← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 89

Sashe 19

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sadiya ta."
 
Ya kira sunana cikin raunin murya sai na É—aga ido na kalle shi kwarmin idanuwana suna mai cika kwallah.
"Sadiya wallahi ban ɓoye miki wannan auran da wata manufa ba, sai domin na kasa.  Na Kasa jarumtar sanar da ke na ƙara aure. Ban san da wata kalma zan yi amfani da shi ba,ban kuma san ta yadda za ki karɓi mganar ba. Ba na so na faɗa miki wani abu da zai ɓata farincikin ki na wannan ranar. Ban san dalili ba sai na ji ina jin kunyarki. Ina jin kamar ban kyauta miki ba, har ma a cikin kwanakin nan Sadiya sai na riƙa ji a ƙasan zuciyata kamar na ci Amanarki ne, don Allah ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki ya fe min don Allah SADIYA TA."

Ya ƙarishe faɗa ya na mai ɗora fuskarsa a saman tafukan hannayena ba kuka ya ke yi ba amma ina jin hucin numfashinsa lokaci ɗaya da bugawar zuciyarsa. Yau fa ban san me ya faru dani ba, kamar ruwa ruwa da an fara mgana sai na ji kamar na fi kowa rauni a duniya sai na fara kuka yanzu ma ɗin ma hawaye na ke yi, ina danne abin da ke taso min a cikin zuciya ta. Kai na ƙara yarda da cewa kishi cuta ne kishi masifa ne da bala'i domin a lokacin ji na ke yi ko na ce gani na ke yi yadda ya kwanta a jikina yana lallashina wata rana fa zai kwanta a jikin Gimbiya itama ya na lallashinta ko? Kawai sai na ji zuciyata na rufewa da kanta, ƙuncin da ya fara barina na ƙara ziyarta ta.

Bai san ina kuka ba sai da ya ji ɗigan hawayena a saman hannunshi na dama da ya sauke shi a saman cinyata. Da sauri ya ɗago ya na kallona ai sai ya ga ina hawaye wasu na koran wasu da rawan jiki ya miƙe zaune ya samu hannun kujeran ya zauna ya mai sanya yatsun hannunsa  ya na share min hawaye amma kamar sun sani ya na share min wasu suna ƙara ɓulɓulowa.

"In kina kuka Sadiya ta. Ni me kike so na yi?

Haka ya faɗa ya na share min hawaye, kawai sai na fashe da kuka har da buɗe murya saboda ji na yi kamar in ban fittar da kukan ba zan iya mutuwa, tashi ya yi a ruɗe ya cicciɓeni shi ya koma ya zauna ya ɗora ni bisa jikinsa ya rumgume ya na ta share min hawaye, ya na kuma lallashina ni bai ma san ma lallashin na shi ke ƙara sakani kuka ba, ina shessheƙan kuka na ƙwaɓe hannun shi daga saman fuskata ya ƙara kawowa na ƙara kwaɓewa sai ya tsaya ya na leƙen fuskata da na ke boyeta a saman ƙirjinsa.

Sai kawai ya daga hannayensa sama ya na faÉ—in" To na bari tunda ba ki son lallashin."
Saki na ya yi sai gashi na zamiye kamar zan faɗi kasa kuma shi bai riƙe ni ba, gani zan sha ƙasa ya sa na ƙamƙame shi ina kallon shi ya na murmishi ya ce" Na kawo hannu ki ture ni?
Ya faɗa ya na kallona wani abi ya soki zuciyata a raina na ce ai in Gimbiya ce ba zai bari ta kai ƙasa ba. Kawai sai sai na ƙara saka masa kuka lokaci ɗaya na saka duka hannayena ina dukkansa a ƙirji bai hanani ba sai da na yi har na gaji sannan na koma na lafe a saman kirjinsa ina maida numfashi hannayena suna zagaye a wuyansa.
Sai da ya ga na yi laushi sannan ya saka hannuwansa ya tare ni sosai a saman jikinsa bai sake yi min mgana ba amma hannunsa guda ɗaya da ke bayana da shi ya ke ɗan bubbugamin bayan alamun lallashi, ina ta jan majina da jan numfashi cikin lokaci kuma sai kukan nawa ya ɗauke na koma ina ajiyar zuciya, har kuma na koma na yi lamo idanuwana suna lumshe amma ba barci na ke yi ba. Mun zauna a haka sama da awa ɗaya na san hannayensa da kafafunsa sun gama sandarewa da gangan na ƙi sauka a raina na ce gwara duk na gama more jikin ko ta zo sai dai ta samu saurana.
 
Kuma na samu natsuwa sosai fiye da tsammani na. Ba tare da ya nuna ya gaji ba na sake shi ya saka hannu zai riƙe ni na ce" Zan ta shi.'
Sai ya taimaka min na miƙe hijabin jikina duk ya bushe da ruwan hawaye shima miƙewa ya yi ina gani yana juya wuya da hannayena. Sai da na yi dariyan mugunta a raina, ban ce masa komai ba ya ga na fara ta ku zan bar falon sai ya biyo bayana ya na faɗin"

"Sadiya ba mu karya ba fa yau"

Sai a lokacin sai kuma ya na mganar na ji cikina na juyawa sai na juyo muna fuskantar juna kafin na ce" In soya ƙwai mu sha tea."?
Na tambaya cikin sarƙewa muryan. Ya ƙariso gabana ya kuma saka hannunshi ya riƙo hannayena lokaci ɗaya ya na faɗin" Za ki iya?
Ko na kama miki?
Kai kawai na gyaɗa masa alamin zan iya. Amma bai bar ni ba duk in da na bi yana bi na, hijabin jikina ma shi ya cire min tare muka soya ƙwanan ko na ce shi ya ma soya a falon yara muka karya dka da shima bai ja ni da hira ba amma zai kalleni da kulawa in ya ga na yi shuru na kasa kurɓan tea ɗin

"Are you ok?

Da kulawa ya ke tambayata amma ga ni na yi ni da ya yi ma kishiya sai na ga kamar tambayar ta renin wayau ne shi ya sa na bi na haɗe rai, duk da haka bai ƙyaleni ba bayan mun gama shi ya kwashe komai ya kai kitchen ya dawo ya iske ni dafe da kai ya na tambayata na ce kaina ne ya fara ciwo jikinsa na rawa ya je ya kawomin panadol ya ɓallo ya ba ni tare da ruwa na sha ya kuma riƙe ni har bedroom ɗin mu na kwanta na ya rufa ma ƙafafuna blanket.

"Ki kwanta ki É—an huta ina ga kukan da kika yi ne ya sa ka miki ciwon kai."

Ya faɗa lokaci ɗaya ya duƙa ya sumbaci goshina. Ya juya zai fita sai na riƙe masa hannu sai ya juyo ya na faɗin" Me kike so uhm?
Sai na ce"Ba za ka fita ba ne?
"Ko zan fita sai zuwa anjuma."
Sai na gyaÉ—a kai sannan na sakar masa hannu
"Menene ko kina son wani abu ne?
Sai na girgiza masa kai alamun babu, sai ya ƙara dawowa ya duƙa ya sumbaci bakina, har zai tashi na riƙe masa wuyan rigarsa da hannuna guda ɗaya na ɗago kaina nima na sumbaci bakinsa sannan na sake shi sai kuma da sauri na juya masa baya har ina runtse ido kamar na yi abin kunya na san ya na ta kallona sannan na ji sautin mirmishinsa kafin na ji takunsa da fitarsa lokaci ɗaya ya na faɗin.

"Ina son ki Sadiya ta."

"Ina sonka Yallaɓai na."

Na faɗa a hankali tare da jin wasu tasowar wasu hawayen amma na danne. Ni fa sai yanzu da kishiya ta faɗo kaina na fahimci halin da waɗanda kishi ke saka su kashe miji ko su illata kishiya, a da in na ji labari in ta mamaki ina zaginsu a raina har ina ji ma a tunanina kawai saboda namiji sai mace ta haukace har da kisa. Wato daga ranar da na san Yallaɓai ya zama namu ba nawa ba na fara yi musu uzuri da gaske ba sa cikin hayyacinsu. Sheɗan na ƙawata zafin kishi, ka ji kamar ka yi hauka, ka koma kana ganin hotuna kala kala waɗanda in ba ka da imani tsab za su iya saka ka aikata abin da za ka dawo kana nadama. Ka koma kana ganin mutane dishi dishi tsabar kishi, zuciyata ta riƙa suya ta na kai ka in da in ka hasaso za ka ji kamar kowa ma na duniya ya mutu duk a huta. Ni kaina ba domin Allaah da addu'ar da na riƙa yi da dauriya da tuni an ji kanmu ni da Yallaɓai tsabar yadda na ke jin haushinsa sai sheɗan ya sarrafa tunanina na yi masa illa.

"Astagafurillah."

Na furta a fili saboda tunanin da ya giftamin a fili na furta" Ya Allah ka sassautamin wannan zafin kishi. Sannan ka  tsare ni da aikata abin da zai jawo min nadama a rayuwata."
Na duba wayata ban gani ba sai na tuna na baro ta can falo sai na koma na kwanta na runtse ido ina karanto suratul Jumma'a tirya tiryan ina cikin yin karatun barci mai cike da natsuwa ya kwashe ni ban farka ba sai sha biyu da wani abu na rana.

****

Ko da na tashi Yallaɓai ya gama komai na aikin gida. Girki ne kawai bai yi ba shima domin zai je office ne ya ce akwai aikin da zai yi, ya fita ya barni a falo yau har haraba na raka shi, ni kaina na yi mamakin ji na sakayau kamar ba ni ba. 
Bayan fitansa ba daɗewa aka kawo naman rago kilo biyu duk da ma muna da sauran naman salla a cikin kakide, sannan ga dambun nama bai ƙare ba Musbahu ne ya kawo min tare da kayan miya da kayan lambu. Daga Yallaɓai ne, kawai sai na samu kaina da tambayan shi ina Yallaɓan ya ke.?

"Ya na can office akwai mutanen da ya ke ganawa da su."

Har ya bar gidan ina zaune ina tunanin dalilina na tambaya. Me na ke tsoro? Kar ya je wajen Gimbiya? Wata zuciyar ta ce kar ki manta ya aure ta wata rana tare za su kwana a ɗaki ɗaya. Sai na ji hankalina ya tashi amma sai na fara kiran sunan Allah har na samu natsuwa. A raina na saka jarumta sannan zan ɗauki shawaran Nene zan riƙe Allah domim shi kaɗai ne za ba ni ƙwarin gwiwan fuskantar wannan yaƙin da ke gabana.
Chapter 19 · 0% Book details