← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 89

Sashe 33

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe tara da rabi na dare sai ga Yallaɓai ya dawo shi kaɗai ya ce min ya ba ro su Tariq a gidan mai za su saka mai amotar shi kuma sai ya hau adai daita ya taho gida ya yi wanka ya shirya kafin lokacin sun taho sai su raka shi can gidan Gimbiyar.
  Kamar ya sani bai ko neme ni na haɗa masa ruwan wanka ba, ba domin in ya ce na yi ba zan yi ba sai domin zuciyata a lokacin ba ta cikin sukuni, muna gama maganar nan da shi ya shiga wanka ni kuma sai na koma can falo wajen su Rahila ba na so na zauna ni kaɗai tunani da damuwa su taru su ƙara ruguza ɗan sauran kuzarina.

Duk hiran da suke yi na kasa saka musu baki, zaune kawai na ke kamar mutum da mutumu ba na ma fahimtar hiran da suke yi, tun da ni nawa tunanin ya yi zurfin tunanin yau fa Yallaɓai ba anan zai kwana ba, yau ɗin wata rana ne da zai je ya kwana da wata mace ba ni ba, tuna haka kawai in na yi sai na ji numfashina ya sarƙe. Zuciyata na harbawa da sauri sauri ina dai zaune ne ina wasa da yatsun hannuna amma ni kaɗai na san halin da gangan jikina da zuciyata ke ciki, amma ban bari na shagala ba, sai na fara kiran sunan Allah a acikin raina domin na samu natsuwa.

  Haka kawai na ji ba na son komawa cikin bedroom ɗin mu, tun da Yallaɓai a yanzu na san ya fito wanka ya na shiryawa. Tun da aka faro wannan al'amarin ban bari Yallaɓai ya ga gazawata ba. In ko na bari ya gani yanzu kamar na yi faɗuwar baƙar tasa ne, shi ya sa da na koma na gan shi raina ya sosa hankalina ya tashi gwara na yi zama na a nan cikin ƴan'uwana a ƙalla dai ko ba na da natsuwar fahimtar hiran su ina kallon fuskokinsu za su iya zame min garkuwa daga bayyana raunina a wannan daren.

Ina nan zaune shuru sai ga Sameena ta fito daga ɗaki har sannu da su Amina suka yi ta mata wallahi ni ban ma ji ba, sai da ta zo kusa da ni ta na taɓa kafaɗata sannan na dawo duniyar da suke, kallona ta yi sai ta ga kamar ina firgice ne, sai ta zagayo kusa da ni ta zauna ta na faɗin" Matar Baba lafiya?

"Ya jikin ki! Sannu"

Na katse wancan tambayan na ta, sai ta amsa min da ta ji sauƙi, daga ni har ita sai muka rasa abin cewa, ni kam ba na rasa ba ne yanayin da na ke ciki ne ya sa kalaman bakina suka ƙare, Faridan Tariq daman ta na ɗakin su Jidda ta je kwantar da su Hassan sai ga ta fito ta na faɗin ga su Tariq can a waje ya ce suna kiran wayar Tafida ba ta shiga suna jiran shi a ƙofar gida.

  Lokacin da ta faɗi haka sai gabaɗaya jikina ya fara rawa har Sameena da ke gefena sai da ta fahimci haka, da sauri ta saka hannu ta riƙe hannuna guda ɗaya sai na juya ina kallonta da idanuwana da na ji kamar sun juye, kai ta girgiza min kawai sai na bi ta da kallo domin kamar wata yarinya sai na kasa fahimtar ta, bakina na ji ya bushe na kasa ma haɗiye miyau, maƙogaro na kuma na wani irin zafi kamar wani abu ya karce ni ban sani ba.

"Sadiya ki faɗa ma Yallaɓai suna jiran shi a ƙofar gida."

Farida ta faÉ—a ta na kallona sai kawai na bi ta da kallo itama kamar irin ban fahimta ba, kuma dukkansu sai suka kasa gane yanayin da na ke ciki, illa Sameena da ke gefena da ta yi saurin cewa" Ta shi Matar Baba."
Ta faɗa ta na kallona, lokaci ɗaya ta na ɗan bubbuga hannuna alamun lallashi da ban baki, ina ƙokarin ƙwato numfashina ne na ji muryan Yallaɓai ta korido ya na kiran sunana.

"Sadiya."

"Sadiya.."

"To ai ga Yallaɓan ma can ya na kiran ki Ya Sadiya."

Amina ta faɗa ta na kallona kamar an ja ni tsaye sai ganina na yi na miƙe kan kafafuna duk yadda na so na yi musu mirmishi na kasa illa kaina da na kaɗa ina faɗin" Ba. ba ri na yi masa mgana."
Ina gama faɗin haka na juya zan wuce ban ko kallon gabana sai gashi na ci tuntuɓe da cafet na kusa faɗuwa gabaɗaya suka haɗa baki wajen faɗin" Subhanallah."

  Na kusa kaiwa kasa na samu na riƙe kujera ban riga na kai ƙasan ba, jikina ba in da ba ya rawa sai kawai na wuce ina tafiya ina ji kamar ina jin sanyi zazzaɓi zai kamani domin ina ta matse jikina a waje ɗaya, da kallo suka bi ni, saboda sai a lokacin dukkansu suka kula da yanayina sai kuma jikinsu ya yi sanyi ina jin Farida daga bayana ta na faɗin" Ki yi a hankali Sadiya kar ki faɗi." Cikin muryan sanyi kamar na tausayi haka na ji a cikin maganarta.

Ina gama shigewa koridon Sameena ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Allah ya ƙara ma Matar Baba haƙuri da juriya." Faridan Tariq sai ta koma ta zauna a gefen kujera ta na faɗin"Amin. Amma lamarin ba daɗi."
Rahila dai da Amina ba su yi magana ba, amma jikin su duk ya yi sanyi sai falon ya koma ya yi shuru hiran ma sai ta tsaya kowa da tunanin da ya ke yi shi da zuciyarsa.

Ni kuma ina fita daga koridon na buɗe kofa na tsaya a ƙofar bedroom ɗin na kasa shiga, dafe kirjina na yi jin kamar zuciya ta za ta faso ta fito saboda yanayin da na ke ciki, duƙawa na yi ina maida numfashi sama sama kamar wacce ta yi gudun tsere ji na ke yi kamar sheɗata na neman ɗaukewa na ma kasa iya dai daita yanayina ballatana har na tura ƙofa na shiga ɗakin, ina duƙen ban sani ba sai kawai na ji an buɗe kofa Yallaɓai ya bayyana a gabana. Kaina na dago ina duke kan gwiwoyiyina na ɗago ina kallon shi, na ga lokacin da ya ɗan buɗe ido cikin mamakin ganina a wajen, ni kuma kayan jikinsa na ke kallo wata shadda ce sabuwa ce mai ruwan sararin samaniya ɗinkin zamani ne, har saman kaina na ke jin ƙamshin turaran Yallaɓai har kafarsa sabon takalmi ne domin ni ban ma san ya siya takalmi sabo ba, kamar wani cuta ina ganin Yallaɓai sai na ji kawai ina haƙi, daga tsuggune kamar ina ganin hajijiya ne ma.

"Sadiya lafiya? Me kike yi anan?

Ya faɗa yana kallona yana ƙokarin shima ya duka shima da sauri na yi ƙoƙarin na miƙe kawai sai na ji juwwa ta ɗauke ni na yi baya zan faɗi da hanzari Yallaɓai ya taro ni, nima sai gani na ƙamƙame hannayensa ina cigaba da haki kamar mai cutar Asthma saboda na ɗauka zan faɗi ne, ni fa gabaɗaya ji na ke yi kamar wata cuta ta kamani, kuma irin cutar da ban taɓa samun kaina a cikin sa ba, ina tunanin cutar yau ce ta kamani.

"Ba ki da lafiya ne?

"Subhanallah."

Na ji yo Yallaɓai na faɗa Sama sama ni dai ban dawo hayyacina ba sai da na ganni zaune a gefen gado, kitchen ya koma ya ɗauko min ruwa mai ɗan sanyi ya buɗe min ya kuma kafa min a baki ya ce na sha. Na ɗauka ban ji ƙishi sai ga shi na ɗaga roban ruwa na dire bakomai a ciki shi kan shi Yallaɓai da mamaki ya ke kallona Allah ya taimake ni sai na fara dawowa hayyacina na ji numfashina na daidaita sannan na daina hakin nan, kuma bakina bai bushe ba yanzu sannan ina jin maƙogwarona ya daina kartamin ɗin da ya ke yi ɗazu.

  "Sadiya."

Yallaɓai ya faɗa yana durƙushe a gabana lokaci ɗaya kuma ya na kallona sai na ɗago ina kallon shi, yadda kuka san na gaji haka na ke jin duk jikina ya yi sanyi kamar an yi min dukan tsiya. Fuskata ya saka hannu ya na shafawa har ya na ɗan tapping ɗin shi da hannun shi sai na ƙara buɗe idanuwana ina kallon shi amma ban yi magana ba.

"Me ke damun ki?

Haka ya faɗa cikin kulawa, a cikin zuciyata na ke maimaita Hasbunallahi wa'imal wakel. Sai kuma na ji nauyin jikina ya ragu sannan bakina ya saki numfashina ya dai daita, Yallaɓai ya tashi tsaye ya saka hannunsa guda biyu ya ɗago duka kafaɗuna tsaye lokaci ɗaya ya sakani a jikinsa ya rumgumeni ƙamƙam a cikin jikinsa nima ban san lokacin da na miƙa hannuwana na zagaye bayan shi na shige jikinsa sosai kamar zan tsaga jikinsa na koma ciki, shi kan shi ya ji yanayin riƙon da na yi masa duk yadda na so kar kuka ya zo min duk yadda na so kada yau ɗin nan na raunana sai da raunin zuciyata ya rinjayeni sai kawai ji na yi ina kuka har da shessheƙa, hawayena suna sauka a saman kafaɗan shi, ko bai faɗa min ba ni na san jikin Yallaɓai ya yi sanyi, domin kansa na saman kafaɗata kawai ya na riƙe da ni amma ya kasa iya mgana ni kuma ina ta kuka yi yi har da kamar zan shiɗe, kuma in za a kashe ne ba zan iya cewa ga dalilin kukana ba kawai ni dai a raina ji na ke yi kamar na fi kowa na duniya nan shiga matsala, kuma ina ji kamar Yallaɓai zai yi min nisan da tun da muka yi aure bai taɓa min irin shi ba.
Chapter 33 · 0% Book details