← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 89

Sashe 37

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwafa na yi kafin na ce"ka ji min yarinya mara mutumci kawai da mangariban nan ki É—aga min hankali! A'a ba gidan Anty Gimbiya ba saura gidan Sarki."
Raina a bace na koma É—aki ina magana ni kaÉ—ai.
"Mata duk ta bi ta gama min da Æ´aÆ´a. Ina dalili."
Wayata da ta kwana ma a kashe ban san ko uban na su ma yau ya tuna da su ya neme ni ba. Sai ga shi can ajuma na koma na ganta har ta yi barci a raina na ce ashe ma iskanci ne irin na yara, Jidda ma da wuri ta kwanta ranar amma ni na É—an dade ina kallo saboda ma kar na kwana ni kaÉ—ai na yi tunani na ce Jidda ta zo É—akina mu kwana ni kuma na É—auki Baby na kaita bedroom É—ina na kwantar.

Ranar tare da yara muka yi barcin mu har da su makara domin sai shidda na safe muka farka. Qur'ani na riƙe shi kuma ya kawo min salama da kwanciyar hankali a kwanakin da Yallaɓai ya yi a gidan wata mace ko na ce wata matar ta sa bayan ni, sai a ranar na kunna wayata na kikkira mutane na yi musu ban gajiya Amina ma ta ce jiyan da suka isa gida ta yi ta kirana a kashe haka ma Farida ta ce itama ni dai na ce su yi hakuri wayar ce ta mutu ba chaji ban sani ba.

Ina lissafe da yau kwanan Yallaɓai uku kenan a gidan Gimbiya na ɗan ji ba daɗi da na kunna wayata ban ga saƙon shi ba amma dai ina ji a jikina ya kira ni wayar ce bai samu ba. Ko bai sanar da ni ba na san kwanakin bazawara kwana uku ne yau Yallaɓai zai dawo gidana shi ya sa da yamma na dumama sauran kazar da na siya wajen Hajiya Surayya Halin yau, na ci tare da tsumi karfe bakwai da wani abu na yamma Yallaɓai ya kira ni lokacin ma ina kan darduma ina lazimi ne bayan na idar da sallar mangariba.

Ban ɗauka a lokacin ba sai da ta katse sannan ba daɗewa ya ƙara kira sannan na ɗauka cikin sanyin murya lokaci ɗaya da sallama a bakina.
Sai ya amsa min daga can bangaren shima a sanyayen, tambayar ya kuke? Ya yara na ce lafiya lau daga nan shuru muka yi dukkanmu na wani lokaci.

"Me ya faru jiya da yau wayarki a kashe."

"Ta mutu ba chaji ne ban sani ba."

Domin kar ma ya kawo tambayar ba wuta ne? Shi ya sa na ce ban san ta mutun ba.

"Ok. Yanzu ba daÉ—ewa za mu taho nan gida tare da Daugther"

Haka na ji ya faÉ—a sai da na dan yi jim kafin na samu damar magana ya cigaba da faÉ—in" ina so zan yi magana da ku gabaÉ—aya."

Sai da sauke ajiyar zuciya sanna na amsa masa da cewa.

"Shike nan sai kun ƙariso."

Da ga haka muka yi sallama ban tashi ba sai da na gama lazimina na yi salatin Annabi na shafa sannan na miƙe na ninke darduman na ɗora saman gado daman na yi wanka na saka riga da wando. Ban kuma jin zan iya sauya shigata turaren wuta na ɗauka na fita falo na  saka Jidda ta kunna Burner gidan ya dan yi kamshi Baby kuma na baje a falo ta ba je littafinta na drowing ta na ta zane zane kuma ta na bin shi da kala a baya in na gani sai na hana ta Yallabai ya ce na kyaleta na sani ko ita ce za ta ga je shi? Tun daga lokacin na saka mata ido daga karshe ma katon drawing ya siya mata mai kama da littafi da pensira na zane da clours ya na zane ni, in akwai makaranta ban barin ta yi amma yanzu da suka samu hutu ba na hana ta.

Muna zaune a falon gabaɗayan mu mu ka ji shigowar Motar Yallabai gidan da ƙaran rufe get, tun da karfe ne dole in an buɗe ko an rufe sai mun ji kara. Jidda ta daka tsalle ta mike ta na faɗin" Baby Abba ne."
Daga ita har Baby a guje suka fice baby ta yi falati da kayan zanen ta suka fice da gudu suna kiran oyoyo Abba, na ji buÉ—e kofar falon da yadda yaran suka naÉ—e shi da muryan shi ya na faÉ—in.

"Oyoyo My princess. I miss u."

Ina zaune a in da na ke na kasa tashi. Haka kurum sai na ji gabana na faÉ—uwa ras! Kamar kuma sai na ji kamar wani tsoro tsoro na shiga ta.
Yau ne fa zan hada ido da kishiya? Kishiyar da mijina ya kwana da ita har uku. Ƙilama akwanakin nan ta samu ciki.

"Auzubillahi minal sheÉ—anir rajim"

Haka na faÉ—a da sauri domin koran sheÉ—an É—in da ya ziyarce ni.

*Janafty*
*TKG*

*Assalamu alaikum!*
*Ina muku gaisuwa irinta addinin musulunci da fatan masoya labarin ƳAR KARUWA suna cikin ƙoshin lafiya,baya ga haka ina muku albishir da cewa free pages na labarin ya ƙare mun shiga asalin labarin wanda ya kasance shine part 2 na labarin.*
*Karku manta bamu ce komi ba a free page's na labarin domin kuwa yanzu nema za a fara wasan,don haka karku bari ayi tafiyar babu ku masoya.Ku hanzarta ku shigo cikin tafiyar ARCH.AMMAR CHIROMA TARE DA HAFSAT KABEER CHIROMA,Tabbas a cikin wannan tafiyar akwai tarin faɗakarwa,zazzafar soyayya,ƙiyayya mai zafi da kuma halacci.*
*Paid page's sun fara sauka a manhajar whatsapp da kuma Telegram,masu biyiyar arewabook tuni labarin part 2 ya fara nisa a can,sai ku garzaya domin Shan karatu.*

*Ku biya kuɗinku ta wannan asusun Kamar haka👇🏻*

For VIP on Telegram Pay 1k for Whatsapp group Pay 500 in to this account 👇🏻
7087809778
Aisha Dansabo Ibrahim Opay,evidence of payment to 08167768704.

*Masu buƙatar free pages na labarin ku tuntuɓeni ta wannan line ɗin 08167768704.*

10.

Ina zaune ne amma na kasa tashi domin sai na ke jin gabaɗaya ilahirin jikina na rawa. To in ma na tashi wa zan je tarowa? Kishiya ko miji? Kawai sai na yi zama na amma fa zuciyata bugawa ta ke yi da sauri da sauri cikin lokaci ƙalilan hankalina ya tashi ina neman fita hayyacina saboda wani iri abu na ke ji yana ta so min daga ƙasan zuciyata.
Kishi masifa ne, zai iya haifar ma da mata lalura mai karfin da nan ta ke za a iya kai su emergency a yi tunanin ciwon ya daÉ—e a jikinsu ne ba a sani ba alhalin kishi mai saka ma zuciya ciwo nan take ba tare da mutum ya sani ba.

Idanuwana suna kallon ƙofar falon suka shigo, shi ya buɗe mata kofar ta fara shigowa hannunta na riƙe da na hannun Baby.  Sai shi ya biyo bayan su, shima hannunsa na riƙe da na Jidda. Gimbiya fara ce sosai doguwa domin har ta ɗan fini tsawo sannan tana da jikin murjewa kyakyawa ce domin hancin ta har baka. Sanye ta ke da atamfa mai kalan orange shi ya sa mayafin da ke jikinta ma kalan shi kenan, shi kuma Yallaɓai an cakare cikin ƙananun kaya har da zanzaro. Dukkansu fuskarsu tana fitar da wani annuri ne. Annurin da ka na ganin shi za ka san na farinciki ne wanda zuciya ke samu ta hanyar gangan jiki.

Duk ina zaune ne na ƙare musu kallo, ina ganin za mu haɗa ido da su na yi saurin ɗauke kaina ina jin zuciyata na ƙara tsananta bugawa. Ina jinjina ma matan da ake yi musu kishiya sannan a haɗa su zama da su a gida ɗaya. Wallahi in ni ce ba zan iya ba, domin na tabbata wata rana zan iya haɗiyan zuciya na mutu saboda baƙin ciki.  Da na so na tashi na tarbe ta amma daga baya kawai sai na fasa sai ma gyara zaman da na yi daga in da na ke zaune na ce.

"Sannun ku da zuwa."

Na faɗa ina ƙara gayyato mirmishi a saman fuskata.
Ita ta amsa amma a hankali shi ne na ji amsar ta shi da ƙarfi yaran na maƙale da su, shi ya nuna ma Gimbiya kujeran da za ta zauna na zaman mutum biyu, ta isa ta zauna Baby ta haye jikinta shi kuma sai ya durkusa a gabana lokaci ɗaya ya na mai riƙe duka hannayena cikin tafukan hannunsa so ya ke mu haɗa ido, ni kuma na ki bashi damar haka sai ma Juyawa da na yi ina kallon Jidda da ta zauna gefen Gimbiya sai mirmishi suke yi daga ita har Baby umh yara ai ba ku san dawan garin ba.

"Jidda kawo ma Antyn ta ku ruwa da lemu mana."

"To Umma."

Ta faÉ—a da saurin ta sannan ta ta shi ta nufi kitchen É—in.

"Kalle ni mana Sadiya ta."

Ya faɗa ya na leƙa fuskata sai na yi fuska ma maze na kalle shi ta ƙasan idanuwana. Haushi fa ya ke ba ni, hannayena ma da ya riƙe ji na ke yi kamar na ƙwace, domin haskowa na ke yi da waɗanan hannayen na shi fa ya riƙe Gimbiya da su, shi ne nima zai dawo ya na taɓa ni tuni na ji gabaɗaya hannayensa sun zame min kamar lantarki mai ja a cikin hannayena sai ƙokarin kwacewa na ke yi ya na ƙara riƙe ni, ita kuma Gimbiya ba ta kallon mu tana ta hiran ta ita da yara.

"Yallaɓai. Ka bari mana."
.

Na faɗa bayan na ƙwace hannayena lokaci ɗaya ina kallon shi.

"Ba ki yi mini sannu da zuwa ba."

Ya sake faɗa yana mai ƙure ni da ido.

"Shi wanda na yi maka fa?

Kawai sai ya buÉ—e mini hannuwansa yana faÉ—in" Ba wannan ba irin wannan."
KaÉ—an ya rage ban danno masa na katsinawa ba amma dai na daure ban yi ba, sai ma hararan shi da na yi na matsa gefe ina kallon Gimbiya.

"Ki sha ruwan mana."

Ta na kallona ta ce" Zan sha."
Chapter 37 · 0% Book details