Sashe 11
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na so ne na juya cikin lumana na bar masa falon amma kishi ya sarrafa zuciyata domin a fusace na juyo, ko kallon Yallaɓai ban yi ba da wani uban sauri na wuce sa har ina bangazan kafaɗansa.
"Sadiya.."
"Sadiya.."
Haka ya riƙa kirana, amma ko juyowa ban yi ba, da wani irin zafi na buga masa ƙofar falon bam! Na kuma san sai da ƙaran ya shiga kansa ina tafe ne zuwa ɗaki amma ina ganin nisan shi a yau, ni dai kafata kawai ke tafe da ni ban san ya aka yi ba na ganni zaune saman cafet ina kuka bayan na shigo ɗakin barcin mu na rufe ƙofa duk ƙoƙarina na kar na yi kuka sai da na yi. A raina ina faɗin Yallaɓai ya cuce ni da ya yi auran nan a lokacin da ban yi zato ko tsammani ba.
 Ni dai tun da na shige ɗaki ban buɗe ba, ban kuma fito ba ina jin Yallaɓai ya gama bugun duniya da kiran sunana na yi masa banza. Sai da na ji fitarsa masallaci sallar mangariba na buɗe nima na shiga tiolet na yi alwala na zo na yi salla a lokacin su Jidda suka shigo sun dawo daga makaranta tun ɗazu wai Abba ya ce ba na jin daɗi, sai amsa musu da eh tunda ya ce ban jin daɗi ai shikenan zama na yi kan darduma ina ta salatin Annabi har sai da na samu natsuwa ana kuma kiran sallar isha'i na miƙe na yi ina idarwa na yi shirin barci na koma na kwanta. Ni yanzu ma waya ba ta gabana saboda na fahimci ita ke barazana da kwanciyar hankalina.
Yallaɓai sai bayan isha'i ya dawo ya kuma shigo ɗakin sai na fara nishi kamar ban da lafiya. Sai ya ruɗe ya ƙariso gare ni yana tambayata meke damuna na dafe kaina na ce kaina ne, ya ce zai bani magani na ce ai nasha. Bawan Allah ya bani tausayi haka ya zauna a kusa dani ya na ta min sannu ni fa daman guje ma mganarsa ne a yau ya sa na yi haka ganin yaƙi tashi a kusa dani ya sa na fara barcin ƙarya, ganin haka yasa ya gyaramin kwanciya ganin ina zufa sai ya kunnamin fanka ya fice bayan ya rage min hasken ɗakin gabaɗaya.
Yana fita na mike zaune ina mai harɗe hannayena a saman kirjina. Na daɗe ban yi barci ba ina ta tunanin wai yau Yallaɓai ba nawa ba ne ni kaɗai kai lamarin akwai girma. Tun ina jiyo ƙaran tibi daga falon yara har barci ya ɗauke ni sai asuba na tashi, da rawan jiki ya fara min sannu har ya na taɓa goshina.
"Ya kan na ki? Ya yi sauƙi?
Sai na gyaɗa kai ina faɗin ya yi sauƙi saboda na ji yana faɗin in ba zan iya ba na ɗaga zuwa asibiti sai wani sati da sauri na ce zan iya.
Yallaɓai ranar ya yi ma yara da mu kan mu abin kari, doya ya soya mana sai abincin jiya da ya ɗumama duk tare za mu fita shima ya na da zuwa jana'iza baban wani yaron shi ne ya rasu a can sheƙa. Su Jidda suka fara tafiya mu kuma takwas da rabi muka fita ni da Yallaɓai sai da ya fara kaini asibiti sannan ya wuce jana'izan da za a yi ƙarfe tara na safe ya na ta ma sauri, ni kuma har muka rabu ban iya ce masa daga asibiti Ɗorayi zan wuce ba na bari sai na gama da asibitin sai na kira shi na faɗa masa.
 Yau ban samun ganin Dr.Aisha Bukar da wuri ba, saboda ba ta zo da wuri ba , sai 12pm na rana na baro asibitin. Daman na je mata da Test ɗin da ta rubutamin a ƙarshen zuwana tun da yanzu bayan sati uku na ke dawowa. Yau ma ta ƙara rubuta mini wani amma tace shi ne na ƙarshe, daga shi za ta ɗora ni kan mganguna.
 "Dr kina ganin zan ƙara samun ciki har na haihu?
Na faÉ—a cikin karaya saboda ni dai na gama sarewa.
Sai da ta kalleni kafin ta maida hankalinta kan fayel É—ina ta na rubutu.
"E mana. Me zai hana? Likitoci ai ba Ubangiji ba ne, duk abin da muka faÉ—a hasashe amma ba gaibu ba ne. Balle ni ban ce miki kina da wata matsalan da ba za ki sake haihuwa ba. Za ki sake haihuwa haife haife ma in sha Allahu."
Haka aka sha faɗa mini amma kuma kalaman Dr Aisha ya sa na samu sukuni, na yi mata godiya da ya ke mun saba sosai da ita. Sai da na fito bakin asibitin na kira wayar Yallaɓai bai ɗauka ba sai na ƙara kirana har sau uku amma bai ɗauka ba.. gani a bakin hanya ina son hawa adaidaitan da za ta kaini Ɗorayi.
 Dubaran tura masa saƙo ya shiga kaina. Da sauri na shiga bangaren saƙonni na lalibo Yallaɓai tun saƙon Anniversty da na tura masa bai ko ba ni amsa ba, ban damu na shiga yi masa rubutu.
"Ina so daga asibiti na je gida na gaida Alhajinmu."
Na daɗe fa a bakin hanya raina har yafara ɓaci har na yanke shawaran ƙarisawa Office ɗin sa tunda ya ce min daga wajen jana'iza office zai zo, da ya ke ba nisa offishin na su na can gaba ne ko a ƙafa ma zan iya takawa. Ina wannan tunanin sai ga saƙon sa.
"Ok."
A takaiçe haushi ya kama ni na yi ja dogon tsaki na maida wayata jaka na samu adaidaita da za ta kaini ɗorayi. Ina sauka a a bakin layi na tako zuwa cikin layi na haɗu da wasu matansa anguwa muka gaisa. Na shiga gida ana ta kiran sallar azahar na samu Gwaggo a tsakar gida ta na alwala gidan shuru.
Ina sallama Gwaggo ta É—ago ta na amsawa.
"Ah maraba Dubu ke ce tafe? Na amsa mata ina gaisheta ta amsa lokaci ɗaya tana tambayan Yallaɓai da yara, nace suna lafiya.
ÆŠakinta muka shiga ina tambayan Alhajinmu ta ce jiya ya je can yashe sai yau zai dawo.
"Topha lafiya ko Gwaggo?
'Lafiya lau. Kan auran autan su Muntari ne kinsan bikin saura kwana goma."
Gwaggo ta amsa min.
Shaf na manta da bikin kuma daman na yi alƙwarin sai na je wannan karon.
Nima sauke jakata na yi na tuɓe hijabi na fita na ɗauro alwala na zo na yi sallah bayan na idar Gwaggo ta ce ɗanwake ta yi na je na zuba na ci, ina son ɗanwake jikina na rawa na tashi na je na zubo na dawo ɗakin ina ci muna hira sai da na gama na sha ruwa sannan na ce mata daga asibiti na ke.
"Allah sarki ina fatan dai ba matsala ko?
Sai na amsa mata da " Muna saka ran haka Gwaggo."
Sai ta yi min fatan Allah ya sa a dace ta ce min akwai na gargajiya a can gida ta yi mgana za ta karɓo min na ce to bari in na gama shan na asibitin tukkuna. Tun da Alhajinmu baya nan Gwaggo na faɗa ma ƙarin auren Yallaɓai itama ta sha mamaki har sai da ta furta..
"Topha aure haka bagatatan Sadiya?
Ni kuma sai na ce mata an É—aura ne amma ba a yi tariyan ba, duk da ban sani ba amma alamu sun nuna mini haka. Gwaggo ta yi fatan alheri nima kuma ta yi min nasiha ta ce sai na yi hakuri na kauda kai na ce mata in sha Allahu.
Ina gida tare da Gwaggo muna ta hira sai gabda la'asar na yi ma Gwaggo sallama na ta fi gida bayan na ce a gaida Alhajinmu in ya dawo.
Ina komawa gida na yi salla na shiga kitchen kuskus na dafa mai kayan lambu da hanta. Sai na yi lemun ginger na saka a fridge ya yi sanyi, Yallaɓai ya ba ni mamaki ko ya kirani? Har wayata na dinga dubawa amma bawan Allah bai kirani ba sai kuma abin ya dameni ai ya ga saƙo na ko? Wata zuciyar ta tunaar da ni yanzu fa ba ke kaɗai gare shi ba bai zama lalle sai ya damu da ke kamar baya ba.
Ina ta so yakice tunanin haka a raina amman na kasa gaskiya kishi akwai wahala gabaÉ—aya har na fara rama a tsaye saboda zullumi da tunani ban sani ba.
******
Gwammaja.
Wajajen takwas da wani abu na dare ya shigo anguwan gwammaja a motar shi. Ko a cikin gidan ma ya daÉ—e a mota ya kasa fitowa bayan ya kashe motar. GabaÉ—aya jikinsa ya yi sanyi ko na ce ya mutu.
Ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cak ya kasa ma wani tunani tun safe ya ce tun bayan barowansa wajen gaisuwan nan ya ji kamar zazzaɓi zai kama shi, ya je office ya yini amma ya kasa taɓuka komai kamar mara lafiya.
Ya na gani Sadiya na kiran shi ya kasa ɗaga kiranta to me zai ce mata! Akwai wasu kalaman da zai iya kare kanshi ne da su ne? Ya ga saƙon ta ok ɗin ma da ya tura mata hannunsa na rawa ya tura mata, domin gani ya ke yi duk abin da ya ce ko zai ce a baya da yanzu Sadiya ba za ta daina masa kallon maƙyarci ba kuma ma ci Amana ba, duk da ba haramci ya aikata ba.
Amma dai ba daÉ—i shi kan shi ya sani bai kyauta ma Sadiya ba