Sashe 23
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Gaskiya ne. Nima dai haka na ce a raina. Ina laifin ta bari in ya zo ya faÉ—a miki sai a saka rana tun da ta matsa sai an É—aura."
Hauwa ta faɗa kai tsaye Munnira ta gyara zama ta na ƙara faɗin" Ni fa ban iya shuru ba, har Nasir sai da na yi ma ƙorafi namiji ne kuma ɗan'uwansa ne shi kan shi ya ce ba a kyauta miki ba, ya kamata a fara ba ma Tafida lokacin da zai yi miki mgana da ke haƙƙin ki ne mganar wai da ke da Gimbiya ɗaya ta ɗauke ku ta faɗa ne kawai amma Ke suruka ce a wajenta matar ɗan ta. Gimbiya kuma ƴa ce a wajenta kuma suruka gaskiyan mgana kenan, sauran mganganunta kuma gaskiya ta faɗa ko Nasir ya ce ya na da kyakyawan shaida a kan Yallaɓai na daraja ki, na yarda da duka Nasabobin da ta ce Ubangiji ya ba ki amma kar ki sake ki ji a ranki da cewa Nene da yayanta za su ɗauke ke da Gimbiya ɗaya. ba gaskiya ba ne Sadiya. Kawai dai a yi sha'ani an cuci na ƙauye."
Duk fa abin da ta faɗa gaskiya ne. Ni daman ban isa na haɗa kaina da Gimbiya ba kuma ko Nene ta so ta ɓoye laifinta gaskiya ɗaya ce daga ƙin ta sai ɓataa ta yi son kai a wannan lamarin daga baya ne ta ji kunya ta zo ta na gyaran zence.
Yadda Munnira ta tsani kishiya ina tunanin in ita ce aka yi ma irin auran Yallaɓai da Nasir da Duniya ta gama jin kansu. Faɗa min ta ke yi na saka a raina kawai ni girman ne Allah ya ba ni na kama kaina amma ba ta ce na zauna a takani ba duk da ta san halina.
Hauwa dai ta na gefe yar cewa gaskiya ne, sun daÉ—e a gidana sai wajen biyar na yamma na raka su har bakin titi suka samu adaidaita sahu.
Kafin tafiyar su har mganar tafiyata Yashe na yi musu Munnira ta ce wallahi gwara na je na huta ko na samu salama mganar tariya suka yi min na ce ban sani ba Munnira ta ce da an tsaida lokaci na sanar da su za su dawo mu ma shiri za mu yi duk da ta sanni ni ɗin a shirya na ke, sai dai kawai na ƙara sabon shirin.
Na ji daɗin zuwan su kamar kar su tafi haka na dawo gida ni kaɗai duk sai na ji kewa, Allah ya taimake ni Khaleesat ta kirani a waya muka kusa awa muna hira. Kan dai maganar auran Yallaɓai ne itama faɗa min ta ke yi ta yi mamakin auran nan gaskiya. Duk daɗewar da muka yi muna waya shawarwari ta ke ba ni, na kama kaina na ƙi ji na ƙi gani, da sauran shawawarin masu girma ciki daman shi ne haƙuri sai na ninƙa haƙuri domin zan ta ganin abubuwa.
Kowa fa maganarsa kenan akwai zafi sai na daure, kuma kowa kalmarsa kenan sai na yi hakuri wato an san cewa lamarin akwai zafi akwai ciwo an kuma san zan ta ganin abubuwa sai na yi haƙuri ni dai fata na Allah ya sa har Yallaɓai ya yi gangancin cewa a nan gidan za ta zauna domin a lokacin ne zan yi abin da ba a yi tsammani ba. Gidan nan gidan shi ne amma kuma ya zama gidana tun da domin ni ya gina shi, in ina ma tuna yadda a ka gama gidan har na tare a ciki sai dai kawai na kaina wani abun gwara ka bar shi a rufe bayyana shi ba shi da amfani.
Sai da su Jidda suka dawo makaranta gidan ya ɗan min daɗi. Yallaɓai tun safe da ya fita sai bayan isha'i ya shigo gidan da tarkacen su cakulate da ice crean ɗin da ya siyo ma Baby. Ya na dawowa ya yi wanka sannan ya ci abinci farar shinkafa na dafa masa tun da shi ba ya son taliya, ya na gama ci ya ce su Jidda su shirya za su je Gwammaja domin duba Gimbiya ni har na ma manta da maganar amma shi ya na nan sane.
Yaran ko suna ta murna ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah. Yallaɓai ya sha shigan ƙananun kaya rigar fara ce haka wandon kuma baki ne har da saka rufaffen takalmi da daddaren kamar wanda zai je taɗi! A raina kuma sai na tuna ai ya na da Amarya shi ke da ko babban taɗi adon ma domin ita ya yi shi ya sa gabaɗaya na yi kici kicin da raina. Lokacin da za su fita na rakasu har bakin ƙofar falo, har Yallaɓai ya fita yaran sun yi gaba suna ɗaga min hannu har na ba ma Jidda Soyayyen nama na ce ta kai ma Nene ina tsaye riƙe da kofar falo na kasa tafiya sai na ji kamar an dasa ni.
Kawai sai na ga Yallaɓai ya dawo sai ya ganni a tsaye riƙe da ƙofa sai muka tsaya muna kallo kallo.
"Lafiya! Ko ka yi mantuwa ne?
Na tambaye shi ganin ya na kallona. Sai ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" E. Na manto waya ta a É—aki."
Sai na juya na ce bari na ɗauko masa a can bedroom ɗin mu ya barta ina ɗauko ma sa wayar hannuna tsautsayi ya sa na ta ɓata sai hasken ta ya kawo, idona ya hango min Daugther 3 missed call. Da sauri na danne gefe hasken wayar ta ɗauke, da sauri na koma na kai masa wayar ya karɓa ya na kallona kafin ya ce.
"Thank you."
Ya faÉ—a lokaci É—aya ya na zura wayar cikin aljihun wandon shi sannan ya É—ago ya na kallona, idanuwana na ware masa ina kallonsa da sigar tambaya.
"Ba damuwa in muka bar ki a gida ke kaÉ—ai.?
Sai kawai na tsaya ina kallon shi a fuskarsa na gama nazarin abin da ya ke nufi da maganarsa amma ban nuna masa na gane in da ya dosa ba.
"Babu."
Na bashi amsa a takaice, ya fita ni kuma na ja ƙofar zan rufe sai ya kira sunana.
"Sadiya ta."
Sai na dakata ina kallon shi har ina gyarawa tsayuwan yadda zan yi ma Yallaɓai tijara in har ya sake ya ce na shirya mu je gaida amaryansa sai Allah ya ƙwace sa bai ce ba.
"Bar shi ma. In dai na dawo za mu yi mgana."
Sai na gyaÉ—a kaina lokaci É—aya ina faÉ—in" A dawo lafiya."
Daga haka na maida kofa na rufe na koma can falon yara na zauna, ba na son damuwa ya sa na ɗau romot ina yawo a tsakanin tasha she, har dai na tsaya a Mbc2 suna haska wani american film mai kyau shi na tarrara ma hankalina gabaɗaya nan saboda kallon da ya ɗau hankalina ban ma ga daɗewarsu ba, sai da na ji kiran Yallaɓai a waya sannan na ga duba lokaci goman dare har ya gota.
Yallaɓai na min ƴar murya wai ya siyo min tsire ko kaza? Ni ko na ce muna da sauran nama.
"To ko fura ba za ki sha ba?
Kar ya ga na ture ƙoƙarinsa sai kawai na ce ya siya min kawai furan, ba su shigo gidan ba sai goma da rabi na yi mamakin ganin har Baby ba ta yi barci ba na ɗauka acan ma za su fara barci,sai dai suna dawowa ta ce min Umma ina jin barci na ce ta shiga ciki mana ta kwanta. Jidda kuma na ce ta ta ya Baby ta cire kayan jikinta ta saka na barci, ni kuma da na yi ma kaina tsiya domin furan da Yallaɓai ya siyo min ita na sha na kwanta kuma na ji daɗin furan bakina ya yi min daɗi sosai.
Kafin mu kwanta ya ce ina abin da ya ce na rubuta sai na nuna masa a wayata.
"Kin tabbata su kenan muke buƙata?
Ya faÉ—a ya na kallona lokacin dukkanmu muna saman gado amma ba mu kai ga kwanciya ba.
"E yanzu dai su kenan gaskiya."
"Bari da safe sai na tura can singer. Na ku kuma zan saka miki kuÉ—in in sha Allahu."
Na amsa masa da Allah ya kaimu amin, har na juya zan kwanta na ji ya kira sunana.
"Sadiya."
Sai na juyo ina kallon shi kafin na amsa masa.
"Na'am."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Yau Nene ta yi min mganar tariya. Ta ce in son samu ne zuwa karshen watan nan."
Gabana ya faÉ—i amma ban nuna masa ba.
Sai kawai na kalle shi kafin na ce" Allah ya nuna mana."
"Amin. Ita ma Daughter na yi mgana da ita yau. Ta ce ba ta da matsala ko yaushe ne."
Ya na mgana ne ina kallon shi kawai ina ganin kamar almara. Wai yau ni Yallaɓai ke maganar watar matar tasa da ni turƙashi!
"Shi ne na ce a bari na zo gida na ji na ki tsarin? Lokacin ya yi miki?
Sai kawai na yi mirmishin, mirmishin da iyakarsa saman leɓena.
"Ni miye na wa a ciki? Tun da Nene ta amince da ita kanta Gimbiya ni me zan ce? Allah ya nuna mana."
"Akwai na ki a ciki mana Sadiya."
Ya katse ni, sai kawai na ƙura masa ido ba tare da na yi magana ba.
"Saboda ke matata ce kuma kina da haƙƙin na sanar da ke abin ke faruwa kuma na ji ra'ayin ki"
"Oh! Haka ne?
Na faÉ—a ina kallonsa in zai lura kallon kar ka raina ma kanka wayau na yi masa ban sanin masa in ya gane.
"E. "
Ya faÉ—a ya na kallona saboda ba na son maganar ta yi tsayi ya sa na gyaÉ—a kaina kafin na ce" To na ce komai ya yi. Allah ya nuna mana."
Ya amsa da Amin amma a sanyaye, juya masa baya na yi ina gyara kwanciyata.
"Zuwa da safe za mu ƙarishe maganar."
"Allah ya kaimu."