← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 89

Sashe 87

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Marwa nan gidan su Hauwa ta so muka haɗu da mangariba ta tafi za ta ce gida ta shirya ta na da aikin dare ne ranar. Mu kuma nan gidan su Hauwa muka kwana washegari aka tashi da yinin biki da ɗaurin aure, ni kwata kwata tun bayan saukan mu ba mu yi waya da Yallaɓai ba kuma bai faɗa min zai zo ba, duk da na san zai zo ɗin amma ban ɗauka tare da matarsa za su zo da yara ba sai ganin su Jidda kawai na yi wa ya kawo ku? Wai tare muke da Anty Gimbiya da Abba. Sai ga Khalipa da ita kanta Gimbiyar ɗauke da Anwar kenan shi ya tuko su alhalin ni bai nuna min ma za ta zo ba. Ban nuna mata wani abu ko a fuskata ba muka gaisa. Lokacin ni ban ma yi wanka ba sai daga baya ankon less ɗin da muka yi mu uku muka saka gabaɗayanmu wani marroon da baƙi yi yi mana kyau duk in da muka gifta sai an ce kai leshin nan ya yi kyau. Har cikin gida su Yallaɓai suka shigo Allah ya sanya alheri da shi da Kawu Abba da Tariq sai Musbahu sai Nasir da Muttaka. Sannan a ɗakin samarin gidan su Hauwa suka zauna aka kai musu abinci ni dai ban je ba domin na ga Gimbiya ce ke kai da kawo sai na bar mata amma dai mun je dukkan mu mun gaishe da mazajen namu.

"Madam kin fa samu duniya"

In ji Yallaɓai ya na kallona ni ko sai na kalle shi ina yi masa fari kafin na ce.

"Allah ko! In ma duniyar ce ai kai ka ba ni ita a hannuna Yallaɓai."

"Wannan gaskiya ne Uwargidan Alaji Tafida ba."

Tariq ya faÉ—a ya na dariya Kawu kan cewa ya yi." Ba dole ya ba ta duniyar ba. Saboda ita ce ta san shi tun kafin duniyar ta same shi."

"Tariq ya su Farida? Sai ban gan ta ba."
Na faɗa ina kauda maganar Kawu Abba tun da na ga Gimbiya ta shigo lokacin Yallaɓai sai fama da yara ya ke yi, Khalipa ya manne masa ga Anwar a jikinsa duk sun ƙi bari ma ya ci abinci ni dai ina gefe a raina na ce can ku ƙarata.

"Wallahi ba ta samu zuwa ba saboda makarantar yara."

Tariq ya ba ni amsa, zan yi magana Munnira ta ja ni muka fita waje ta na min raÉ—a.
"Ke na ga matar nan sai wani rawan kafa ta ke yi ne"
Sai na kalleta ban ce komai ba na wuceta ina faÉ—in" Ta yi ta gama Munnira."
Daga haka na koma cikin gida na bar su, can ma aka fara ƙidan ƙwarya muka je can muna chasewa da aka ce filin na yayyen amarya ne, muka shige fili ni da su Hauwa muna ta rawa ana yi mana liƙi sai can da yamma su Jidda suka ce za su tafi Gimbiyar ma ba ta min sallama ba a raina na ce a gayas, to uban gayyar bai min sallama ba ballanta ita.
Amarya cikin garin Kano za a kaita a daran aka tafi da ita amma mu ba mu je ba. Tun da muna gari muka ce sai mu sa rana mu je daga baya.
Ranar a gidan Marwa muka kwana washegari muka yi shirin dawowa gida. An ba mu kayan biki su cincin da dublan da kayan robobin da aka raba can muka bar Hauwa sai ranar talata za ta dawo. Amma tare muka taho da wasu dangin su kuma za su je gidan Amarya.

Ko da na koma gida ba kowa, sai da na buɗe ashe suna can sharaɗa gidan Gimbiya. Yallaɓai bai kirani ba sai ni da kaina da na kira shi na ce na dawo. Shi ne da daddare sai gashi sun taho da yaran har da Khalipa da na ke murnan kwana biyu ya bar ni na huta ashe ba haka ba ne. Ranar ga gajiyan biki hayaniya ta yi yawa a can ba mu wani samun barci, amma yaron nan haka ya hana mu barci a ɗakin su Jidda na kai shi ya kwanta saboda ya fara barci a falo amma sha biyu saura muna kwance a ɗaki muka ji ihun shi dole Yallaɓai ya je ya ɗauko sa ya saka shi a tsakiyarmu kamar wani yaro haka ya tashi cikin dare daga ya ce zai sha ruwa sai ya ce zai ci abinci. Gabaɗaya ya hana ni barci, ni ƴaƴana ba su hana ni barci sai ɗan kishiya. Yaro kamar an haife shi da makirci da kissa a daran Yallaɓai ya tashi ya haɗa masa tea. Ban san yadda aka yi ya cire masa pampers ɗin jikinsa ba, kawai sai farkawa na yi da asuba na ga Khalipa ya kelayamin fitsari a sabuwar katifa ta.

Tsabar baƙin ciki ma na kasa mgana. Wallahi ko su Jidda ba su yi zaman yi min fitsari a kan katifa ba domin tun zamanin napkin shi na ke yi musu in zamu kwanta. Kuma ba na bari su sha ruwa daddare ko su sha tea amma saboda iskanshi shi Yallaɓai cikin dare ma ya ke tashi ya na ɗura ma yaro ruwa ba dole ya yi fitsari ba da na ga kalli wajen har sai da ya yi shaida a zanin gado kawai sai na kalli Yallaɓai lokacin ya dawo daga sallar asuba Khalipa na can ɗakin su Jidda.

"Yallaɓai cire ma Khalipa pampers ka yi? Ji fa yadda ya yi min fitsarin kwance."

Kai tsaye ya ce" E jiya ne ya na ta rigima sai na cire masa sai na ga ma duk ya cika shi da fitsari."
Ban sake magana ba sai shi ne ya É—ago ya kalleni kafin ya ce" Ba komai ai fitsarin yaro ne. Ki kuna fanka kawai ni bari na je can É—akin na É—an runtsa."
Daga haka ya fice ya bar ni ina bin shi da kallon takaici. Sai da na cire zanin gadon sannan na saka ruwa da omo na goge wajen na saki fanka zanin gado kuma na fita waje na jiƙa shi ina ta ɓata rai da sassafe ya sakani wahala, ba fitsarin ne abin haushi ba na ga dai ba jariri ba ne, ba zan hana shi kwana a gidana ba amma ba a ɗakin da na ke kwana da mijina ba har kuma ya kwanta ya yi min fitsari.

Shi ya sa ko su Jidda ba su ga fara'ata ba har shima ko da ya fito na haɗe rai na. Amma bai hana nai yi ma Khalipan wanka na sauya masa kaya ba. Ni kuma na je na wanke zanin gadon da ya yi min fitsari na shanya. Duk da Yallaɓai ya siya mana in ji min wanki amma da hannuna na wanke shi tun da guda ɗaya ne. Da Yallaɓai zai fita nan ya bar min shi wai maman shi ba ta nan za ta je asibiti Anwar ne ya kwana ya na ciwon ciiki. Ya fita ya bar ni ina ta aikin a kitchen ina can ina wanke wanke bayan na gama gyara duka ɗakunan na saka turaran wuta. Cartton na kunna ma Khalipa na yi masa jan ido da cewa in ya sake ya tashi sai na yi masa bulala ashe yaron nan bai ji ba ina can ina wanke wanke shi kuma ya samu dispanser ya danna ya yi min ta min ɓarin ruwa har ya gangaro ya jiƙa min cafet ruwa ne cike fa sai da ya yi rabi da shi kamar an ce na leƙa falon na ci karo da mummunan aikin da ya aika ta min

Na ko kama shi na yi masa bulala biyar, saboda haushi ko ɗana ne ya yi min ɓarnan nan sai na dake shi sai kawai ya fashe da kuka ko tsayawa bi ta kan shi ban yi ba haka ya ja min aiki sai da na naɗe cafet ɗin nan na fita dashi na shanya. Sannan na koma na sake goge wajen yaro nan neman ya yi ya saka min hauka ranar ina can ina aiki amma ina fargaban abin da zan je na tarar na ƙudira a raina zan yi ma Yallabai magana sai dai duk abin da zai ce ya ce. Ga barcin gajiya a idanuwana amma ban isa na kwanta ba domin in na kwanta na san abin da zan ta shi na tarar shi ya sa bayan na gama aikin jikina da zuciyata na son na kwana na huta amma na kasa, tun da in dai na bar shi na kwanta sai ya jawo min gagurumin aiki shi kuma ga shi ba ya barcin rana ballantana mu kwanta tare.

Ba ni na samu na huta ba sai da yamma shima ba barci ba tun da yamma ta yi. Dawowar su Jidda ya sa na shiga ciki na kwanta na dai samun natsuwa kawai. Allah ya sa in da ya yi fitsarin ya bushe sai na shimfiɗa wani sabon zanin gado, saboda gajiya ana sallar isha'i na kwanta tun kafin Yallaɓai ma ya shigo. Na dai haɗa masa abincin sa a dining, ni ban san yadda aka yi ba tun da da wuri na kwanta can cikin barci na ji kuka sannan da muryan Jidda ta na kiran sunan Abba sai na farka a firgice lokacin har Yallaɓai ya farka shima kuma ya kunna hasken ɗakin ma.

Waya ta na jawo a gefen gado na duba lokaci ɗaya da rabi na dare. Hankalina ya tashi na ɗauka wani abu ne sai da na ga Yallaɓai ya buɗe ƙofa sai ga Jidda ta ɗauko Khalipa ya na kuka ya na ganin uban ya maƙale masa ya na kuka, shi kuma Yallabai sai ya rumgume shi ya na faɗin.

"Shii ga Abba nan shii."

"Abba ya tashi ne ya na ta kuka ya na cewa sai an kawo shi wajen ka."

"To Jidda je ki kwanta. Sai da safe."

"Sai da safe."
Chapter 87 · 0% Book details