Sashe 56
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni na zaunar da Marwa na yi mata bayani ta na jin kunya ta rufe fuska ta na faÉ—in" Umma abokin Kawu fa kika ce? Ina dariya na ce" E to mi ye a ciki? Zan yi matukar farinciki in haka ta faru ina tunanin gobe ko jibi zai zo ya ganki. Marwa Kawu Abba ba shi da matsala ki ba shi dama kin ji ko?
Sai ta gyaÉ—a min kai kafin ta ce" To Umma in sha Allahu."
Na ma ɗauka a ranar zai zo amma sai bai zo ba mun yi waya da Yallaɓai ya ɗauko Gimbiya sun dawo gida ya ce min ba ta da lafiya ta na fama da ciwon mara da safe za su je asibiti na ce Allah ya sauwaƙe.
Washegari Kawu Abba da kanshi ya kirani ya ce zai zo. Marwan na gidana ne? Na ce ta na gidana da yau za ta koma gida amma tunda ya na tafe sai gobe a lokacin da muka yi wayar na faɗa masa ba ta nan ta je asibiti ta na da aikin safe sai biyu na rana za ta dawo sai ya ce min zai shigo da yamma in sha Allahu. Mun gama wayar da shi kenan Yallaɓai ya kirani.
"Sadiya Albishirin ki "
Ina ɗauka abin da ya fara ce min kenan duk da ban sani ba amma a raina na san abin da zai faɗa min ba na raba ɗayan biyu tun da na ji Yallaɓai farincikinsa ya ƙasa ɓoyuwa.
"Goro fari ƙal. Me ya faru?
"Daughter tana da ciki. Wata biyu Sadiya."
Sai na danne abin da ke taso min na washe baki ina faɗin" Alhamdulillah Ma sha Allah barka da arziƙi Yallaɓai Allah ya raba su lafiya."
Ya amsa min da Amin Amin sannan ya ce ni ya fara kira ya sanar ma wa, sai na ji daÉ—in haka ko bakomai ya karramani kuma na ji daÉ—i na yaba. Jin haka yasa na ce ya ba ni Gimbiyar na yi mata sannu sai ya ce ta na ciki tare da likita ya fito ne daman ya kirani sai na ce shikenan in sun koma gida zan kira shi sai ya ba ni ita na yi mata sannu.
Duk yadda zuciyata ke son kaɗaicewa ta yi damuwa ban ba ta damar haka ba. Na taya Yallaɓai murna kwarai kusan shekaru bakwai ne ba a sake yi masa haihuwa ba dole ya yi farinciki amma na yi hawaye tare da fatan nima Allah ya sake ba ni ba domin ban gode masa ba a'a na gode masa ina kuma fatan ya ƙara min.
Marwa ta na dawowa na faɗa mata ta shirya Kawu zai zo duk sai ta daburce daga karshe ni ce na taya ta shiryawa bayan na saka ta yi masa girki jalop ɗin shinkafa mai karas da gabeji. Ana idar da sallar la'asar sai ga shi ya iso ni na fara fita muka gaisa su Kawu an sha kwalliya za a burge Marwatu ta bakin Yallaɓai ba.
"Yallaɓan kuma ba ya nan Kawu Abba."
"E mun yi waya. Ya na can baki ya ƙi rufuwa Saudatu ta na da juna biyu."
"E wallahi."
"To Allah ya raba su lafiya. Mun yi mgana ya ce zai shigo kafin na tafi "
Sai na amsa masa da toh na kuma ciki na turo Marwatu da farantin ruwa na ce in sun gama gaisawa ta koma ta É—auko abinci Jidda dama ba sa nan yau suka koma makaranta sai shidda saura za su dawo gida.
Bederoom na koma na ɗau wayata na kunna data. Ai na ga ruwan status. Anty Bahijja ta saka Ni'imar haihuwa za ta ƙara sauka a gidan Tafidan Nene Ubangiji Allah ya riƙa musu ya tsole idon maƙiya saboda na shaka mata haushi na tagging ɗin status ɗin na shiga na ce" Amin ya rabb mun gode. Ai ni Yallaɓai ya fara kira a wayar ya sanar min da cewa mun samu ƙaruwa."
Ta gani amma ba ta yi mini mgana ba Anty Maimuna kuma har da saka hoton Gimbiya ta na cewa" A karon farko Hajiyar Tafida da Nene za su samu jika na farko da tsatson ahalinsu. Congratulatin Mutanen Rano da kewayenta gabaÉ—aya."
Itama na shiga na ce mata Amin na ga har Naja'atu ta saka yadda kika san su Jidda ba ƴaƴa ba ne a bola aka tsinto su gajiya na yi da ganin takaici na kashe data ko na ce kiran Yallaɓai ya katse ni. Bayan mun gaisa sai ya haɗa ni da Gimbiya na yi mata sannu sun dawo gida kuma na ji hayaniya kenan gidan na cike da su Anty Bahijja domin ni na san ko kowa bai je ba ita sai ta je, mun yi sallama ya ce min zai shigo gidan anjuma.
"Su Kawu ana can ana yaÉ—a manufa ko?
Ina dariya na ce" Ban sani ba."
"Su kaÉ—ai kika bari a falo Sadiya? Kawu fa Tuzuru ne kin sani."
Ina ƙara yin wata dariyar na ce" Ka zo sai ka saka ido "
Ya ko ce ga shi nan zuwa sannan muka sallama ba daɗewa sai ga shi, sai da ya gama yi ma Kawu tsiya a falo sannan ya ƙariso ciki yunwa ya ke ji na saka mai abinci ya na ci ya na faɗa min tun shayin safe bai ci abinci ba a raina na ce na ga alama kam domin ya ci abinci sosai.
"Ya mai jiki?
"Ta ji sauƙi sun ce ta samu hutu ne. Shi ne na ke tunanin wa zai zauna da ita Jidda kin ga akwai makaranta."
Sai na jinjina kai kafin na ce" Gaskiya ne. To kai ka koma can da kwana mana har ta ɗan samu ƙwarin jiki"
"Ni kuma?
Sai ya kalleni ya na mai nuna kan shi sai na gyaɗa masa kai lokaci ɗaya ina faɗin" E. Ka je bakomai ai lalura ce."
Sai ga shi a gabana ya rumgumeni ya na faɗin" Na gode. Allah ya iya miki Sadiya ta." Na amsa da Amin sai hira ta buɗe ya na faɗa min yau duk abin da ta ci sai da ta amayar da shi sai da Anty Bahijja ta zo mata da kunin tsamiya daga gidanta shi ta sha ya zauna mata. Ya na ma faɗa min ta na can gidan ya baro ta shi ne ya samu sararin zuwa nan ni dai ina ta bin sa ne ka nuna wani abu a ce kana baƙin ciki.
Â
Yana gidan har mangariba suka fita tare da Kawu. Marwa ta dawo min da fara'an ta ta na gaya min ya ce ta ba shi lambarta ta ce wayarta ta lalace ya ce to zai kawo mata waya.
"Umma to Baba zai bari na karɓa?
Ina dariya na ce" Me zai hana! Ai ya je ya ga Baba. Kuma baban ne ya bashi izini Marwanatu."
Sai ta dukar da kai ta na jin kunya ni kuma na daki kafaɗanta ina fadin" To ya ya a ke ciki? Kin san an ce ƙaramar uwa abokiyar shawara."
Kanta na ƙasa ta ce" Ya na da ban dariya Umma."
"To ina ruwan kawu. Balle ke da ya ke so ai za ki sha hira da barkwanci."
Sai ta rufe fuska ni kuma na leƙa ina faɗin" To wai ya ya ne! A tsaida shi ko a sallame shi?
Sai ta ki mgana sai ma tashi da ta yi za ta gudu na ko ce to shikenan tun da ba ta son shi zan faÉ—a masa.
"Umma ni fa ban ce ba na so ba."
"To kina so kenan?
Sai ta gyÉ—a min kai kafin ta zura da gudu zuwa É—akin su Jidda, har suna cin karo ma da Jiddan da ta fito ta na ce min" Umma me ya samu Ya Marwa?
Ina dariya na ce" To Jidda ni me zan ce? Ki tambaye ta."
Na faÉ—a ina dariya ita Jidda irin yaran nan ne marasa damuwa kawai sai ta wuce kitchen ta bar ni nan ina ta annuri.
Washegari Marwa ta koma gida na faɗa mata zan tura ma Kawu lambar wayar Ya Aina zai riƙa samun ta ta can kafin ta tafi ta ke gaya min suna gama pratical suka koma makaranta semester ɗaya za su yi sai jarabawa ashe Diploma ce Kawu zai ji daɗin jin wannan labarin domin ya ce min ba ya so a ɗau lokaci sannan kuma ya ce shi bai faɗa ma kowa ba sai Innayi sai mu da muka sani ya na so ko maaganar za ta fita sai manya sun shiga ciiki shi ya sa na yi gum da bakina.
Na je har gida na duba Gimbiya gaskiya ta na shan laulayi, duk ta rame sai ido ta ƙara fari kamar ba ta da jini Sulaihat ɗin Anty Bahijja kan je ta yinin mata suma kuma suna zuwa sannan kuma ga Yallaɓai. Sai dai ya yi kusan kwana goma a gidan Gimbiya sannan ya dawo nan lokacin ta ji sauƙi sosai ta na cin abinci kuma ta ɗan ayyukanta sai ɗan abin da ba a rasa ba.
 A washegarin ranar da ya dawo gidana karfe huɗu na asuba wayar Gimbiya ta tashe mu ta na kuka wiwi da cewa cikinta a firgice Yallaɓai ya dau mota ya tafi can gida ni kuma ya bar ni a gida amma duk na damu ni na ma kira shi wajen shiddan safe na ji yadda ake ciki sai ya ce min ciwon mara ne ya turƙeta an ba ta gado kuma likita ya ce za a ba ta bed rest saboda cikin jikinta ya samu rauni zai iya zubewa a kowani lokaci yadda na ga hankalin Yallaɓai ya tashi ne ya sa na ɗan kwantar masa da hankali. Nima yara na tafiya makaranta na taho asibitin duk da dai ita Gimbiyar ba za ta ci komai ba yanzu amma na je da kayan tea da ruwan zafi ko da na je na iske Anty Bahijja da Maman farko a asibitin.
*Janafty*
*TKG015*