranar asabar mun tashi da taron biki, ni dai kamar muka tsara haka tsarin ya tafi. Su Munnira su ka yo waina su Amina kuma suka yi miya da zoɓo anan gida sai kuma Alele ba dai da yawa ba na ce su Saude su wanke wake a yi. Da safe dai Tea muka sha sai buredi sannan aka soya ƙosai. Da ya ke ba wasu jama'a na gayyata ba ƴan'uwana ne, dangin miji kuma suna can Gwammaja suna na su taron

Tun 11am na safe muka yi wanka gabaɗaya gidan kowa ya shirya. Tun da tun safe an gama komai, zuwa sha ɗaya da rabi su Munnira sun iso da waina Yallaɓai kuma tun safe Kawu Abba da Tariq suka zo suka fita tare da shi, ashe Tariq tare suka zo da Farida anan garin ya kwana ni ban ma sani ba sai da safen da suka zo gidan ya ke faɗa min, anan ma suka karya sannan suka fita, Yallaɓai an sha wanka da fararen kaya har da babban riga, ni kaina na jinjina ma kaina kamar an ƙwara min ƙwarin gwiwa na yi mamakin yadda na tashi cikin kuzari da dakiya.
Kawu Abba ya ce min na kwantar da hankali na su suna bayana kuma matukar Tafida ya yi min wani abu da ban gane ba kawai na kira shi zai yi min mganin shi, na ce an gama mgana zan ko kira shi suna ta dariya shi da Tariq.

Abin mamaki Ya Murja da wuri ta zo ita da yaranta gabaɗaya Anti ce ba ta zo ba amma ta ce ta je makarantan hadda ne in sun ta so ta ce mata ta same ta a gidana abin da ya ƙara ba ni mamaki da ita shi ne har awara ta yo min mai yawa ta zo min da shi, har sai da idanuwana suka ciko da kwalla da Ya Balki ta ba ni kula cike da awara ta ce Ya Murja ta yo min ta zo da shi.

Na kalleta cikin wani yanayi kafin na ce" Ya Murja ashe dai ba Ma'u kaÉ—ai ki ke so ba. Nima kina so na."
Na faɗa cikin wani yanayi a muryanta su Ya Aina suna ta mana dariya ita ko harata ta yi kafin ta ce" Ji wata magana mutun ya taɓa kin ɗan'uwansa ne Sadiya? Ni fitinarki ne ya ba ma shiri amma ki sani ke ɗin fa jinina ne, jinin da ke gudana a jikinki da jikina bai kai wanda ke gudana a jikin Ma'u ba Ki daina gasa da ita ni duka ɗaya na ɗauke ku."
Sai kawai na rumgume Ya Murja ina ƙokarin maida ƙwallar da ta kawo min

"Na gode Ya Murja. Allah ya bar zumunci."

Ta amsa da Amin Amim ta na dariya su Rahila na ta ya mu, haƙiƙa ba abin da ya fi ka ga ɗan'uwanka ya zo ta ya ka farincikin ko aka sin shi, duk da dai ba ma shiri da Ya Murja yau sai ta nuna ma duniya ni ɗin jininta ne Ma'u ce bare domin da ake mganar jiya ba ta zo ba, Amina ta yi karaf ta ce an ce ta je can gidan dangin mijina Walima, kuma ni na faɗa mata yau da safe da na ji ta na cigiyar Ma'u.

"Gaskiya ba ta kyauta ba. Duk zumuncin da ke tsakaninta da yayar mijin Sadiya ba kai kwatan alaqan da ke tsakaninta da Sadiya ba. Maganar gaskiya ba ta kyauta ba."

In ji Ya Murja, Ya Aina ko cewa ta yi" To in ma an gayyaceta can ɗin me ya hana nan ɗin ma ta leƙo? Kome ke tsakaninsu Sadiya zumumci ya wuce wasa"
Rahila ta karɓe da cewa" ballatana ita Sadiya ma tun da Alhaji ya yi sulhu shike nan ta daina faɗa da Ma'u. Ta kira ta a waya ta faɗa mata tana gayyatan ta ita da shema'u.

Amina ta kaÉ—a kai kafin ta ce" To gulma ce ya kai ta amma in ba haka me ya sa sai ta je! Wannan ma fa kamar cin mutumci ne wallahi."
Ya Balki kuma tace wallahi in ta zo sai ta yi mata mgana Ya Aina ta ce ta ƙyaleta ita da kanta za ta yi mata mgana, ni dai ina gefe sun tare min faɗa ban ce komai ba ina ta mirmishi. Daman muna cikin bedroom ɗina ne mun bar su Hauwa acan falon su Jidda suna hira tare da su Farida. Jama'an da na gayyata sun yi min kara sun zo min kaf iyalan Inna mariya da na yan gandun albasa sun zo min, har da matan su Kawu Tasi'u kuma da wuri suka zo, Sameena da wuri ta baro Gwammaja ta dawo gidana da kayanta ta ce nan za ta kwana sai gobe za ta je Rano daga can za ta koma gidan mijinta haƙika na yaba da karamcinta.

Iya imu muka ci taron bikin mu, mun ci waina da alele da zoɓo sai son barka. Ma'u sai wajen uku na rana suka zo ita da Shema'u sun saka kaya iri ɗaya sun chaba kwalliya tare da kanwarta Zainab da Alhaji ƙarami. Ni da ya ke na daina saka sha'anin Ma'u a gabana da fara'a ta na tarbesu lokacin na sanya leshina riga da sikat kayan kuma sun zauna a jikina adon leshin ja ne, domin ni daman ina son jan abu, sai leshin ya yi min kyau na yi kwalliyata mai sauƙi na kashe ɗauri bayan na cire atamfar da na saka da safe na tabbata daga Gwammaja ta ke, kuma a yanayin da suka ganni cikin fara'a da gayu na ya yi musu baza ta sun ɗauka za su zo su ganni cikin kuka da baƙinciki ne, ina lura da su sai bi na suke yi da kallon mamaki ni kuma ina juyi da mazaune na domin akwai su Allah ya ba ni.

Shema'u za ta min shaƙiyanci da cewa" Uwargida a gidan Yallaɓai wannan ba za kalan fa? Ina mata fari na kaɗa mata kugu sannan na juya wuyana gashina da ya sauka ya karkace na baza shi da gyara tsayuwata kafin na ce" Ke ma ba ki ji abin da kika faɗa ne. Uwargida a gidan Yallaɓai fa, kin kuma san cewa daman tun can matar Yallaɓai akwai kashe kala ba sabon abu ba ne wannan."
Munnira na gefe ta ranguɗa ta na faɗin" Wannan gaskiya ne ta Yallaɓai ita belbela daman ai da farin gashin ta a ka gan ta."
Sai ta mika ma Hauwa hannu suka tafa, Faridan Tariq na gefe ta miƙe ta yi juyi kafin ta riƙe hanci tana faɗin" Jama'a ku ta ya ni rangaɗa ma duk wata uwargida guɗa."

Kafin kace me su Munnira sun rikita falon da guɗa, ni dai ina ta dariya ganin har da Ya Balki a masu guɗan. Ni dai na saka Amina ta zubo ma su Ma'u waina da alele, na ɗauka za ta ce sun ƙoshi sai na ga ta fara cin alalen. Amina ce ta yi mata tsiyan sai da yamma ta ke zuwa bikin gidn su?

"Na É—an je Gwammaja ne. Kin san ni duka tudun biyun nawa ne Uwargida da Amaryan."
Chapter 31 · 0% Book details