Sashe 2
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shima yau ɗin ya raba ni da wata ni ai ba Sadiyarsa ba ce ni kaɗai ya na da gimbiya shi ya sa yau Yallabai ya ke kirana Sadiya gatsal ta sar ma ya kasa ma minibwannan karan. Ji na yi kamar na fashe da kuka saboda baƙin ciki.
"Sadiya.'
A wannan karon da ɗan karfi ya sake kiran sunana. A sanyaye na kalleshi kuma kallon bai yi yawa ba na yi saurin kauda kaina ina ƙoƙarin miƙewa sai na ji duk jikina ya saki. Amma hakanan na miƙe ina ƙokarin dai dai ta kaina ina gani ya na nuna min gefensa na yi kamar ban gani ba na zagaye shi na isa kujera mai zaman mutum biyu dake gefen su na zauna. Ban kalle shi ba sai na sadda kaina ƙasa ina wasa da zoben azurfan da ke hannuna.
"Sadiya ta."
Sai yanzu? Sai yanzu ne ya gane ni tasa ce kafin ya samu wata. Haka na faÉ—a a raina sai na É—ago idanuwana da na ji har nauyi sun yi min ina kallon shi, shima fa karfin hali ne amma kunya da nauyin Sadiya da ya ke ji sun hana shi sakewa.
"Na tambaye ki meke damun ki, kin ce min bakomai."
Ya faɗa ya na mai kureni da ido a cikin zuciyarsa kuma na san bugu ta ke yi saboda nima ƙura masa ido na ke yi ina hasashen shike nan yanzu wai kwana zan riƙa rabawa da wata a kan Yallaɓai ko? Shi kenan mun tashi daga Family of 4 mun koma Family of 5 ƙilama kafin a rufe shekara ta haihu za mu hauhawa. Sai na ji kuka na taho min amma na yi saurin kannewa.
"Me ke damun ki? Ko an faɗa miki wani abu ya faru ne?
Shike nan ya fara kama kanshi da kanshi. An ce mara gaskiya ko a cikin ruwa ya ke gumi ya ke yi. Da gangan na kalle shi sai na ga ya daburce yana ƙokarin gyara mganarsa.
"Nufina ko can Ɗorayi su Alhajimmu duk lafiya ko?
Mirmishin takaici ya kwace min. Yallabai ya na so ya raina ma kansa ma wayau. Ya na tunanin abin da ya rufe bai faÉ—a min ba ya na ji a ransa zai tabbata a rufe ne ni ban sani ba.
Sai kawai na yi masa wani kallo kafin na ce" Ko ɗaya. Ba abin da ya faru kawai raina ne ya ɓaci ba ka dawo da wuri ba alhalin kasan tun karfe nawa muka shirya ni da yara muna zaman jiran ka?
Na faɗa hawaye na ciko min a ƙwarmin idanuwana. Ƙura masa ido na yi sai na ga ya sauke ajiyar zuciya irin na samun salama ya na neman ɗauko mgana na yi saurin tare shi da faɗin" Mu yanka cake ɗin ina jin barci.'
Na faɗa ina mai kauda kaina saboda ƙokarina na maida hawayena sai ma na ga sun koma da kansu ba tare da na yi yinƙurin maida su ba.
"Sadiya"
Ya sake kiran sunana a zafafe na juya na kusa na ce ya daina kiran sunana haka tunda ba shi ya raÉ—a min ba amma sai ya yi sauri tare ni da cewa.
"Ta so ki zo nan ki zauna kusa da ni."
Ya faɗa ya na nuna min gefensa. Kamar na ce bar ni anan sai kuma ban ce ba na tashi na koma kusa da shi na zauna amma ban matso kusa da jikinsa ba sai shi ne ya sauke Baby da ke kan jikinsa gefen Jidda sai ya ƙara matsoni ba zato kawai na ji ya sunkuya ya sumbaci kuncina kallonsa na yi bai bani zarafin mgana ba ya yi mirmishi kafin ya ce.
"Ki yi hakuri Sadiya."
Kallonsa na ke yi amma na kasa mgana sai ya ƙara marairaicewa ya na ƙara matso ni a jikina.
"Sorry ba na ce ki yi haƙuri ba? Kin ji ko?
Ya faɗa ya na ƙoƙarin saka hannu ya ɗago haɓata da sauri na kauda kaina ina faɗin" Nima ai na ce komai ya wuce ko?
Sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Yaushe kika ce! Yanzu dai ko?
Ban iya ma yi masa mgana ba ya dame ni kamar na ce ya matsa baya amma na kasa. Shi bai san ni yanzu ba na so ma ina zuwa kusa dashi ba a raina na ke jin duk abin da na ke tunanin ni kaɗai ke da shi yanzu ya tashi a mallakina nawa ya koma mallakinmu kuma namu. Ya yi ƙokarin ba ni haƙuri amma kuma ya kasa bayyana uzurin da ya zaunar da shi tun safe sai dare, Me ya sa Yallaɓai ya boye min ? Zan hana shi aure ne? Ni a cikin zuciyata na fi jin zafin munafuntata da ya yi sama da auran shi. Har Ma'u ta na murna ta samu makamin da za ta ya ƙe da shi ni kuma na ce ƙaryanta ba zan taɓa bari ta samu wannan damar ba.
Mun yanka Cake amma wannan shekaran Walimar tamu ba cike take da farinciki ba. A fuskata za ka fahimci ba na cikin farinciki shima kuma haka su Jidda ne kawai ke ta murn. Ko wajen yanka cake ɗin ma hannuna saman na Jidda na ɗora sai shi ne ya ɗau hannuna nawa ya ɗora saman wukar sannan ya kama sai ya ce yaran su ɗora saman na shi. A haka muka yanka cake ɗin kuma wajen ba da wa yarana na fara ba mawa sannan shi na karshe in da a ce zan yi masa kutumar uba wallahi ko kallo bai isheni ba amma hakanan na daure ma zuciyata. Shi ko ni ya fara yankawa ya saka min a baki wanda dakyar na buɗe bakin duk ma ya shafa min a gefem baki ya na ƙokarin ya saka hannu ya goge min na goge da kaina sai ya koma ya na ba ma su Jidda cake ɗin suma suna bashi suna ta dariyan farinciki ina kallonsu a cikin raina ina tunanin shike nan Yallaɓai ya yi sanadiyar lalatamin farincikina na wannan ranar. Daman ya ce zai ba ni suprise lalle na karɓi babban suprise da ba zan manta da shi ba a rayuwata ba.
Na gaji so kawai na ke yi na keɓe ni kaɗai. Shi ya sa kawai na mike na isa ga ƙwalin agogon da na siya masa ban jira na bashi a hannunsa ba na ijiye masa a gabansa ina faɗin" Gift ɗin ka"
Na ga ya yi shuru ya na kallona ni ko sai na yi saurin kallon su Jidda ina fadin" Oya tunda an gama ku je ku kwanta."
Da sauri ya ce" Ba mu gama ba. Ba mu yi ciye ciye ba Madam."
 Ina kallonsa ina shirin mgana da sauri ya ce" Kuma na siyo kaza gasashiya da tsire ba ki duba ba."
Sai na fara hammar ƙarya ina faɗin" Ina jin barci Yallaɓai."
Haka na faɗa kawai sai na ga ya miƙe ya na mai ɗaukan kwalin agogon ya bude ya na gani kafin ya kalleni ya na min mirmishin da ni yanzu ya daina yaudarata.
Ban tammaci haka ba. Shammata ta ya yi ya kawo min rumguma lokaci É—aya yana faÉ—in" Thank you so much. Happy marriage Anniversy MRS YUSUF INUWA."
Haka ya faɗa ya na kamkame ni kamar sanda haka na tsaya masa, illa hannuna na dama da na saka kaɗan na dan rike shi kaɗan na ƙosa ya sake ni sai na fara mutsu mutsu shi ya sa ya sake ni amma sai ya sumbace ni a kumatuna sannan ya bi ni da kallo kafin ya ce" Thank you for coming in to my life Halima."
Yaƙe kawai na yi domin ni kalamansa ba sa wani shiga ta. Su Jidda na kallah suna ta cin nama da cin cin ita da dai Baby duk ta yi dama dama da Cake jin na ce ina jin barci sai ya ce na je na kwanta shi in sun gama shi da yara zai gyara wajen sannan ya zo ya same ni kaina na gyaɗa masa kamar akan ƙaya na ke na yi saurin barin musu falo ina ji a jikina ya bini da kallo ni dai na fita na jawo musu kofa ba tare da na juyo ba.
 Ƙaran ƙofar dai dai da sauke ajiyar zuciyarsa. Komawa ya yi ya zauna ya na jin zuciyarsa na rawa. Gabaɗaya yau sai ya ji ya kasa mallakan kansa. Ya kasa yin wata jarumta yau sai ya ke jin kamar ba Namiji ba duk da haramci ya yi ba amma yau ya fahimci abin da ake kira kunya da nauyin Sadiya sun gama lulluɓe rayuwarsa. Har ga Allah bai taɓa hango rayuwarsa ta yanzu a kusa ba. Ya ɗauka in zai ƙara aure da amincewar Sadiya da yardanta bai taɓa tunanin kaddara za ta juyo masa ta wannan fannin ba. Ya na tsoro ya na tsoro tsoron kar Sadiya ta ji labarin auransa a bakin wani ba abakin sa ba. Ya daɗe a kofar gida a cikin mota amma ya kasa shigowa ciki ya rasa jarunmta da karfin gwiwan da zai iya haɗa ido da Sadiya bayan kuma yau ya munafunceta ya yi aure ba tare da saninta ba. NENE ce ita ce ta sha gabansa kuma ita ɗin Nene Uwa ce a gare shi da ba zai iya mata musu ko saɓa umarninta ba amma gabaɗaya yau yini ya yi jikinsa ya yi wani irin sanyin. Sanyin da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba.
Ya na zaune su Jidda na ta bidirinsu amma ya kasa cewa komai. Har Naman da kazan su kaɗai suka ci shi ya kasa in zai tuna tun abincin da ya ci jiya da daddare ne bai ƙara saka wani abu a cikinsa ba sai ɗan wannan cake ɗin kuma a yadda ya ke jin cikinsa ya toshe ba zai iya cin wani abu ba.
Wayarsa ce da ke cikin aljihun gaban rigar shi ta yi É—an kara alamun shigowar sako sai ya yi saurin É—aukowa ya duba. Musbahu ne.
"Yaya Tafida sun sallama Shagon nan fa. A kan dai yadda kuka yi mgana. Ga ma key din sun ba ni a hannuna."