Sashe 61
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na amsa masa a takaice saboda ni nasan can ya ke son ya ce zai kwana kunya ce ta hana shi mgana. Ina gidan a gaban idanuwana Yallaɓai ya shige da Gimbiya ɗaki suka sakayo ƙofa sai da na yi kuka karshenta dai Jidda da Baby na ɗauko zuwa ɗaki na suka taya ni kwana amma ji na ke yi kamar ba zan iya ba. Muna gida ɗaya kusa da ɗakin juna amma Yallaɓai ba ya tare da ni ya na tare da wata matar ba ni ba, lalle mata suna ƙokari matan da ake yi musu kishiya suna zama da su a gida ɗaya ya tabbata za a kira su Jarumai.
*Janafty*
*TKG016*
Tun dawowar Gimbiya gidana na ke ta ganin ikon Allah a wajen Yallaɓai da dangin shi, su rawan ƙafa shima rawan ƙafa, ni dai ina gefe ina ganin komai kamar al'amara kamar mafarki. A ce yau wai a gaban idanuwana Yallaɓai ke ririta wata macen ba ni ba, kuma a cikin gidana ƴan'uwansa ke zarya saboda wata ba ni ba. Rayuwa kenan abin da ya baka dariya wata rana shi zai koma ya na ba ka tsoro.
Anty Bahijja ku san kullum sai ta zo gidan nan sai ka ce ni ɗin zan cutar da Gimbiyar ne. Kuma in ta zo ta riƙa bibiya kenan me Gimbiya ta ci? Kar a riƙa ba ta abincin da ba ta so kar a riƙa tashin ta daga barci in ta kwanta daga ta ce wannan sai ta ce wannan, ni dai ba na wahalar da kaina wajen mgana, saboda duk abin da zan faɗa ba shi zai sa komai ya koma yadda ya ke a baya ba shi ya sa kawai na kawo ido na saka musu daga shi har ƴan'uwan na shi.
Abu ɗaya na ke yi shi ne ina girki sannan in zan dafa na kan shiga na ji ra'ayinta in ma na dafa abin da ba ta so in har ta ce min ga abin da ta ke so ina dafa mata ba zai gagare ni ba. Don Allah na ke yi don kuma ita da Yallaɓai sannan in ya fita ina shiga na duba ta in na ji ta shuru saboda kar wani abu ya faru a ce ai ina gidan amma ban sani ba, ba ta cika fitowa falo da rana ba sai dare shima sai Yallaɓai ya matsa mata, yara kuma suna shiga wajenta suna ɗeɓe mata kewa ni dai tsakanina da ita sai mutumtatawa na kama girmana na riƙe gam ko da na gani ɗin ba na ma nuna na gani ɗin amma domin ba a yin abubuwa ba ana yin abubuwa, kawai dai ina kauda kaina ne, in na ga Yallaɓai na wani ɓare ɓare a kan Gimbiya kawai kai na ke girgizawa, sannan nima sai ki ga ya na wani min rawan baki ba saboda komai ba ne saboda matarsa ce ya ga ta na zaune damu ina kula da ita da zuciya ɗaya. Kallon shi kawai na ke yi amma ni a idanuwana kar na ke kallon shi ba wani abin da Yallaɓai zai yi da ban gane manufarsa ba Allah na tuba ai jiya ba yau ba.
Kowa ya ji Gimbiya na gidana sai ya yi mamaki Munnira ta doka min kira ta na min kumfar bakin a gida ne zan sama ma kishiya wajen zama ta na kwance ina yi mata aiki? Ina dariya na ce" To miye a ciki Munnira?
"Akwai mana. Kuma miji ya kwana da ita?
"E"
Na faÉ—a ina dariya wata ashar ta laulayo da sai da na ce"Ke Munnira ko ni da haÉ—a iri da katsina ban iya wannan ashar É—in ba."
"Abin ne na ji kamar ma na yi zage zage"
"Me ye a ciki? To ai ta aure shi to gida kuma don ta zauna ai duk abu É—aya ne Munnira. Ni dai fata na mu rabu lafiya kawai "
Duk yadda ta so ta nuna min kar na yarda ta zauna ba ta aiki kuma ina bata miji ban nuna na gane ba, ni yanzu me zai dame ni? Abin da na ke ma gudu da kishi tuni ya faru to me ya yi saura? Ciki gare ta fa kuma cikin ba na kowa ba sai na Yallaɓai to me ya yi saura? Babu saboda haka mganar gida ko kwana ƙaramin abu ne a waje na tunda na iya hakuri na bari muka raba mijin da ita ai kuma an gama mgana.
Daman ni a raina na yi niyyar na ce Yallaɓai ya yi sati a ɗakin Gimbiya ban dai riga na furta masa ba amma ina da niyyar haka har a cikin raina. Ranar da ya cika kwana uku a ɗakin Gimbiya ina shirin sai ya dawo da daddare na ce masa kawai ya yi mata sati kafin ya dawo wajena amma sai na ga da safiyar Allah Yallaɓai ya fito min da munafuci wai ni Yallabai zai mayar ƙaramar yarinya muna karyawa a saman dining ni da shi yara sun tafi makaranta. Gimbiya kuma ta na ciki ba ta tashi ba tukunna. Sai ya kalleni ya na min duniyan cin da ya koya tun da ya yi aure nan.
"Abar ƙaunata."
Sai na kalle shi amma ban yi magana ba.
"Na gode."
"Wannan godiyar fa?
"Ta ki ce, ki karɓa da martabawa."
Sai na yi mirmishii kafin na ce" To shike nan na karɓa."
Tun da na ga yanayin shi na san cewa tabbas wani abu ya ke so, shi ya sa sai wani kashe murya ya ke yi ya na wani ja na da hira, sai faɗa min ya ke yi yanzu kwangila biyu ne a kan tuburin shi akwai na gina wani ƙaramin ma'aikata sannan akwai ma na Kaduna again faɗa min ya ke yi wattanin nan ya na ta samun aiki sai godiya.
"Ma sha Allah. Allah ya sa albarka ya kuma ba da sa'a."
Ya amsa min da Amin ya na faɗa min zuwa gaba in komai ya dai dai ta, ya na so shima ya gina kamfanin shi ko ƙarami ne kafin zuwa gaba, ni kuma sai na ce ai hakan ya yi saboda komai na son cigaba, kuma babbar cigaba ne a gare shi tun da ya na samun manyan kwangiloli mun daɗe muna tattauna abin da ya shafi aiki sannan muka ganganro kan maganar Gimbiya wai ni Yallaɓai zai zaunar ya na kallo na ya na min bariki da munafuncin su na maza.
"Ina faÉ—a miki jiya fa Daugther sai ciwon ciki cikin dare."
"Subhanallah me ya faru?
"Ni ma ban sani ba, ta É—an yi kukan cikin ne amma ina ba ta mganinta sai kuma ya lafa sannan ta yi barci."
"Allah ya ƙara lafiya. Ko dai za ku je asibiti ne?
Sai ya girgiza min kai kafin ya ce" Na ce mu je asibiti ta ce min wai cikin ya bari."
Sai na kalle shi amma ban yi mgana ba sai na ji ya cigaba da cewa" Ni tunani ma dare Sadiya. Amma dai na ce ga waya nan tun da muna tare in wani abu ya faru kawai sai ta kira ni ko?
Ƙura masa ido na yi ina kallon shi sai ya ƙara cewa" Ko? Na ce ai ga waya ma da ta ji wani abu ta kirani ko ta kira ki."
Har Yallaɓai ya gama lissafin kwanakin shi ya ƙare a ɗakin Gimbiya ba ya so ya ce min zai riƙa kwana a can saboda kar cikin dare wani abu ya faru kai tsaye shi ne zai shiryamin alaye kamar ni ɗin ƙaramar yarinya ce.
"Ba ki ce komai ba?
Ya faÉ—a ya na goge bakin shi da Tissue, sai na yi masa wani irin kallo kafin na yi mirmishi.
"Me zan ce! Ai ba sai ta kai ga haka ba. Daman ina shirin na faÉ—a maka cewa ka yi zaman ka a É—akin Gimbiya har ta samu lafiya ta koma gidan ta."
"Saboda mene?
Ya faÉ—a ya na kallona irin me ya sa kika min haka É—in nan.
"Saboda cikin dare mana? Ba fata mu ke yi ba in wani abu ya faru kiran waya zai yi wahala gwara dai ka na kusa É—in zai fi."
"Ban gane ba."
Ya faɗa ya na kallona ni kuma sai na miƙe ina tattara kwanakun da muka yi amfani da su lokaci ɗaya ina faɗin" Shi ne na ce ka cigaba kawai da kwana tare da ita har ta samu lafiya ta koma gidan ta."
Ina gama faɗin haka na kwashi kayan hannuna na bar masa falon, ni sai ma ya ba ni dariya daman wai Yallaɓai ya iya alayen magana haka? Ai ban taɓa sani ba sai yau ƙwalla suka cika min ƙwarmin idanuwana yau har an yi lokacin da Yallaɓai ba ya son kwana dani sai da wata macen. Har an zo gabar da zai ji gwara ya riƙa kwana da mataras sama da ni. Ni ce fa Sadiya. Sadiyar shi da ban taɓa tunanin wata rana da za ta so Yallaɓai ya ririta wata mace bayan ni ba, sai ga shi ya na faruwa a lokacin kusan ma da ban yi tunani ba.
Ina kitchen din ya biyo ni ya na borin kunya. To borin kunya mana Yallaɓai ya kalli tsabar idanuwana ya na faɗin" ban gane na koma wajen ta gabaɗaya ba? Da wa kika yi shawara kafin ki yanke hukunci?
Ni ko na ce ai maganar ba ta bukatar shawara shi ya sa ban faÉ—a masa ba. Sai ya fara kunyata kan shi ya na faÉ—in" To ni ban amince ba. Ki ma bar wannan mganar."