← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 89

Sashe 72

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To Kawu a gidan ta take. Kuma ita ta dafa abincin da Gimbiya ta ci na ƙarshe ko kai ne Kawu wa za ka zarga?

"shi ne hujjar ki?

Sai ta yi shuru ta kasa mgana sai ya dawo da kallon shi kaina ya kira sunana na amsa cikin ladabi.

"Kamar yadda Bahijja ta yi mana bayanin abin da ya faru kema za ki iya yi mana bayanin farkon abin da ya faru?

"In sha Allahu Kawu."

"Bismallah."

Nima ko na gyara zama na fara mai da abin da ya faru tun zuwana gidan a jiya da zubar da abincin har zage zagen da muka yi ban ɓoye ba na faɗa na ƙarishe da faɗin" Kawu ni babban abin da ya fi ɓata min rai ƙazafin da suka yi min. Amma ta wani fannin ba ta da laifi tunda yar uwata ce ta ba da ni,   sai dai itama ba zan ƙyaleta ba mgana ta kai gaba za a ɗauki mataki. Saboda haka suma ina so a yi min adalci a bi min haƙƙin kazafin da suka yi min domin ba zan yafe ba "

Na karishe faÉ—a ina mai rufe fuskata saboda kukan da ya ta so min

"Kina da gaskiya. Tabbas wannan cim zarafi ne."

In ji Kawu Sa'adu."

"Ke Bahijja ni sa'an wasanki ne da za ki shiga gona ta don uban ki?
Kawu Abba ya faÉ—a bayan ya daka mata tsaawa a fusace saboda har da mganganun da ta faÉ—a akan Marwa sai da na faÉ—a.

Ai sai Anty Bahijja ta fara rantsuwa sharri na ƙulla mata ita ba ta ce  haka ba.
"Kuma ko mganar Kawu Abba É—in iita Æ´ar uwan Sadiya ta faÉ—a min."
Ta faÉ—a ta na wani tura baki saboda Kawu ya zage ta.

"To ina ruwan ki da Sha'anina! Ko uwarki gata nan zaune ba ta isa ta hana ni abin da na yi niyya ba. Sai dai ta ba ni shawara ballatana ke karan kaɗa miya? Kuma kina duniya zan auri ɗiyar yayar Sadiya sai dai ki mutu saboda baƙin ciki"

"Kawu ni.."

"Ba na son ji wata magana. Ke daman ina da labarinki kin cika saka ido. Ke wa ya je gidan mijin ki ya takura miki? Ok to ke da kike zaune lafiya ke ma asirin kike yi kenan ko?

Kawu Abba ya ƙarishe faɗa a fusace, da ga ganin yadda ya ke mgana ran shi a ɓace ya ke.
Tafida dai ƙala bai ce ba daga shi har Nene da Hajiyar Tafida.

Sai Anty Bahijja ta fara kuka. Kawu Abba ya ce ta rufe ma mutane baki, kuma fa bai girmeta ba amma matsayin shi na Kawunta sannan kuma daman shi ba shi da wasa.

"Kin takura mata ita da mijinta amma ke kina can kina zaune lafiya a gidan auran ki? Wanzami daman ai ba ya son jarfa ke ko an faÉ—a miki wata mgana ya kamata ki zo ki saki maganar kai tsaye? Shekaran Sadiya nawa tare da ku duk ba ki san haka ba sai yanzu?

"Ni kaina sai da na ce ta bar mganar da ta faÉ—a min amma ba ta ji magana ta ba "

Nene ta faɗa cikin bayyana ɓacin ranta.

"Ni fa ba laifin kowa na ke gani ba sai na wannan yar'uwan Sadiyan duk ita ta ɓata komai. Ya kamata itama ta na wajen nan"
Hajiyar Tafida ta faÉ—a itama.

"Ba ruwammu da ita. Can tsakaninsu ne da Sadiya amma tabbas alaqar tun da ba ta alheri ba ce rabuwar shi ya fi."
Kawu Sa'adu ya ce haka sai Anty Maimuna ta fara faÉ—in ai Ma'u ta na auran yaron yayar mijin Anty Bahijja ne.

"To sai me? Za mu raba alaqar ko da ta fi karfin haka ballantana ba ta yi wani karfi ba."

"Sosai. Tunda daga ita Bahijjan har ita dayan ba alheri a zukatan  su."

In ji Mimisco da daman ita yar gaskiya da gaskiya ce.
Duk kuma mganar da aka faÉ—a sai Anty Bahijja ta karyata Allah ya sa ga shaidu suka maida yadda na faÉ—a daki daki.

Gimbiya ta sha kunya domin kai tsaye Kawu ya kalleta ya na faɗin" Ke Saudatu  ke ma kin ƙara hura fitina ke da kika zauna gidan Sadiya ta dafa abinci ta ba ki kina kwance sai ki saka mata da sharri? Kuma ke fa kika aure mata miji ita ba ta biki da sharri ba sai ke?
Sai ta fara kuka tana faɗin a yi haƙuri kuskure ne ba za ta ƙara ba.

"Ba tarbiyan da na yi ma Saudatu ba kenan ni kaina ta ba ni kunya."

In ji Hajiyar Tafida. Ita kuma Nene sai ta ce koma me ya faru Anty Bahijja ce ta ja shi. Sai ta ƙara saka kuka ta na faɗin shike nan duk an maida laifi a kanta ba a duba nima cin mutumcin da na yi mata ba.

"Ke kika fara ci mata mutumci. Kuma ta yi min dai-dai da ta rama kwatankwacin yadda kika yi mata."

Tafida ya faÉ—a cikin fusata Kawu Abba ya taya shi da cewa" Kuma daman in babba bai ji kunyar hawa jaki ba. To shima jaki ba zai ci kunyar ka da shi ba. Ke kika zubar da girman ki, ban ga laifin duk wanda ya taka ki ba. Me ya sa ita Zuwaira ba a yi mata ba? Saboda ta kama kanta ba ta kuma zama ji da jiyarwan da kika zama ba."
Sai ta ƙara fashewa da kuka ta kasa mgana ita da Gimbiya sai kunya.

"Ba kuka za ki yi ba haƙuri zaki juya ki ba ta ki kuma janye kalaman da kika yi a kanta. In ba haka ba zan bar Tafida ya ɗau matakin da ya dace."
Kawu Sa'adu ya faɗi haka Anty Bahijja da ta san akwai ranar da za ta zo ta ba ni haƙuri da ba ta aikata ba abin da aikata ba. Kowa kuma ita ya ba ma rashin gaskiya har su Maman farko dole ta juya ta ba ni haƙuri na ƙi mgana.

"Sadiya ki yi hakuri kin ji ko? In sha Allahu ba za ta ƙara ba."

In ji Nene sai na ga girmama maganar Nene shi ya sa na ce na yafe mata amma sai dai na ce"kin ci darajan Yusuf da Nene shi ya sa na yafe miki."
Gimbiya ma aka ce ta ba ni haƙuri ta ba ni haƙuri Hajiyar Tafida ma ta ba ni haƙuri na yi shuru ban yi magana ba itama.

"Ki yi hakuri kin ji ko?

Yallaɓai ya faɗa a hankali ya na kallona.

"Zan haƙura amma sai na cire mata kokwanto."
Kafin ma ya yi mgana na zazzage jakata na fito da mgungunan a tsakiyar falon.

"Ga mganin da ta ce Inna ta ta kawo min mganin sanyi na wanke mahaifa ne na ga ta karɓo ma yarta yana yi shi ne na ba da kuɗi ta kawo min. Wallahi tallahi ban taɓa karɓan wani abu da sunan na asiri domin na cutar da mijina ko makusantansa ba."

Na karishe faÉ—a ciki son na yi kuka.

"Ba ki yarda da ni ba ne?
Yallaɓai ya katse ni, jin na ce zan Kira Inna Mariya ta yi mgana anan wajen.

"Ba sai kin kirata ba Na yarda da ke duniya da lahira Sadiya."

"Ba kai ba. Kowa ma saboda ya cire tantama a kaina."

Kawu Sa'adu ya ce a bari na kira hakan da na kyau. Nan ta ke na kirata na saka ta a handfree bayan mun gaisa sai na ce.
"Inna Mariya wai mganin da kika karɓo min mganin me ya ke yi wata ke tambaya ta?

"Ya na wanke mara sannan ya na mganin sanyi sannan ya na wanke mahaifa ko mace ta daÉ—e ba ta haihu ba in dai ta yi amfani dashi ana dacewa. Ya na da kyau sosai kin fara amfani da shi ne?

"Ban fara ba amma zan fara."

"Ki fara Sadiya in sha Allahu za ki da ce"

"Na amsa mata da Amin sannan muka yi sallama kai tsaye na kalli Gimbiya kafin na ce" Ina so ki sani ko ban taɓa haihuwa ba, ba zan yi shirka ba saboda ni na fito gidan tarbiya. Ballatana na haihu Saudatu ƴaƴana biyu ko a haka ubangiji ya bar ni ya gama min komai saboda haka ki sani ko duniya za ki tara abin da za ki haifa ba zai taɓa tsole min ido ba. Sannan duk da ban yi dogon zama da ke ba, ba zan yanke miki hukunci ba, zan yi miki kyakyawan shaida da uziri ina fatan ko anan gaba ki rika yi ma mutanen zaton alheri ba na sharri ba. Na yafe miki Allah ya kyauta na gaba."

Na faɗa ina mai kauda kai, sai ga shi kunya ya gama lulluɓeta. Kawu Sa'adu ya ce" Gaskiya ne ya kamata mu riƙa kyautatama junan mu zato."

Nima ya saka ni na ba ma Anty Bahijja haƙuri, na ba ta ba domin ina ji a raina na yi mata wani abun ba sai domin yi masa kara tun da shi babba ne kuma bai kamata na watsa masa ƙasa a ido ba.

Sannan ya sha ta layi tsakanin Bahijja da Ma'u ya ce kar ta ƙara zuwa gidan nan bai hana su haɗu can dangin mijinta ba amma in aka sake jin wata mgana ta bullo ba za su hana ni na ɗau matakin da ya kamata ba.

"Nima Kawu ka faɗa mata kar ta ƙara shiga harkan gidana da matana. Ba Saudatu ba Sadiya ba. Ta kama girmanta a matsayinta na yayata su kuma su girmamata a matsayinta na yayar mijinsu."

In ji Yallaɓai.

"Fakat"

Kawu Abba ya faɗa, Kawu Sa'adu ya ce gaskiya kar ya ji kar ya ƙara gani.
Har Anty Maimuna itama an ce kowacce ta ji da kanta ba ruwansu da matan ƙannensu. Mazan su ne dolen su su tsaya a kansu.
Itama Gimbiya Yallaɓai ya ce ya yi mata tsakani da Anty Bahijja bai ce ya raba su ba amma ta sani su yi zumumcin su kawai in har wani munafunci ya sake fitowa sai ta raina kanta da sauri ta ce ba za a ƙara ba.
Kafin a tashi Kaawu Abba ya gyara zama ya na faÉ—in"
Chapter 72 · 0% Book details