← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 89

Sashe 64

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce masa na sha ya na wani taɓa goshina da wuyana ni ko burgeni bai yi ba na ce masa barci na ke so na yi, na san in na tashi kaina zai daina sara min sai ya fice ya na mai rufomin ƙofa na raka shi da harara, ko washegari a dakune na tashi daga shi matar tashi na riƙa yi musu yatsina ai shima sai ya sha jinin jikinsa ya san halina da na fara haka to ya san an ɓata min rai ne sai ya kiyaye ne da wata mgana sai da ni da kaina na ba ma kaina haƙuri na sauko gabaɗaya.

****

Kimanin satin Gimbiya uku a tare damu. Ta warke garas ba wata matsala muna kuma zaune lafiya ba abin da ya taɓa faruwa tsakanimmu amma fa ina ganin bariki domin tun da ta ji sauƙi ta fara shan gayu ana ma miji kwalliya da karairaya, da daddare kuma su shige ciki suna shagalinsu ni kuma ina nan ina musu wahala, duk ina gani fa amma na nuna ban gani ba, ni abin da ya ke ba ni mamaki shi ne Yallaɓai har zai iya tsawon sati biyu bai neme ni ba amma kuma bai damu ba, ni fa a da na ɗauka Yallabai ba zai iya kwana biyu ba ni ba sai ga shi ya wuce tunanina ko a jikinsa. An ce ciki ya samu rauni bedrest ta ke yi amma suna ɓarnan ruwa ni na sani kuma suna sun sam ni ba yarinya ba ce ba su isa su yi min wayau ba. Na faɗa ma zuciyata Yallaɓai ma ya daina ba ni mamaki, domin ko ajikinsa ya na cin amarcin sa, tun da ga boyi boyi sun samu a gida na dai lallashi kaina tun da sati biyar ne in ya cika ta koma gidan ta, ban ji ba kuma ban gani ba saboda haka can su ƙarata.

Yau ta kama laraba ne, Gimbiya da Yallaɓai sun je asibiti bayan sun dawo ya kawo ta gida shi ya fita muna falo muna hira ta tashi ta shiga ciki shigan ta ba dafewa sai na ji ana buga get ina zuwa na buɗe sai na ga Inna Mariya ce ban yi mamakin ganin ta ba saboda daman shekaranjiya mun yi waya za ta aiko min da wani mganin gargajiya na sanyi wanda ke wanko mahaifa. Aneesa ɗiyarta ta yi aure shekaru bakwai ba haihuwa shi ta karɓo mata ta yi amfani da shi ga shi yanzu ta haihu shi ne da na ji na ce ina so. Mun yi waya za ta karɓo min amma ban ɗauka za ta zo da kanta ta kawo min ba.

Muka shigo cikin gida tare ina mata sannu da zuwa na kawo mata ruwa da lemo. Lokacin sha biyu ta gota anan falon yara muka zauna ta fito min da mgamin ta na nuna min.
Akwai wanda zan sha da koko akwai kuma na ruwa har da na cin a abinci.
Ta ɗauko ƙullin mganin ta na nuna min ta na kuma faɗa min magungunar arraɓi ne a ciki haɗe haɗen ganyeyyeki, shi zan rika sha a koko ta ɗauko ɗayan ta na faɗin.

"Wannan kuma a ruwa za ki saka. Ina mai tabbatar miki in sha Allahu za a da ce."

Ni ban san Gimbiya ta fito ba, da ya ke muna falon yara ne ashe ta daɗe a tsaye ta na kallon mu sai Inna Mariya ce ta ganta sai ta yi min mgana a hankali ta na cewa bakuwa na yi? Sai na juya na ga Gimbiya ganin na ganta ya sa ta ƙariso abin da ya ba ni mamaki ganin ta na ta kallon magunguna da Inna Mariya ta kawo min ni kuma har ga Allah ban kawo komai ba sai na gabatar musu da juna.

"Inna ta ce ƙanwar Mama. "

Na faÉ—a ina kallon Gimbiya nan da nan ta rankwafa ta na gaishe ta.

"Abokiyar zama na ne, ba ta jin daÉ—i ne sai ta zo ta na zaune damu na wani lokaci."

Na faÉ—a ma Inna Mariya itama cikin fara'a ta amsa mata gaisuwa ta yi mata ya jiki.

"Bari na shiga ciki tunda kin yi da baƙuwa"

Sai na amsa mata sai bayan wucewarta ne Inna Mariya ta ce min" Ke Sadiya na ga ta na ta mana wani kallo ne?
"Ba ta da wata matsala Inna"
Sai ta jinjina kai kafin ta ce Allah ya sa ba ta wani daɗe ba na yi na yi ma ta tsaya ta yi sallar azahar ta ce min daga wajen karɓo min mganin ta wuto gidana ba za ta zauna ba, har haraba na rakata na ba ta kuɗin mota da kuɗin mganin da ta karɓo min ta ce 5k ne gabaɗaya mun yi sallama na dawo cikin gida na tattara mganin nawa na kai kabinet ɗin kitchen na ajiye na daga nan tiolet na shiga zan kama ruwa sai na ga jini yanzo min yanzu in zan yi al'ada ko ciwon mara ba na ji sai dai na gan shi cikin salama ba kamar baya ba, da sai ya yi watanni bai zo ba kuma bayan ya zo ya yi ta min wasa.

Kawai sai na wanke fuskata na fito. Ban san abin da ya faru ranar Gimbiya ba ta sakar min fuska ba da na ma shiga duba ta a daƙile ta amsa min tun da na ga haka na kama kaina. Abinci ma da na shiga na ce ko na zubo mata ne sai cewa ta yi ta ƙoshi. Ni dai na ga ban yi mata wani abu ba amma duk da haka na yi mata uziri saboda ta na da ciki daman a san yanayin masu ciki sai a hankali shi ya sa ban saka komai a cikin raina ba. Na cigaba da harkan gaba na.

Kwana biyu tsakani ranar asabar kenan Jidda ce kaɗai ta je tahfez Baby na gida ba ta jin daɗi. Awara na saka aka yo mana daga gidan su Saude to ba a kawo mana ba sai na tambayi Gimbiya me za ta ci na dafa mata? Sai ta ce fanten wake haka na miƙe na dafa mata fentan waken nan na zuba na kai mata, Saude ma na gidan ta kawo min awarar ni da Baby tun ya na ɗanyen shi na mu ke ci na fara suyan kenan sai na ji ƙara daga ɗakin Gimbiya kamar ta na kiran sunana, saboda sauri har ina wurgar da ludayin hannuna mai ya na zubar min a kafa amma ban ji zafi ba ni da Saude da Baby muka iske Gimbiya a jigace a bakin tiolet ta na ce min maranta na ciwo sannan kuma ta ga jini hankalina ya tashi na koma ɗaki da gudu na kira Yallaɓai a waya bai ɗauka ba sai kawai na ce Saude ta fita ta taro mana adaidaita mu je asibiti.

Ni na taimaka mata ta saka Hijabi da takalmi ni Baby ce ma ta rarumomin hijabin Jidda na saka kafata da silaf ɗin tsakar gida, muka tafi asibiti Saude ta rufe mana gidan gabaɗaya muka tafi asibitin da ta kwanta da farko na kaita ina zuwa aka amsheta suka shiga da ita saboda ruɗewa ban ɗauko waya ta ba sannan ban ɗauko kuɗi ba sai da na fita haraban asibitin na ari wayar wata Nurse na saka lambar Yallaɓai na kira shi sai lokacin ya ɗauka hankalina tashe na faɗa masa ga halin da ake ciki ya ce muna wani asibti ne na faɗa masa ya ce ga shi nan zuwa.

Shi ya fara zuwa kuma har lokacin likitoci ba su ce komai ba, shi ya kira Anty Bahijja ya faɗa mata ita kuma ta yaɗa ma Dangi Yadda Yallaɓai ya ga na ɗaga hankalina sai na bashi tausayina shi ya koma ya na lallashina da cewa ba abin da zai faru, a gigice Anty Bahijja ta zo asibitin kuma ta na nan aka kira Yallaɓai ofishin likita sai ta bishi ni ban san me ya faru a ciki ba ta dai fito ta na ta faɗan mganganu.

"Ni fa shi ya sa tun farko ban so Gimbiya ta je gidan Sadiya ta zauna ba. Saboda ba kamar gida wajen Nene ba. Yanzu to ga shi nan an ce ta ci wani abu da cikinta ba ya so ta kusa yin ɓarin cikin jikinta."

"Duk fa ba wata matsala ba ce. Tunda dai cikin na lafiya itama tana lafiya ai shikenan ko?

Amma ba ta bar mganar ba, an kira ta a waya ta É—auka ta na surutu ni dai na yi zaune shuru kawai ban yi mgana ba.

"Sadiya me kika ba ma Gimbiya ta ci ya kusa saka ta ɓarin cikin ta?

Tambayar ta zo min a ba za ta na ma kasa mgana, sai kawai na kalleta ma juya ina kallon Yallaɓai cikin rawan baki na ce" Ni ko me zan ba ta? Awara na saka aka yi mana yau shi ne ita Gimbiyar ta ce na dafa mata fenten wake kuma ai na saba dafa mata ta ci kuma ba a taɓa samun matsala ba."

"Uhm Allah ya iya faten waken ne?

Sai na ji raina ya ɓaci a fusace na miƙe ina faɗin" Me kike nufi da mganar ki?
Ta ta so ta yi min mgana Yallabai ya tare ta da cewa" Don Allah Bahijja ki bar wannan mganar. Yau Daugther ke zaune da Sadiya? Kuma duk a baya komai bai faru ba sai yau?
Za ta yi mgana ya sake tare da cewa ba ya son wata mgana kuma kar ya ƙara jin ta ƙara min wata tambaya ganin ya harzuƙa sai ta yi shuru ni kuma na koma na zauna ina tunanin manufar Anty Bahijja ko ta na zargina da ni ce na ba ta wani abu ta ci da ya sa ta shiga wannan halin?
Lalle ne ma matar nan, ganin Yallaɓai ya tare mgamar ya sa nima na yi shuru, sai Allah ya sa ma Gimbiya ta farka lafiya cikin ma bai fita ba amma dai likita ya ce ya na cikin risk sai an kiyaye.
Chapter 64 · 0% Book details