← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 89

Sashe 8

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai saboda ya ga na yi shuru. Lalle nema Yallaɓai nima ko ina kallonsa na ce" Laifi! Sai ka tambayi kanka Yallaɓai."
Na faɗa ina ƙoƙarin wucewa wannan karon da karfi ya jawo hannuna ya tamke har sai da na ji zafi ina kallon shi cikin mamaki kafin na samu zarafin mgana ya ce da ƙarfi" Ina tambayarki kina tambaya na Sadiya?
Ihu Yallaɓai ke yi min a saman kaina saboda ina guje ma ɓacin raina kar nima na haukace masa.

"Me na yi miki kike ba ni wasu attitude da ban gane musu ba ne? Ko akwai wani abu a zuciyan ki ne! Ki fada min na ji.!"
Yadda yaƙarishe tsawan ne har ya na neman ɓallamin hannu ya sa a fusace na make hannunshi nima cikin ihu na ce" Sakar ni. Ban sani ba. " Na faɗa nima cikin hargowa ina mai ɓalla masa harara idanuwana har sun kaɗa sun yi jajir
Wucewa na yi ina faɗin" Na ce ka yi haƙuri ka kyaleni amma ka ƙi so ka ke yi raina ya ɓaci na haukace maka?

"To ki haukace mana. Ina dai dai da ke."

Ya faɗa ya na wani sakin tsaki Yallaɓai na kallah wannan abun na ƙirjina na taso min har wani duhu duhu na ke gani wato wannan shi ne halin maza in sun ƙara aure yau wai ni Yallaɓai ke faɗa ma ya na dai dai da ni. Kallon shi na yi idanuwana sun cika da kwalla sai kawai na nuna kaina cikin sanyin murya ina faɗin" Yau ni ce Yallaɓai ka ke faɗin kana dai dai da ni ko?

Sai na ga jikinsa ya yi sanyi saboda ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" To ya kike so na yi miki Sadiya. To taho ki ji."
Ya faÉ—a ya na tahowa wajena da sauri na É—aga masa hannu sai ya dakata kafin na kalleshi na jinjina kai ina faÉ—in" Ka guji haukacewan tawa domin na rantse da Allah kai ba za ka iya da ni ba sai ka yi gayya "

Ina gama faɗin haka na fice daga ɗakin na bar shi nan. Ina jin kuka na taso min ɗakin su Jidda na shige na faɗa saman gadon Baby sai na ji kawai na fashe da kuka, sanin Yallaɓai zai iya biyo ni ya sa na tashi na rufe ƙofa ilai ya zo ya na ta kiran sunana na yi masa banza sai yau na samu damar yin kuka wato har na fara fuskantar wulakanci daga wajensa saboda ya ƙara aure ina kuka mai sauti amma kuma zafin da ke zuciyata ba ya raguwa sai ma ƙaruwa. Yallaɓai ya yi ta bugun kofa ban bude ba sai can kuma ya dawo ina jin sa ya na faɗin.

"Sadiya ki yi hakuri raina ne ya ɓaci. Na shirya zan je kaduna in na dawo yau in sha Allahu za mu yi mgana"

Ina jinsa ya gama mganganunsa ya fice ya bar gidan Ranar Saude ban san abin da ya hanata zuwa ba ni kuma kwance na yini É—akin su Jidda salla kawai ke ta da ni ban komai ba hatta girki da suka dawo ne na ce Jidda ta dafa musu indomie ni kuma sai na sha ruwan zafi saboda cikina ya tanmke ga marata na matsannancin ciwo.
Su kansu yaran sun san yau ba kanta Jidda ta ce" Umma ba ki da lafiya ne?
Sai na amsa mata sannu ta yi min, yadda na yini kwance haka ma har dare ina kwance can bayan isha'i al'ada ta zo min sai na tashi na sake wanka na gyara jikina ranar ma da wuri na kwanta su Jidda ma na saka su barcin wuri. Wayata ko a yinin ranar ma kashe ta na yi saboda ba na so damu na fi son a bar ni na gama ji da abin da ke damuna wannan duka dukan da Yallaɓai ya yi mini ba.

Ban ɗauka a daran ya dawo ba sai farkawa na yi cikin dare na ganshi kwance kusa da ni. Da safe kuma na dai gaishe shi na addinin da ya ce mace ta gaida mijinta ya amsa a daƙushe shima, muryata ta shaƙe da safe tunda kukan da na yi ta yi jiya ya saka min mura mai zai shi ne ma ya yi min mgana.

"Sannu Mura kike yi?

Ya faÉ—a lokacin da ya dawo daga kai su Jidda makaranta an saka su wata tahfiz can gaba damu kaÉ—an asabar da lahadi. Salisu na gida ba ya jin daÉ—i. Ya ji ni ina ta attishawa ne sai ya yi min sannu na amsa kuma shi da kanshi ya je ya dafo min shayin citta ya kawo min na sha sai na É—an samu sauki sannan ya duba cikin box É—in mu na mganguna ya samo min mganin mura ya ba ni na sha sai ya ce na kwanta na huta har yana gyara min kwanciya ya na rufamin bargo da ya ke kuma mganin kamar ya na saka barci sai barci ya É—auke ni sai wajen sha É—aya na farka na tashi ina mutsike ido wayata na kunna na ga 11 na safe ta gota gashi yau É—in asabar.
A kasalance na sauko daga kan gado ina hamma tiolet na shiga na kama ruwa yunwa na ji ina ji sai na tafi kitchen sai na ga Yallaɓai ya soya doya ya rage min ita na diɓa zuwa falon yara daga nan na ke jin tashin muryoyi kamar ba ta Yallaɓai shi kaɗai ba sai da na gama cin doya na kora da ruwan shayi sannan na kai kofin da filet kitchen ni kaina wajen duk ya yi min kazanta jiya Saude ba ta zo ba ni kuma ban yi ba.

Bedroom na koma na sako hijabi da takalmi na yi sallama a falon Yallaɓai suka amsa min sannan na tura ƙofa na shiga.

"Uncle Abba kai ne tafe ba labari."

Na faÉ—a ina karisowa cikin falo, lokaci É—aya ina É—an tari kaÉ—an.

"E. Na shigo duba wani fili sai na kira Yallaban ki ya ce yana gida na ƙariso. Ina zuwa ke na fara tambaya ya ce ba ki jin daɗi kin kwanta "

Ina zama saman kujera mai zaman mutum É—aya na ce" E wallahi sannu da zuwa."
Na faɗa ina kallon Yallaɓai ta gefen ido ya na zaune a gefen Kawun na shi ya duƙar da kai ƙasa.

"Sannu ya muran to?

Sai na ce da sauƙi ina tambayan ya mutanen gida.  Mu ɗan yi hira saboda ni dai muna shiri da shi kuma har muka gama Yallaɓai bai saka mana baki ba, ban daɗe ba na tashi na koma falon su Jidda.
Daga Yallaɓai har Uncle Abba sun bi bayan Sadiya da kallo har ta fice kafin Yallaɓai ya sauke ajiyar zuciya ya na faɗin" Ka ga abin da na ke faɗa maka ko? Kwata kwata na kasa gane kanta."

"To daman ina za ka gane kanta ka yi mata kishiya."..

Yallaɓai ya ce" Ai ba ta sani ba."

"Ko?

Uncle Abba ya faɗa ya na kallon Yusuf. Shi kuma sai ya gyaɗa kai kafin ya ce" Yes. Domin na roƙe su kar su faɗa mata sai ta faraji daga bakina."

Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce" Ni kuma sai na ke tunanin kamar ta sani Tafida."
Ido Yusuf ya saka masa kafin ya ce" Ta sani?
To wa ya faÉ—a mata?
Abba ya zaƙuda kaffaɗa kafin ya ce"oho amma ka yi tunanin me ka yi mata da ta sauya maka haka? Ni kaina na ga duk ta yi wani iri kamar ba Sadiya ba."

Yusuf ya yi shuru ya na tunanin kai bai yarda ta sani ba in ta sani me ya sa ba ta yi masa mganar ba. Sai dai ya fi yarda ƙila ta na ji dai a jikinta domin an ce mata in za a yi musu abokiyar zama suna ji a jikinsu.

"Ba ta sani ba gaskiya rigimarta ce kawai ta tashi."

Ya faÉ—a cikin jadaddawa.

"To sai ka sanar da ita da wuri kafin ta sani a wani wajen."

Sai ya jinjina kai kafin ya ce" In sha Allahu.
Daga nan suka cigaba da tattaunawa duk a kan ba tun dai.

*Janafty*
*TKG*

03.

FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622

Ni ko ina barin falo ɗaki na koma na ɗau wayata na kunna na kira Saude sai balaraba ta ɗauka tana faɗa mini Saude ba ta da lafiya zazzaɓi ya rufe ta. Amma ta ji sauƙi, fatan samun lafiya na yi mata sai ta ce min ko ina buƙatar ganin ta ne? Ai sai ta rarrafo ta zo tunda ta ji sauƙi.

Da sauri na ce" A'a ta bar shi kawai in ta ƙara jin sauƙi sai ta zo."

Sai muka yi sallama bayan na ce ta haÉ—a ni da Sauden na yi mata sannu sai ta ce mini ta shiga makewayi mun rabu akan zan sake kiranta in sha Allahu.
Ajiyar zuciya na sauke ina mai riƙe ƙuguna aikin da ke gabana kawai na ke hasashe jiya ba a gyara gidan ba ga wanke wanke mai yawa ba a yi ba in dai ba ina so a zo gidana a tafi da ni a baki a bangaren kazanta ba ne. Dole na sauke son jiki na gyara gidana wayata na ɗauka zuwa kitchen na kunna karatun Qur'ni cikin suratul Maryam saboda ina son suran sosai ta na yi mini daɗi.
Chapter 8 · 0% Book details