Sashe 22
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hauwa ta zaro ido ta na kallona kafin ta ce" Daman kin sani?
Haushinta ya kamani da sauri na ce" E da ba ku gaya min ba na sani a can duniya ba."
Hauwa za ta kwaso rantsuwa na ɗaga mata hannu raina a ɓace ina faɗin" Daman ina jiran ki Hauwa daga ke har Munnira na yi ta tsumayin ku. Ai na ɗauka ni da ku ɗaya ne in kuka ji wani abu a kaina za ku yi saurin zuwa ku sanar da ni amma sai ga shi an yi min kishiya kowa ya rufeni ciki har da ku Hauwa. Kun bani mamaki kuma wallahi na riƙe ku a cikin raina Ubangiji ya gani na ji haushin ku ƙwarai kun kuma nuna min irin na ku zaman tare kenan."
Na ƙarishe faɗa ina jin takaicin abin na taso min daga ƙasan zuciyata.
Hauwa ta fara rawan bakin rantsuwan itama ba ta sani ba Muttaƙa bai faɗa mata ba daga can Rano ne ƙanwarta ta kira ta faɗa mata. Da ta kira Munnira ta faɗa mata sai ta ce itama ta ji Jamila ta kira ta faɗa mata amma an ce a yi shuru Tafidan bai sanar da ke ba tukunna."
Hararan Hauwa kawai na ke yi ta na mgana ganin haka yasa ta ƙara kwaso rantsuwa ta na faɗin" Wallahi ki yarda da mu. Ta ya ya za mu fara sanar da ke wannan labarin mara daɗin ji? Munnira ta ce kar mu faɗa miki mu jira shi da ya kwanto kuran ya ɗaure ta da kansa."
Ta ga dai in zaune ina karkaÉ—a kafa ban ce komai ba sai Hauwa ta yi mirmishi kafin ta ce" To ki yi hakuri tun da kin ji zafin mu."
Kai tsaye na ce"Wallahi na ji zafin ku. Kuma waÉ—anan mganganun ba su saka na daina jin haushin ku ba. Haba a taren mu ya wuce wasa. To ai shi bai faÉ—a min ba a duniya na ji "
Hauwa ta yi ta bani hakuri na ce ni fa ba zan haƙura ba sun ba ni haushi kuma na riƙe su a cikin raina na kuma ce mata wallahi in ita ce ko Munnira haka ya faru da su ba zan iya yin shuru ba saboda a tunani haɗuwar mu ta bangaren gidan aure ɗaya a shekarum da muka yi tare mun ƙulla kyakyawan alaqa a tsakaninmu da duk iskar ko guguwar da ta tunƙaro wani daga cikin mu sai in da karfin mu ya ƙare, ba su koma gefe su bari duniya na yi min dariya ba."
"Mun ji mun yi laifi. Don Allah ki yi hakuri."
"Ba fa zan haƙura ba. Ko na haƙura to ba zan ɓoye muku ba, na riƙe ku a cikin raina."
Na faɗa kai tsaye ina kallon Hauwa da ta yi kalan Tausayi. Ni kuma na ƙara jadaddamata da cewa na riƙe su a raina ita da Munnira na hakura amma ba zan manta da abin da suka yi min ba, ta na jin haka ta ce to ba za ta iya da ni ita kaɗai ba nan ta ke ta ɗau waya ta kira Munnira ta ce ta zo gidana yanzu a she su suna can suna ɓoye min mganar kar na ji hankalina ya tashi ni kuma ina nan gida na ƙullace su. A cikin wayar ma Munnira ta ji ina mita ina faɗin kwarai Ubangiji ma ya sani na ƙullace ku a cikin raina.
A she duk sun san abin da suka yi mini ba su kyauta ba muna cin abinci da Hauwa sai ga Munnira. Ni da kaina na je na buɗe mata gida ta na shigowa ta fara faɗin" Haba uwargidan Yallaɓai afuwan."
Hararanta na yi kawai na wuce na barta ta biyo bayana itama da na ta mganganun, ni abincin ma duk ya fita kaina ita kanta Hauwa kaÉ—an ta ci Munnira daman da na yi mata ta yi sai cewa ta yi sai da ta ci abinci ta fito daga gida.
"Haba Sadiya wa zai iya tunkaranki da mganar kishiya? Suna mafi muni a wajen mu mata. Tabbas na riga Hauwa jin mganar nan auran domin a daran Jamila ta kirani ta faɗa min ta kuma ce an ce a yi shuru saboda ba ki sani ba. Na shiga ruɗu da tashin hankali Sadiya lokacin da Hauwa ta kirani da niyyar wai mu shirya mu zo mu faɗa miki na ce a'a kar mu yi haka, ke ba za ki manta da mu a matsayin waɗanda suka sanar da ke labari mafi muni ba, sannan Tafida zai ta ganin baƙin mu. Mazajenmu kuma za su ji haushin mu domin mun shiga hurumin da namu ba. Sadiya ki kalli dalilinmu ta fuskar fahimta ki yi mana uzuri, in kin ƙullace mu wannan ba laifi ba ne hali ne na ɗan adam saboda kina ganin har da mu aka munafunceki, amma kin ji dalilinmu ki yi duba da tsaka mai wuyar da muke ciki ki yi haƙuri zuciyarki ta yi sanyi a kan mu don Allah."
Kallon Munnira kawai na ke yi har ta dire mganarta ban ce komai ba. Ganin haka ya sa ta gyara zama a saman kujera mai zaman mtum ɗayan da ta ke fuskata ta, ta cigaba da faɗin" Ni fa sai dai ki yi ta ƙullatana Sadiya amma Allah ɗaya ne wallahi tallahi ba zan iya fara iya taran ki da labarin Yallaɓai ya ƙara aure ba. Hauwa ma ni na ƙwabeta. Gwara shi da kansa ya sanar da ke zai fi sauƙi."
Kai na gyaÉ—a kafin na ce" Uhm to ai da ba ku sanar da ni ba shima bai faÉ—a min ba a daran aka kirani aka sanar da ni."
"Waye don Allah.?
Har Munnira da Hauwa suna haÉ—a baki wajen tambayata ko wace ce kai tsaye na ce musu Ma'u ce, ita Munnira ba za ta gane wace ce Ma'u a wajena ba Hauwa ta fi sanin ta ita ce ma ta yi mata bayanin matsayin Ma'un a wajena da ta in da suka haÉ—u da Anty Bahijja suke aminta.
Munnira ta lailaya wata aashar kafin ta ce" Kai mutane ba su da kyau. Ita yanzu sai ta zaɓi bare a kan ki Sadiya? Ta na yar'uwanki ta kira ki ta na sanar da ke wannan baƙin labarin?
Ina murmishin takaici na ce" E mana. Ita ai daÉ—i ta ke ji,da kuma gayya ta kirani ta sanar da ni hakan"
"Amma wallahi ba ta kyauta ba."
In ji Hauwa.
"Kai gaskiya ta yi asara."
In ji Munnira. Sai kawai na kalle su amma na kasa mgana saboda wannan tuƙiƙin dake zuciyata yanzu ke taso min da aka ta da mganar.
"To wai shi Yallaɓai har yanzu bai sanar da ke ba?
Munnira ta tamnayeni ta na kallona, jikina a sanyaye na ce" Bai sanar da ni da bakin sa ba sai bayan Nene ta zo gidan nan jiya ta sanar da ni da kanta."
GabaÉ—ayansu suka waro min ido suna haÉ—a bakin faÉ—in" Ita Nenen?
Sai suka ba ni dariya har sai da na dara kafin na gyara zama ina ba su labarin abin da ya faru tun ranar da aka ɗaura auran na dai ɓoye musu abubuwan da suka shafi siirun auran mu, amma na sanar da su duka mganganun Nene a kaina da shi kuma abin da Yallaɓan ya ce min a jiya na ƙarishe da cewa" Ni dai har yanzu bai ce min komai a kan Gimbiyar ba."
"Tiƙashi.!"
Munnira ta faɗa ta na sauƙowa ta yi zaman dirshan saman cafet.
Ita daman Hauwa daman tuntuni a saman cafet É—in ta ke zaune.
"Wai daman ashe haka kishi ya ke? Kishi na da zafi da ƙuna. Wallahi ban taɓa sanin raɗaɗin kishi ya kai ƙunar haka ba sai yanzu da ya faru a kaina."
Na faÉ—a ina jin numfashina na sarkewa. Hauwa da Munnira suka kalleni cikin tausayawa amma sun kasa mgana.
"Ku yi ta fatan Allah ya bar ku da mazajenku har abada. In kuma kaddara ta saka sun ƙara ku fara addu'an salama da sanyin zuciya tun yanzu domin ban sam da abin da zan yi iya kwantanta muku zafin da ke cikin a yi maka kishiya ba. Ballatana kishiya irin tawa wacce ta zo min a cikin bazata. Wallahi ban taɓa tsammamin Yallaɓai zai ƙara aure a wannan gabar ba. Ban kawo hakan a raina ba kwata kwata ba."
In na so na daure amma na kasa sai kuka, na dukar da kaina a cikin cinyoyina ina ta kuka Munnira ta taso zuwa kusa da ni ta zauna ta na lallashina.
"Ki yi haƙuri Sadiya. Ki daure."
"Ki daina kuka don Allah Anty Sadiya. ji na ke yi kamar na ta ya ki kukan wallahi"
Hauwa ta faÉ—a a muryanta itama kamar ta yi kukan
Lallashin su ma ƙara sakani kuka ya ke ganin na ƙi yin shuru ya sa Munnira ta ce Hauwa ta tashi su tafi tun da kuka suke sakani jin haka ya sa na haɗiye kukan da ke taso min.
"Gaskiya Nene ba ta kyauta ba. In hae abin da ta faɗa gaskiya ne ba ta ɗauke ki a ƴa ba. In ke yarta ce sai ta saka a yi miki kishiya! Na fi ganin laifinta sama da laifin Yallaɓai, domin ita uwa ce umarninta sama ya ke da umarnin kowa."