← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 89

Sashe 74

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka ji ko Alhaji.? Ma'u sheÉ—aniya ce. Ta haÉ—a husuma ta na neman wargaza zaman lafiya a gidan auran Sadiya."

Ya Hamza ya faɗa cikin ɓacin rai ganin haka ya sa na kalli Alhajinmu shi da Gwaggo da suka yi shuru sun kasa mgana na ce" To ita da ta ce ma Anty Bahijja a yi hankali da ni. Ina shige shigen malamai zan iya yin komai domin na ga bayan cikin Amaryan Yallaɓai."
Gwaggo ta saka salati tana tafa hannu.
"Kai Ma'u ta yi asara. Ta kuma ba ni mamaki. Wallahi tun da na ji abin da ya faru na kasa suƙuni kawai mamaki na ke yi me kika yi ma Asma'u da zafi haka da ta nemi tozarki haka Sadiya?

"Me kuwa na yi mata Gwaggo? Na faÉ—a muku tun a baya kan fasa auranta da Ya Hamza ne daman ta ce na jira zan gani. Kuma ta daÉ—e ta na yi min shige da fice yanzu dai burinta ya cika akaina ta yi min sharri ta kuma yi sa'a na tozarta."

"Za ta ko ci ubanta. Har Baaba sai an kira ta zo domin a kawo ƙarshen makircinta."

Ya Hamza ya faɗa cikin jin haushi Gwaggo ta ce haka ya kamata a matseta sai ta faɗi dalilinta na aikata abin da ta aikata. Alhajinmu na zaune amma ƙala bai ce ba sai kaɗa kai kawai ya ke yi lamarin ya gama ba shi mamaki. Muna cikin magana da Ya Hamza Alhajinmu ya kira sunana na amsa ina mai kallon shi.

"Ki faÉ—a min tun farko yadda lamarin ya faru."

Na gyara zama na sake faɗa musu duk abin da ya faru har zuwa gidan Ma'u da na yi na ja ta da faɗa sai da na faɗa saboda ban ga abin ɓoyewa ba ni ai ban ma samu yadda na ke so ba, da na samu da tuni ta na gadon asibiti.
" Daman ba tun yanzu ba. Na daɗe ina jin wasu labaraina a bakin Yayar mijina Alhajinmu. Ban taɓa ɗaga maganar ba saboda ko na ɗaga sai a ce ni ce ke da fitina tun da Alhaji ka ce in ban yi zumunci da Ma'u ba za ka yi fushi da ni ya sa na kauda komai ina zumunci da ita to ashe ita babban burinta na tozarta. Ta tozarta zuru'an Mama ni kuma ta yi min ƙazafin ina ƙokarin zubar da cikin Amaryan Yallaɓai. Alhaji ka yi haƙuri amma ina jin lokacin da zan datse zumuncin da ke tsakanina da Ma'u ya yi. Kuma na tabbata kaima ba za ka ce don me ba, domin matuƙar cin zarafi Ma'u ta gama yi min shi anan duniya."

Gwaggo ta nisa amma  ba ta yi magana ba. Ya Hamza ko ya ce gaskiya ne babu amfanin yin zumunci da wanda ke neman ya tozarta ka.
Ya kalli Alhajinmu ya na sake faÉ—in" Alhajinmu mataki za ka É—auka domin bayan Sadiya har kai yar iskar yarinyar nan ta ci ma mutumci."
Alhajinmu kai kawai ya girgiza ba taree da ya yi magana ba.

"Ga ma labarin Marwa. Ƙanin Nene ya ganta gidana ya ce ya na so. Wallahi Babansu Jidda ya raka shi wajen Babansu Marwa ya neme ni izini ya na zuwa wajenta domin su dai-dai ta daman ya ce sai sun gama yarda da juna zai kai mganar ga manya. Amma Ya Murja na samun labari ta je ta faɗa ma Ma'u ita kuma munafuka ta kwashe ta faɗa ma Anty Bahijja. A ranar da abin ya faru har ta na ce min ban isa ba yadda na asirci Yallaɓai ne na ke so na tusa ma Kawun su ɗiyar Yayata shima a asirce shi sai yadda aka yi da shi tun da mu yan na gada ne ba haya ba."

Gwaggo ta ƙara saka salati ta na faɗin" Na ga duniya ni Maimuna. Me Ma'u ta ke so ta zama ne! Ko na ce ta zama ma?
Ya Hamza ya yi wani kayci kafin ya ce" Ni fa daman tuni na san za a rina. Tun a baya ta fi kowa kalkalin mgana da tsara zence. Ta ko gama ma kanta aiki sai ta gane ba ta da wayau"

Alhajinmu ya jinjina kai kafin ya ce" Tabbas Ma'u ta yi kuskure. Kuma ya zama wajibi a nuna mata kuskurenta."
"Tabbas."
Gwaggo ta faɗa daga gani itama ranta duk ya gama ɓaci.
"Hamza kira min Hasiya mu yi mgana."
Alhajinmu ya faÉ—a ya na kallon Ya Hamza nan ta ke ko ya doka ma Baaba kira. A handfree Ya Hamza ya saka wayar bayan sun gaisa sai Alhajinmu ya ce ta zo gobe in da sarari ya na son ganinta kawai sai itama ta ce.

"Daman ko ba ka kirani ba Ya Sule ni zan kira ka. Kana da labarin Sadiya ta je har gida ta daki Ma'u? Me ta yi mata? Ko na ce me Ma'u ta tsareta mata da ta tsane har haka?

Ni da Ya Hamza muka kalli juna cikin mamaki. Ni fa ban yi wani mamaki ba domin yadda na san yunwar cikina a haka na san wacece Ma'u kuma ina da tabbacin ta san Ƙwanta ne ya fashe ya yi wari shi ne ta kira Baaba ta shirya mata mgana yadda in aka taso da maganar za ta samu mai tsaya mata.

"Na samu labari. Kuma akan haka ne na ce ki zo."

"To ai dai ya fi. Gwara ga Sadiya ga Ma'u sai na ji abin da ta yi mata da ta bi ta har gida ta dake ta"

Ta na ta faɗa fa, ta na nuna daman ai tun zuwan Ma'u gidanmu ba ƙiyayyar da ban nuna mata ba, yanzu ma ta yi auren ban ƙyaleta ba to itama ta daina yin shuru wannan karon sai ta ji dalili.

"Baaba ma ta na ƙara ɗaure ma yarinyar nan kugun yin wasu abubuwan"

Ya Hamza ya faÉ—a cikin mamakin mganganun Baaba a waya.

"Daman ai Hasiya ba ta son laifin Ma'u. Shi ya sa ta ke goyon bayan duk abin da ta faÉ—a mata."

Ni dai mirmishi kawai na yi, to ko na yi mgana ban san me zan ce ba. In faɗa musu saboda Ma'u Baaba ta tsane ni ko na ce daman tun can ba ta so uwata ba shi ya sa nima ba ta sona. Ko na faɗi haka za a iya ƙaryatawa amma a cikin raina na kudiri niyyar gobe in aka zo zama wallahi ba zan raga mata ba, tunda ni ba ni da uwar da za ta kare laifina ai ina da bakin da ni zan iya ƙwatan kaina.

"Bakomai. Allah ya kaimu goben zan kira Asma'u ta zo da megidanta kema goben ki taho tare da Yusufan kin ji?

Alhajinmu ya faɗa ya na kallona sai na amsa da in sha Allahu. Ban daɗe ba bayan azahar na koma gida saboda na bar gidan ba shara. Bayan na tuɓe na share gidan na yi mopping na saka turaren wuta gidan ya ɗau kamshi.
Mganin da Inna Mariya ta kawo min ko a raina ban ji ba na so na yi amfani da shi ba. Daman na asibitin sauran kaɗan na adana shi da cewa na asibitin na ƙarewa zan fara amfani da shi in gani ko za a dace. Duk da ko na asibitin ma ya yi min sosai. Ya dai-daita min lokacin al'adata  kwanakin nan yanzu lafiya lau na ke yi na gama sannan ba wannan azababben ciwon maran sai ɗan abin da ba rasa ba.

Sai shidda su Jidda suka dawo daga hadda. Allah ya sa na gama abinci da wuri jalop É—in kuskus na yi musu mai kayan lambu da hanta abinci ni kaina na san ya yi daÉ—i. Haka Jidda da Baby suka rika santi suna faÉ—in" Umma girkin ki ya yi daÉ—i sosai."
Ina dariya na ce ko na saka musu waigi ne suna santi ne. Daman sun dawo a jigace tea kawai da buredi suka tafi dashi makaranta to daman ina tea zai riƙe su tun safe har yamma dole su ji kunya. Maimakon su dafa ko indomie ne, ko da ya ke na rasa me ya sa ba su son tafiya da indomie makaranta, barin ma Jidda sai ta ce wai indomie na yara ne, in dai ba ni ce na tashi na dafa musu taliya ko shinkafa suka tafi da shi ba ta gwammace su ɗura tea a goran su da buredi su tafi dashi akan su dafa indomie.

Yallaɓai sai wajen tara na dare ya dawo ya zo da yara da rake mai yawa ya ce Nene ce ta ba shi ya kawo mana ni da yara. Na karɓa na ce mun gode daman ko bai faɗa ba na san zai biya ta can tun da matarsa na ca. Jidda ce ma ta tambaye shi ina Anty Gimbiya? Ya ce ta na  gidan Nene ta na gaishe su amma ni ko sunanta na ji an ambata sai raina ya ɓaci kuma a saman fuskata ma rashin jin daɗin ya na bayyana. Tun a daran na faɗa masa Alhajinmu na neman mu ni da shi a gida gobe, bai tamnbayi dalili ba ya ce Allah ya kaimu.

Shi ya sa tun safe na tashi na dafa ma su Jidda Macaroni da Miya suka tafi da shi makaranta. Indomie kuma suka ci kafin su tafi, sai da na yi wanke wanke na gyara kitchen sannan na yi wanka shara daman na ce na gaji gaskiya sai gobe ina dalili har bayana na ciwo. Saude duk ta sangartani, mu kan mu da indomie da ƙwai muka karya sannan muka fita, muna hanya Ya Aina ta kira wayara wajen goma na safe tace kowa ya zo ni kaɗai ake jira na ce gamu nan a kan hanya.
Chapter 74 · 0% Book details