← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 89

Sashe 85

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faɗa ya na shafa kumatunsa. Kallon Yallaɓai kawai na ke yi in ya na wani abun, faɗa ya ke yi itama Gimbiya haka ta ke fama da shi. A raina na ce muna fama dai ni fa sai dai na bar Yallaɓai da Khalipa domin a daran ma wasa suka fara yaron na bin shi da bindiga shi kuma ya na ɓoyewa shi da Baby saboda ita ce mai son wasa. Jidda kam ba ruwanta da wannan shanshanci shi ya sa na ke sonta ta na da aji sosai.

Ɗaki na koma na yi kwanciya ta ban ma san shigowarsa ba, sai cikin dare na farka na gan shi maƙale da Khalipa wani abu ya kawo min wuya amma ban yi wani abu ba, ji na yi kamar na koma ɗayan ɗakin na kwana amma sai na fasa. Da safe muna karyawa bayan yara sun tafi makaranta. Yallaɓai ya siya sabuwar mota wata bakar benz tsohuwar tashi kuma ta na hannun salisu shi ke kai yara makaranta a ciki sai cefane.

"Daughter ta ce a saka Khalipa a makaranta na ce laa ba yanzu baa"

Kallon shi na yi lokacin ina tura dankalin a bakina. Ko a yanzun ma Khalipan na kan jikin shi ya na bashi dankalin a baki, ko fa fita Yallabai zai yi in ba da shi zai fita sai da dubara in kuma ya duba bai gan shi ba haka zai ta rigima to ya riga ya sabar masa.

"Gaskiya kam a saka shi a Baby cllas ba."

Na faÉ—a ina haÉ—iye abin da ke bakina.
Amma sai Yallaɓai ya ce ba yanzu ba sai ya shekara biyar.

"To me ya sa? Na ga dai  da bakin shi ko?
Kuma ko Baby ta na da shekara huÉ—u ka saka ta a makaranta."

"Da  Khalipa da Baby ba ɗaya suke ba. Shi fa ya shaƙu da ni kina tunanin zai zauna a makaranta?

Wani kallo na wurga masa kafin na ce" Tabbas ba É—aya suke ba na ga alama."
Daga haka ban ƙara kula sa ba har ya gama mganganun sa. Tare suka fita da Khalipa ya ce zai kai shi gida a raina na ce a gayas daman na gaji ina so na kwanta. Bayan kwana biyu da ya dawo gidana bai zo da Khalipa fa a cewarsa uwar ce ta ce ba zai biyo shi ba.

"Ta ce wai ana takura miki. Ni kuma na ce mata duk É—aya ne da nan É—in da can duk in da Khalipa ya ke so zai zauna."

Kallon musulunci ma bai samu ba ya gama gyaran zencen sa ya yi shuru. Da safe kuma again muna ƙaryawa ya fara isa ta da labarin shagon Gimbiya na yi masa kasaƙe kawai ina jin sa kuma ina kallon shi.

"Shagon ma fa ta ce ya yi kaɗan kaya ba sa wata suke ƙarewa yanzu fa har jiran oder ta ke yi "

"Uhm Allah ya sa albarka."

Na faÉ—a ina son kauda mganar amma ina shi a dole sai ya faÉ—a min.

"Ina gaya miki ana siya kayan ta sosai duk abokaina da abokan kasuwancina wajenta suke ma matan su siyayya."

"Ka kyauta Marketing manager."

Na watsa masa mgana amma sai na ga ya yi dariya kafin ya ce" Haka Daugther ta ce ta naÉ—a ni markerting manager a shagon ta na iya talla."
Kamar wani shashasha ya na ta dariya ji na yi kamar ina make sa da kofin hannuna amma sai na basar gani na yi ya dameni abu kaÉ—an ya ce Daugther daman ni sunan nan wallahi ya daÉ—e ya na ba ni haushi kawai yau na ce bari na yi masa mgana.

"Yallaɓai kana da abin mamaki."

"Na me fa?

Ya tambaya ya na kallona.

"Ka auri mace har ka yi mata ciki ta haihu sau biyu amma ka na ta wani kiranta da sunan Daugther don Allah miye ma'anar wannan sunan? Ƴa? To kai yarka daman ka aura ka ke yi ma ciki tana haihuwa?

"Ban gane ba"

Ya faÉ—a bayan ya rage fara'aran fuskar shi.

"Ka duk gane abin da na ke nufi."

"To sunan Daugther É—in ke kuma ya tsaya miki a rai?
Kike kishi da sunan?

Ya faÉ—a ya na kallona kafin in samu zarafin mgana a fusace ya cigaba da faÉ—in" Kin ba ni mamaki me ya sa yanzu kwata kwata ba ki tauna mgana in za ki faÉ—a min ne? Ai kin san matsayin ta a wajena da matsayin sunan tun kafim mu yi aure haka na ke kiranta kuma ya kama bakina. Sai a ka ce kuma haramun ne don ta na matata kar na ce mata Daugther?

"Ba haka na ke nufi ba."

Na faɗa ina ƙoƙarin kare kaina ganin ya taso min

"Haka kike nufi mana. Sai an yi magana ki ce ke kin girma kaza da kaza, kin girman ne kike yin abin da kike yi? Sunan mai sai kin yi masa wata fassaran? Ashe ita Allah ya jiƙanta ba domin ta mutu ba da sai ta haɗiye zuciya ta mutu. Wani irin suna ne ban kira ki da shi a gaban ta ba? Wallahi ba ta taɓa mgana ko ta nuna rashin jin daɗin ba, ban taɓa kiran ta da sunan soyayya ba ke fa! Ba sunan ƙaunar da ban kiraki da shi ba karshen ta dai to ke ɗin ce na ke kira abar ƙaunata a gaban ta, ba ta taɓa mgana ba sai ke? Don ina kiran ta Daugther? Ba ki son ji ne? To sai dai ki toshe kunnuwanki domin ba zan iya daina kiran ta da wannan sunan ba."

  "Ka yi haƙuri."

Na samu kaina da furtawa a cikin raina ina mai nadaman fara yi masa mganar. Daga mgana sai kawai cibi ya zama ƙari.

"Ba maganar haƙuri ba ce. Ki gyara a matsayin ki na babba kar ki yi abin da za ta ji ko ta gani girman ki ya zube a wajen ta."

Ya na gama faɗin haka ya miƙe a fusace ya shige ciki sai ga shi ya dawo da key ɗin mota daman a shirye ya ke ya fice ya na faɗin.

"Sai na dawo."

"A dawo lafiyan"

Ko amsa ni bai yi ba ina jin tashin motarsa da ya dawo ma zai rufe get ɗin da ƙarfi ya tura shi har sai da ina daga falo na ji wani garam! Na riƙe baki ina faɗin ikon Allah!

*Janafty*
*TKG020C20c*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX

Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

Sama da mintina goma da fitar Yallaɓai amma na kasa ko da motsa ɗan yatsa na saboda da al'ajabi daga mgana sai cibi ya zama ƙari.? Har ya na min wani gorin ya na kirana Abar ƙaunarsa ni na saka shi? Ban da ma gulma yaushe ne ya fara kirana da wannan sunan? Ba sai da ya yo min kishiya ba ne ya fara min sanaben kirana da sunaye kala kala. Sannan in zai kirani da wannan sunan sai in zai min yaudaran su na maza ko ya na so ya raina min wayau amma shi ne har ya na yi min gori.

Abin fa ya tsaya min a zuciya cikin sanyin jiki na miƙe ina tattara tarkacen abubuwan da muka ɓata zuwa kitchen. Na gaji baya na har ciwo ya ke yi na saka anemin wata ƴar aiki, amma ba a samu ba can kwanaki na yi ma Inna Mariya mgana ta kawo min wata yar anguwan su amma ko sati ba ta yi da fara zuwa ba na ce ta bar shi kawai saboda ba ta iya aikin ba in ma ta yi sai na sake yi, in za ta yi shara bara da bana in mopping ne ta jiƙa min gida da ruwa. In kuma wanke wanke ne duk ta haɗe masu karni waje ɗaya kuma su yi ta warin omo ba ta wankewa da kyau ballantana ta ɗaureye su da kyau shi ya sa kawai na haƙura amma ni kaina na san zai yi wahala na samu mai aiki kamar Saude.

Ɗaki na koma na zauna a gefen gado cikin sanyin jiki. Na rasa me ke min daɗi haka kurum zuciyata sai ta cunkushe, na zauna shuru kawai ina ta nazarin rayuwa ƙaran wayata da ke gefena ya dawo dani daga tunani mai zurfin da na faɗa ina dubawa sai na ga Munnira ce amma har wayar ta katse sai na kira ta daga baya. Duk da ban san dalilin kiran ba amma ina tunanin kan batun bikin autar su Hauwa ne Sakina da za a yi nan da sati biyu. Mun yi ankon can Rano sannan mu ma mun fitar da anko mu uku.

Saboda duk duniya Hauwa ba ta da wasu ƙawaye makusanta ta a Kano irin ni da Munnira. Haka nima duk da dai ga su facololina amma kuma sun riga sun zama aminaina ma su taya ni kuka in dariya ne mu yi tare in kuma na baƙin ciki ne su ta ya ni su ne mutane na farko bayan iyayena da ƴan'uwana ma su zama kusa da ni a duk yanayin farinciki ko baƙin ciki. Nima shi ya sa in sha'anin su ne na ke ɗaukan shi da muhimmaci yanzu ma muna maganar gudummuwar da zamu haɗa ma Mamansu Hauwa mu aika da shi kafin lokacin bikin ne.

Nima har wayar ta katse ba ta ɗauka ba sai na ƙyaleta na miƙe kenan zan bar ɗakin sai ga shi ta sake kirana sai na koma na zauna. Cikin fara'a na ɗaga kiran ina faɗin.
" Mata a gidan Nasiru."
"Uwargidan Alhaji Injiniya Tafida ba"
Chapter 85 · 0% Book details