← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 89

Sashe 59

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko amshi ban yi ba na kashe wayata ina ƙunƙuni ina dalili Yallaɓai na neman ya maida ni yar aikin matarsa daga abin arziƙi ban so yi ba amma haka nan na tashi zan yi mata ban kalli kowa ba sai shi. Mijina ne a kowani hali zan cika Umarninsa, ko faɗa muka yi da Yallaɓai sai dai na yi gaba dashi da kaurace masa amma ba na hana shi abinci zan yi masa komai da na saba, ina bin Umarnin shi saboda na san haƙƙin mijina a kaina shi ya sa na danne komai na yi mata fanten wake ya aiko da hanta da allayahu na saka mata a ciki da ya dawo bayan isha'i ya yi wanka ya ci abinci ya je ya kai mata a wayar ma ya kira ni ta karɓa ta na ta min godiya na ce mata bakomai an zama ɗaya. Bayan mun gama wayar na daɗe zaune ina tunani sai na tuna mganar Alhajinmu da ya ce na yi mata alheri na kuma zauna da ita da alheri in ma ta na da wani sharri Allah zai mayar mata da kayanta.

Kuma ni dai ba ta min komai ba. Laifinta ɗaya ta aure min miji amma ko bayan auran ta na girmamani ta na sona ta na son ƴaƴana ko da ya ke dole ta so ƴaƴana tun da ta na son ubansu sannan nima ta na girmamani sosai sai dai kishi na yau da gobe amma ba zan ce ga wani laifin da ta taɓa yi min ba, tunanin haka ya sa na watsar da mganar Anty Bahijja a cikin raina kuma Yallaɓai in dai bai manta ba sai ya yi mata mgana daman gashi ba shiri ita ta saki nono ya kama akwai faɗan saƙo da saƙo a tsakanin su.

Kafin Yallaɓai ya dawo Marwa na kira da wayar Ya Aina ina tambayanta yadda suke ciki da Kawu nan ta ke faɗa min ma gobe ya ce zai zo ya kawo mata waya ina dariya na ce" To Madalla haka na ke son ji."
Ita kunya ya hana ta mgana sai Ya Aina ta ba ma wayar muka gaisa.

"Ya jikin abokiyar zaman ki? Ɗazu Murja ta kira ni wai Ma'u ta faɗa mata kishiyarki ba ta da lafiya ta na kwance a asibiti ya kamata mu leƙa."

Ban yi mamakin abin da Ma'u ta ce ba kuma ban yi ma Ya Aina munafunci ba kai tsaye na ce" Ya Aina kar ku wani zo don Allah ta ji sauki kuma ga ni ina zuwa Ma'un ma ta je duk bai isa ba! Sai kun zo?

"Kuma fa haka ne. To shikenan kya mata sannu. "
Na amsa mata da zan faÉ—a mata.
"Me ke damun ta hala?
"Ciki gare ta sai ya É—an samu rauni an dai ce ta samu cikakken hutu."
Ya Aina ta ce Allah ya ingata ya raba lafiya.
Daga nan muka yo sallama ba daɗewa Yallaɓai ya dawo ya na faɗa min na ga yadda Gimbiya ta sha fanten waken nan kuwa?

"Ko?

Na faɗa ina kallon shi, ya na zama saman kujera ya ke sake faɗin" Wallahi. Ta yi ta santi ta ce na ƙara gode miki."
"Ayya ai bakomai."
Na faɗa kai tsaye akwai sauran ragowan faten wake sai na kawo ma Yallaɓai ya sha kaɗan sai ya ɗan sha ruwan zafi ko da ya dawo su Jidda sun yi barci ni da shi ne muka yi ta kallo muna hira sai wajen sha biyun dare muka kwanta.

Da safiyar asabar ba makaranta Tahfez kuma yara sun makara ya sa na ce su haƙura sai gobe kawai. Yallaɓai ya fita ba daɗewa sai ga shi ya dawo ina kitchen ina wanke wanke Saude ba ta nan sun je ƙauyen Gwarzo biki, Jidda na can ɗakin su na ce ta gyara Baby kuma na gaban Tibi ta na kallon Cartoon
Ashe mantuwa ya yi ya dawo ɗauka a lokacin ne ya ke faɗa min suna saka rai yau ko gobe za a sallami Gimbiya na ce Allah ya sa domin ta fi sati a asibitin kuma ta ji sauƙi alhamdulillah.

Ranar ban ma saka a raina zan je asibitin ba sai da Hauwa ta zo ta ce ba ta je ba, saboda ba ta nan taje Rano, jin haka ya sa na ce bari na shirya muje tare har ma Hauwa ta kira Munnira ita kuma sai ta ce shekarajiya Jamila ta biyo mata suka je amma tun da za mu je ba ri ta shirya mu jira ta sai mu tafi gabaÉ—aya. Haka ko aka yi sai da muka jira ta ta zo muka tafi tare na bar ma Jidda gidan ita da Baby.

Mun je mun iske asibitin cike da mutane su Anty Bahijja ne da su Anty Maimuna. Halima Suwaiba, Nasara sai Jawaherr da ta ce jiya ta zo gida hutun semister, Maman farko ba ta nan ta koma gida ta yi wanka ta huta, mun gaggaisa da kowa da kowa cikin sakewa amma ita Anty Bahijja sai da ta saƙa mana mgana.

"Uwargida da tawagan ta."

Ta faÉ—a ta na dariya ni na san da sigan cin mutumci ne ta yi maaganar shi ya sa nima na mayar mata da martani.
"Uhm Anty Bahijja yar tawagan Amarya kuma ba "
To zan zauna ne ta na gaya min mgana me na yi mata? Da na faɗi haka sai ta wayance da dariya aka yi dariyan gabaɗaya kowa na ciki na ciki mun gaisa da Gimbiyar ta ji sauki itama ta sake faɗa min yau ko gobe likita ya ce za a sallameta na ce Allah ya ƙara lafiya.

An cika É—akin ana ta hira shi ne ma muka ji Anty Bahijja na waya da Hajiyar Tafida ana mganar wanda za a samo daga rano zai zauna tare da Gimbiya amma kamar ba a samu ba kowa na da iyalai da abin yi, bayan ta gama wayar ta kalli Anty Maimuna ta na faÉ—in" Kin ji ita kanta Baaba Asma'un da na hango ba ta da lafiya.'

"Topha. Ba dai a samu mai zuwa ya zauna da itan ba kenan?

"Ba a samu ba kam."

"To ta koma wajen Nene kawai ta zauna ba shike nan ba."

Anty Bahijja ta ce" Nima haka na ce da farko to kin san halin Tafida da taurin kai ya ce wai Nene na fama da kanta itama. Kuma na kawo hujjan ga su Maman farko ga iya ai duk za su kula da ita ya ce a'a a samo wacce za ta zauna da ita."

"Wallahi kuwa. To da ya ce bai yarda ba yanzu da ba a samu mai zaman ba ya zai yi?

"Shi dai ya sani. Abin haushin ma ita Mimisco ta goya masa baya. Shi fa shegen nuna iko ne da shi."

Ni dai ina gefe in jin su ban tofa ba daga karshe ma ni da Hauwa muka fara tafiya salla tun da ana ta kiran sallar azahar Munnira ba ta yi ta na hutu shi ya sa ba ta biyo mu ba. Bayan ma mun idar da sallar mun zauna a wajen cikin asibitin muna ta hira da Hauwa. Ta na gaya min ba in da labarin cikin Gimbiya bai za ga ba na ce ai ya za ga tun da su Anty Bahijja na raye.

"Ji fa suke yi kamar Tafida bai taɓa haihuwa ba sai yanzu."

Ina murmishin takaici kafin na ce" Bai taɓa ba mana. Ni ai bare ce saboda haka ƴaƴana ma bare ne. Ita kuma ta su ce haka ma ƴaƴan da za ta haifa ma kin ga ai na su ne."
Hauwa ta rike baki kafin ta ce" Lalle kam"
Ban ƙara mgana ba amma ina ƙokarin danne wani abu dake ta so min a ƙasan zuciyata.

Bayan mun koma ɗakin har dai lokacin Anty Bahijja na ta buge bugen waya amma ba a dace ba. To kowa na da abin yi wata mata ce za ta yarda a ɗaukota a zaunar da ita waje ɗaya sama da wata ɗaya tun da na ji Halima na faɗin likita ya ce bedrest za ta yi na sati biyar ko botiki ba a yarda ta ɗauka ba ai neman mai zaman akwai wahala Yallaɓai kuma ba mace ba ne ballatana su ce ya zauna ya kula da ita dole dai ƙanwar naƙi wata macen za su nema. Har muka baro asibitin gabda mangariba ba a dace ba ina jin Anty Maimuna har Nene ta kira ta na faɗa mata ba a samu mai zama ba kowa suka kira sai ya ce ga uzurin shi kila Nenen ta ce a dawo da Gimbiyar wajenta sai na ji ta na cewa.

"To Nene Tafidan ya hana. Sai dai ki yi masa mgana ƙila ke ya saurare ki."

Daga karshe na ji ta na cewa to shikenan.
Mun rabu da su Hauwa a bakin asibiti na hau adaidaita zuwa gida ban san abin da ya faru ba, can bayan isha'i Yallaɓai ya na dawowa wanka kawai ya yi ko abinci bai ci ya ce mu je ɗaki zai yi magana da ni, ina falo ne ma ina koya ma Baby aikin da aka ba ta a makaranta da na ce ma ya bari mu gani sai gani na yi ya ƙariso ya kama hannuna ya mikar da ni tsaye ya kuma nufi har korido ya na faɗin.

"Ƙarisa mata aikin Jidda."

"To Abba."

Ta faÉ—a cikin sanyin ta damam ta na gefe itama ta na yin nata.

"Mene ne ya faru Yallaɓai?

Na faÉ—a ina biye da shi a baya bai direni ko'ina ba sai da muka shiga cikin bedroom É—in mu, kan gado ya zaunar da ni tun da na ga ya jawo stool É—in madubi ya zauna na san akwai mgana ko wani abu ya faru.

"Mene ne ya faru Yallaɓai? Ka fara ba ni tsoro."

Na faÉ—a ina kallon shi ganin kamar ba ya cikin natsuwarsa.

"Sadiya."

"Na'am me ya faru?

Na amsa shi a gaggauce sai ya sauke ajiyar zuciya ya riƙe hannayena duka biyu tun da na ga haka jikina ya ba ni cutavta Yallaɓai zai yi tun da na ga wannan ladabin na shi.

"Me kake so?
Chapter 59 · 0% Book details