Sashe 7
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai na ga ta kalleni bayan ta ga na yi mgana da sauri na ce" Na idar ne."
Sai ta wuce zuwa kitchen ta duba ta dawo ta ce saura guda ɗaya ina daga zaunen na ce ta kira shi ta faɗa masa har da siga ma ya siyo mana ta mu wacce ta rage ta yi ƙasa da ya ke ta san password din wayar ta buɗe ta kira shi ta faɗa masa ya ce to zai taho da shi haka Jidda ta faɗa min bayan sun gama wayar sai na gyaɗa mata kaina. Ina nan zaune Baby ta kunna cartoon jifa jifa ina kalla sannan wani bangaren kuma ina can ina tunani.
Sai da Jidda ta gama aikin makaranta sannan ta kwashe jakarta ta maida É—aki bayan ta dawo falon na ce ta sako musu abinci akwai kaza a fridge ta É—auko ta ta É—umama su ci ta amsa da to bayan ta É—umama kazan ta É—ibo abincin taliya ce jalop mai kifi tun wanda Marwa ta yi ne suka yi min ta yi na ce ba yanzu zan ci ba. GabaÉ—aya na rasa É—anÉ—anon bakina tun yinin yau daga ruwan tea na safe sai ruwa kawai na ke sha na kasa cin komai.
Jna ji Jidda na ce min" Umma shima Abba taliya zai ci?
Sai na kalleta yarinyar nan da iyayin tsiya wato har ta san babanta ba ya son cin taliya. A raina ko na ce ita zai ci in ya ga dama in kuma ya tsaya gidan amaryansa ya ƙoshi shike nan a fili kuma ban ta amsar ta ba shurun da na yi kawai ai ya faɗa mata E ne ita zai ci domin ni ba zan ƙara yin masa wani girki ba bala'in haushin shi na ke ji wallahi na rasa yadda zan yi da raina.
Saboda ma kar ya dawo ina falon ya tare ni da mgana na ce musu zan je na kwanta Jidda ta kalleni kamar za ta yi mgana sai kuma ta fasa ina lura da ita sarai na san a ranta za ta ga abin da ba ta saba gani ba ne. Yallaɓai ko ƙarfe nawa zai kai bai dawo ba sai na jira ya dawo zan kwanta amma yau ɗin nan sai na ga in ma na tsaya jiransa ni ce sakara saboda ai wajen Amaryansa zai biya sai ya gama zamansa sannan ya dawo sai ni kuma da ban san ciwon kaina ba sai na zauna ina jiransa ai ko ya yi kaɗan.
Shigewata ɗaki na yi, na yi shirin barci na koma na kwanta ina juye juye marata ce ta ɗan fara min ciwo ya sa ma na tashi na je kitchen na zuba ruwan lipto na sha saboda marata ta ɗaure ban tsammaci zuwan al'ada ba saboda ni family planing ya gama lalatamin al'ada ba na iya gane zuwansa sai dai kawai duk lokacin da ya ga dama ya ke zuwa wannan ciwon maran daman ina fama dashi lokaci bayan lokaci. Ɗaki na koma na kwanta kuma cikin ikon Allah sai ya lafamin, barci ne a idanuwana saboda akwai bashin sa a kaina a cikin raina na riƙa addu'ar Allah ya sa barci mai nauyi ya sace ni Allah ko ya amsa addu'ata barcin da na yi mai nauyi ne domin har dawowar Yallaɓai ban sani ba sai dai muka haɗu da asuba shi ne ya ke ce min ya dawo ya ga ina ta barci ya na fatan lafiya? A yatsine na ce masa marata ce ta ke ciwo a jiyan sai na sha mgani na kwanta.
"Ayya Sorry.."
Kaina na gyaɗa masa lokacin ya ɗauro alwala ne ya na saka riga ni kuma tashina kenan na fita zuwa Tiolet na duba Al'ada bai zo miin ba sai kawai na kama ruwa na ɗauro alwala sanda na fito baya nan ya fita masallaci sai da na yi raka'atul fajir sannan na gabatar da sallar asuba. Ko da na fita zuwa ɗakin su Jidda har sun tashi ina jin Yallaɓai ne kafin ya fita masallaci ya tashe su barci ne a idona suna cewa karatu na ce Jidda ta yi ma Baby su karanta azkar zan je na kwanta kuma ina komawa ɗaki na kwanta ga casbaha a hannuna sai barci kuma ya sake ɗaukana ban farka ba sai wajen tara saura na safe har su Jidda sun tafi makaranta Yallaɓai kuma na can falo yana aiki a kan system ɗin sa.
Ina ganin haka sai kawai na fara yin wanka na shirya cikin riga da wando. Sai na leka kitchen ɗin na ga sun soya dankali da buredi da ƙwai, saboda kar in koma can falo mu haɗu da Yallabai ya sa na sake dafa wani ruwan tea lipto ne kawai da gnyen shayi ko siga ban saka ba na ɗibi dankalin anan kuma kitchen ɗin na zauna na ci kaɗan ba da yawa ba, ina tunanin ko Yallaɓai ya karya ko bai karya ba? Amma kuma na kasa zuwa falon na ga ni ko hakan ta faru ina wanke hannuna na koma tiolet na kuskure bakina sai na sake komawa bedroom ɗin mu na shige bargo ina jin sanyi sanyi na shigana kamar zazzaɓi zai kamani.
Ina nan kwance sai ga Yallaɓai ya shigo ya riga ya kamani idanuwana biyu ba zan iya masa alaye da na saba masa kwana biyun nan ba.
"Ina kwana."
Na faÉ—a daga kwancen da na ke, sai da ya sauke kayan a hannunsa a saman dirowan gado sannan ya tako har gabana ya duka ya sumabci goshina lokaci É—aya yana faÉ—in" Yaushe muka fara irin wannan gaisuwar Sadiya ta?
Kallonsa na yi ba tare da na yi mgana ba sai na ga kawai ya ware min hannuwana alamun na taso wallahi wani turriri na ke ji a ƙasan raina ina tunanin yanzu fa yadda ya ke yi min nan tuni ya fara yi ma Gimbiya ko? Idanuwana suka ƙanƙance da kishi ina shirin na ce ni ya ƙyaleni ina jin barci ban samu dama ba ko ya fahimci niyyata ne ya sa kawai ya sunkuyo ya ɗago ni zaune yana faɗin"Oya ta so nan."
Ba yadda na iya haka nan na miƙe a kasalance na faɗa jikinsa ya ƙamƙame na wani lokaci ya na sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Kwana biyu nan duk an daina min kirki Sadiya ta. Ko na yi miki laifin ne?
A raina na ce babban laifi ma kuwa sai dai ban ce ba sai da na fara ture sa sannan ya sake ni ya na kallona hancina ya lakace kafin ya ce" Kwana biyu ba mu yi ɓarnan ruwa ba ko?
Kafin na yi wani yunƙuro ya haɗo haɓata ya haɗe bakim mu waje ɗaya ban taɓa sanin akwai ranar da za ta zo Yallaɓai na taɓa ni ina jin ƙuna a cikin raina ba domin sheɗan ne ke haskomin su tare da Gimbiya ya na yi mata kwatankwacin irin abin da ya ke yi min tuni na ji wani ƙarfi ya shige ni da hannu na saka iya karfina na ture Yallaɓai baya ina mai ƙwace kaina daga gare shi.
Cikin mamakin da na gani a saman fuskarsa ya kalleni.
"Me kika yi hakan?
Ya faɗa a ɗan zafafe amma cikin sanyin murya kai tsaye ina goge bakina kamar ya saka min cuta na ce" Ka ga Yallaɓai please."
"Please mene?
Ya katseni da sauri ya na kallona kirjinsa na ɗagawa sama da ƙasa alamun ranshi ya fara ɓaci.
Ina yarfa hannu na ce" Ka ƙyaleni kwana biyu nan am not in the mood."
Ina gama faɗin haka na koma kan gado na kwanta ina jan bargo kenan na ji ya fizge da karfi ya cilla dashi a kasa da gajiya a cikin idanuwana na kalle shi kafin na ce" Na ce ka yi hakuri ka ƙyale ni ko?
Ban jin daÉ—i ne."
"Ƙarya kike yi Sadiya."
Ya faÉ—a ya na kallona sai na ware ido cikin mamaki ina kallonsa sai kawai ya yi wani mirmishi kafin ya ce" Kin É—auka ban lura dake kwana biyu nan ba. Sam ba ki son ina taba ki in kuma na kusanto in da kike a fuskarki kike nuna ba ki son hakan sai na É—aga miki kafa ina tunanin fushin da kike yi a kaina ne ba ki sauka ba! Amma Sadiya ji fa abin da kika yi yau ni ne na zo gare ki kika ture ni? Ture ni fa kika yi to me kike nufi?
Ya ƙarishe faɗa a fusace kaina kawai na dafe saboda ni ba na son damuwa.
"Na yi miki laifi ranar Anniversary ɗin mu na yi dare ban dawo ba. Yes na ji kuma na karɓi laifina sau nawa zan ce ki yi hakuri Sadiya?
Ni kawai tsayawa na yi ina kallon ikon Allah don kawai ya ga ban buÉ—e baki na yi mgana ba shi ne zai wani tsaya a kaina ya na min masifa.
 "Ki ba ni amsata ina miki mgana me hakan da kika yi ya ke nufi?
Ya faɗa a fusace har ya na daka min tsawa na kai makura na ga ba zan iya ɗauka ba a fusace na sauko daga kan gado ina ƙokarin barin masa ɗakin da zafi ya riko ni ya yo baya da ni har ya na yaga min hannun rigar jikina saboda da ƙarfi ya jawo ni ta baya.
"Kar ki sake ina mgana da ke kina barina a wajen zan saɓa miki Sadiya."
Na ƙanƙance idanuwana ina kallonsa kafin na ce" Ni me zan ce? Na ce ka yi hakuri wannan faɗan ne kuma ban san dalilin shi ba"
"Amsa tambaya za ki ba ni malama"
Ido cikin ido yake kallona sai na fahimci ranshi ya ɓaci ya na ta sakin huci ni ko domin na ƙara kunsa masa takaici sai na ce" Me ka ke son sani?
"Abin da kika yi yanzu? Me hakan ya ke nufi?
Ya faÉ—a ya na wani taso min sai na ja baya ina faÉ—in" Me kuwa? Ni ba na nufin komai"
"Na yi miki wani laifi ne bayan laifin ranar?