Sashe 79
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yini na yi a gida ina kunci ni kaɗai. Da su Jidda suka dawo daga makaranta suna tambayan ko mun je makarantar su? Na ce Abban su ne ya je ni ban samu zuwa ba, shi kuma Abban na su sai dare ya zo gidan. Ƙala ban ce masa ba nima bai yi min mgana ba yaran dai suka zagaye shi ya na faɗa musu yadda malaman su suka yaba musu sosai. Baby dai ya ce teacher ɗin ta, ta ce ta fara saka wasa record ɗin ta ya fara ɗan jan baya.
"Ki daina wasa kin ji ko My Baby?
Ha faɗa ya na shafa kanta sai ta gyaɗa masa kai. Kwanto da da ita ya yi a saman jikinsa ya na faɗin" Anty Gimbiya ta ce ki ƙara dakewa za ta siya miki ipad na karatu."
Baby na jin haka ta fara tsalle Yallaɓai ne fa ya yi zaune ya na faɗa musu tare da Antynsu Gimbiya su ka je makarantan na su, suna ta murna ni dai yadda bai ce Sadiya ji ba, nima ko ban nuna na ji ba. Bai jima ba ya yi musu sallama ya wuce ni ina ganin ma zai tafi sai na shige tiolet domin na gaji da ganin yaudaran Yallaɓai ya na ƙara ɓata min rai matuƙa.
Washegari lahadi gidana Yallaɓai zai dawo da yamma. Bayan jiya sun yini tare yau ma tare suka yinin kawai da ya tashi dawowa sai ga shi ya ɗauko min matarsa ta sha gayu cikin wata doguwar rigar yadi mai baza a ƙasa. Ta yi rolling mayafi a saman kanta fuskar nan har tana maiƙo saboda hoda. Bakin nan ya na sheƙi saboda ƙyalin jan baki. Ta kawo ma yara cake ne da donut amma ni na san ba haka ya kawo ta ba, ta rako shi ne ko kuma shi ya ce ta rako shi ba su gaji da ganin juna ba.
Tun kafin mangariba suka shigo gidan har ya fita salla ya bar mu. Ɗakin yara na bar ta tana salla nima na shiga ɗakina na yi, tuwon miyar allayu na yi mana. Har bayan isha'i tana gidan tare muka yi dinner har mamakin yadda Yallaɓai ke kafa kafa da ita na ke yi, ita ko sai wani iyayi ta ke wai ita mai ciki. Duk na gani na nuna ban gani ba, bayan mun gama cin abinci na ga dai Yallabai ya ce zai mai da ta gida har na ka ba shi da niyyar haka sai ma yara da ya kora falon su mu kuma sai ya kunna mana ya zauna saman kujera mai zaman mutum biyu ita kuma Gimbiyar ta na zaune a gefen shi ya na ba ta labarin wani American film da suke haskawa a MbAction.
Ni ko ina kan kujeran Dining ban ta so ba ina kallon ikon Allah kamar ma fa ya manta da ni ne, sai can ne da ya juyo ya ganni sai ya ce" Kika zauna acan?
Sai kawai sa ya sake juyawa ya na ce ma Gimbiya.
"Kin san ita ba ta damu da kallo ba."
Tsabar takaici sai kawai na miƙe ina tattara abubuwan da muka ɓata zuwa kitchen daga can ban dawo ba, falon su Jidda na tsaya na ce su kashe kallon in suna da sauran aikin makaramtan da ba su yi ba su ɗauko su duba gobe akwai makaranta suka ce min to. Daga nan na yi wuceta ɗaki domin ba dole aka yi min da sai na zauna ina kallon wulaƙanci da Yallaɓai ya shirya min a falona ba.
Kai tsaye na shiga tiolet na kama ruwa na dawo na yi shirin kwanciya. Na kwanta kenan sai ga shi ya shigo.
"Kin kwanta ne kuma?
Dago kaina na yi ina kallon shi amma ban yi magana ba.
Amma kaÉ—an ya rage ban amsa mishi da cewa" To kar na kwanta na zauna ina muku gadi."
"Kin bar Daughter ita kaÉ—ai ko?
Kamar na yi masa tsaki sai na fasa kawai sai na mai da kaina saman filo ina faÉ—in" Ba ga ka ba?
Sai ya yi dariya kafin ya ce" Haka ne. To zan mai da ta gida ko za ki zo ku yi sallama ne?
"A'a na riga na kwanta. Ka faÉ—a mata mun gode mu kwana lafiya."
Kamar zai yi magana sai ya fasa ya dai ce Amin ya fice. Ina jin fitar shi da mota wallahi sama da awa ɗaya sannan Yallaɓai ya dawo gidan kuma don ba shi da kunya ya dawo ya na ƙwaƙwumata sai ko na yi masa barcin ƙarya dole ya ƙyaleni, abin da ke ba ni mamaki matar nan ta na da mota amma duk in da za ta je shi zai kaita na rasa gane ita motarta amfanin da ta ke yi da ita. Ko aikinta da ta koma wata rana shi ya ke kaita kuma ya koma ya ɗaukota ranar dai na gaji na yi masa mganar ita motarta ba ta fita ba ce ta ado ce?
"No kawai kin san yanayin da ta ke ciki ni na ce ta daina driving in dai ina kusa zan riƙa kai ta duk in da za ta je."
"Ba shakka."
Na bashi amsa cikin renin wayau ina taɓe baki amma sai ya basar da cewa.
"E mana. Ke da ita kun maida ni direban ku da ƙarfi da ya ji."
Kamar na ce ita dai ka ke yi ma aikin direban ci, ba ni ba sai kuma na fasa ban bashi amsa ba amma Allah na tuba tun ina amarya Yallabai da ko keke bai da shi adaidaita na rika yawo da ƙafata. Duka duka yaushe ya yi motar? Bayan tarewaan mu gidan nan ne fa, kuma ni dai a sananin ba ko'ina Yallaɓai ke samun damar kai ni ba, yawamci na fi yawo a cikin adaidaita. Duka kuma cikin Jidda da cikin Baby haka na riƙa zaryan asibiti a cikin adaidaita, duk bai duba condtion ɗina alokacin ba sai yanzu tun da yar gwal ta yi ciki ai ba zai bar ta ta riƙa tuƙi ba. Tsabar haushi ma ban ƙara tanka ma maganarsa ba na dai ɗauka da ya cigaba da maganganun sa zai kuma gangaro kan cewa nima ya na jigila da ni a motar shi a baya ni ko na yi masa wankin babban bargo don na lura bai san ina masa kawaici ba.
Yallaɓai bai daina kwaso mini matarsa duk ranar girkina ya na kawo min ba. Alhalin ranar girkinta ba na ganin shi sai dare in ya ta so daga wajen aiki ya biyo mu gaisa amma ita in ya na gidana tare suke yini. Na yi musu bakam ina auna tunaninsu na ga daga shi har ita sun maida ni shashasha. Ranar ko na yi niyyar taka musu burki ranar da aka kai sadakin Marwa da kayan saka rana aka saka wata takwas lokacin ta kamallah makaranta ta dawo gida. Ranar daman ya na gidan ta ne, da yamma zai dawo gidana kuma daman tare da Yallaɓai aka je aka yi komai tare da su Kawu Sa'adu.
Bayan sun dawo ne shi ya tsaya gidan Gimbiya ya yi wanka kuma kawai ya ɗaukota suka taho tare. Ni daman ina gida amma suna tafiya Ya Aina ta kirani ta faɗa min an saka rana na riƙe hanci na rangaɗa guɗan farinciki ni kuma na shiga group ɗin gidanmu na sanar da su. Duk farincikin da na ke ciki da na ga Yallaɓai tare da Amaryansa sai da na ji raina ya ɓaci muna zaune afalon bayan ya dawo daga sallar isha'i har da yara gabaɗaya
"Sai kika ji yau dai Finally Kawu ya fara taka matsayin girma."
Yaƙe kawai na yi masa kafin na ce" Wallahi fa yanzu Ya Aina ta kirani ta na faɗa min."
Ita ko Æ´ar iya sai buÉ—e baki ta yi ta na faÉ—in" Ma sha Allah. Allah ya sanya alheri."
Ya amsa mata da Amin kafin ya ce" Lkacin kin haihu za a yi bikin ko?
Ya faÉ—a ya na yi mata wani kallo sai ta kauda kai ta rufe fuska ta na yarfa masa hannu kafin ta ce"
"Kunya na ke ji Daddy"
Ta faɗa cikin shagwaɓa kawai sai Yallaɓai ya kalleni ya na faɗin" Sadiya kin ji ƙanwarki wai kunya ta ke ji in na yi maganar haihuwa."
Kamar na ɗura ma shege ashar haka na ji, haka kurum Yallaɓai na neman ƙure haƙurina. Ai ban san lokacin da na basu amsa dai-dai da kalamansu ba, da ga shi har ita sai da suka kalleni. Amma sai da na ce Jidda da Baby su koma falon su suna ficewa na kalle su ina faɗin.
"Kunyar me? Cikin? Ita ko ba ta ji kunyar yadda ta samu cikin ba ne sai fitowar cikin ne ta ke ji ma kunya?
Sun kalle ni dukkansu kuma daga nan ba su ƙara mgana ba yan jakar uba ai sai ya sauya hira. Kan dai auran Kawu da Marwa ne ya na cewa kowa sai mamaki ya ke yi in ya ji an saka rana ana faɗin ashe dai Abba dai da gaske ya ke yi, tun ina amsa shi har na gaji na yi masa banza na bar ma ta hira saboda na ga sai tsoma baki ta ke yi cikin yanga da iyayi.
Agogon bangon falon na kai ma duba tara har ta gota kawai sai na tashi ina faÉ—in.
"Zo ka ji mana Yallaɓai."
Ya ɗauka wata maganar arziƙi ne ya miƙe ya biyo bayana ya na faɗin" Mu je ta samu ne Sadiya ta? A raina na ce za ka ga samuwa har ɗakin barcin mu na kai shi na rufe ƙofa na tsaya ina kallon shi.
"Me ya faru?
Domin na san ya sha jinin jikin shi ya san mgana ce a bakina.
"Yallaɓai ban ga ne sabon salon da matarka ta fito dashi ba. Ko na ce sabon salon da kai ka fito da shi ba."
"Wani irin sabon salo? Ban ga ne ba?