← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 89

Sashe 30

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falon Yallaɓai na shige ina waya. Ya ce min Laila ta shigo gari amma sun yi mgana ita da yara sai gobe za ta zo gidana na ce bakomai ai itama biki gare su. Mun yi shuru na wani lokaci Ya Auwal ya san ni da hira da mgana amma yau gabaɗaya na yi sanyi. Tunani na ke ni ba uwa ba, ba kakanni baa dukan ya yi mini yawa. Aka ce ɗan uwa rabin jiki ko da ya ke namiji ya fahimci ina cikin damuwa sai na ji ya kira sunana a hankali.

"Sadiya."

Na amsa da Na'am ina É—aga idanuwana sama domin sai na ji kamar zan fashe masa da kuka.

"Ba ki bukatar wani abu?

"Ba na bukatar komai Ya Auwal kiran ka mean alot to me. Na gode"
Na faɗa muryata na rawa sai kawai ya ce" Ko Yallaɓan ya yi miki wani abu ne?.
Da sauri na ce" A'a ba abin da ya yi min Ya Auwal."
"Kin tabbata?
Sai na gyaÉ—a masa kai kamar ya na ganina ina ta share kwalla da gefen rigana

"E. Bakomai."

Na amsa masa cikin muryan kuka.

"To shike nan zan saka miki 50k ki kara wani abun kin ji ko?

Kamar daman ina jira ne kawai sai na fashe da kuka cikin kukan na ke faɗa min" Na gode Ya Auwal. Allah ya kara ma nema albarka Allah ya ra ya maka zuru'a. Ita kuma Mama Allah ya jiƙan ta da Rahama."
Kamar mutuwar ce ta dawo min sabuwa kawai sai na ƙara volume ɗin kukana ya na ma lallashina da min mgana ba na jinsa har ya kashe wayarsa ni kuma sai na sulale a ƙasan kujera ina ta kuka ina cikin kukan nan Jidda ta zo ta ganni hankali tashe ta je ta kira su Rahila suka taho da gudu ganin yadda na saka kaina acikin gwiyoyina ina ta kuka mai sauti sai tausayina ya kama su Rahila da Amina suka rumgumeni suna lallashina Ya Aina ta kori yaran can falo domin sun tsaya akan mu suna ta kallo Jidda duk ta damu sai faman faɗi ta ke yi.

"Umma ko ba ki da lafiya ne?

Baby ko har ta fara kuka da Rigima sai Marwa ta bi su can falon su ta na lallashin su, Ya Aina ta tsaya a kaina ta na faɗin"Me ye haka Sadiya? Har na saka miki suna jarumtar mata kuma sai ki ba ni kunya! Don Allah tashi ki bar kukan nan ki yi haƙuri ki ƙara daurewa da ikon Allah alheri ne za ki yi ta gani in sha Allahu."
Amma na kasa iya yin wannan jarumtar kamar ana tunkuÉ—o kukan daga cikin zuciyata ya na zuwa ta bakina.

Ya Balki kuma cewa ta yi" Ku bar ta don Allah ta yi kukan ta ko za ta samu sauƙin zuciya."
Rahila da saurin kuka har ta fara tayani hawaye.
Ni kuma ganin sun damu ya sa na ɗago ina faɗin" Ni fa ba kukan auren Yallaɓai na ke yi ba. Ina kuka ne na tuna da Mama ne."

"Allah ya jikanta da Rahama."

Suka haɗa baki gabaɗayansu wajen amsawa da Amin bayan kuma sun yi addu'a Amina sai ta fara kuka sai kawai ta tashi ta bar falon tana sharen ƙwalla ganin na ki daina kuka ya sa Yaya Aina ta kira Gwaggo a waya ta faɗa mata ba zato kawai Alhajinmu na gefe ya karɓe wayar ya kuma ce ma Ya Aina ta ba ni wayar zai yi mgana dashi.

Sai na yi saurin tsaida kuka na ina gaishe da Alhajinmu.
Cikin yanayin maganarsa ya ce" Dubu in na ce ki zo gida yanzu ina son ganin ki, za ki iya zuwa?
Muryata a shake na ce masa in sha Allahu, shi kuma sai ya ce na taho yanzu ya na jirana, bayan na bama Ya Aina wayar sai ta ce ko ta rakoni ne, amma Alhajimu ya ce ni kaÉ—ai ya ke son gani. Jin haka yasa na tashi na shiga ciki ina shiryawa ina cikin ne sai ga Faridan Tariq da Sameena da Hauwa sun shigo gidan ina ta jin hayaniya sai da na sako hijabi da takalmi bayan na dauko wayata da kuÉ—i na fito na gansu, muka rumgume da Sameena, Farida kuma muka gaisa cikin fara'a sai ta yi min mgana ko ban jin daÉ—i ne ta ga idona duk ya ta sa ga muryata a shake.

"Mura na ke yi kaÉ—am."

Na ba ma Farida amsa daga Walima suke domin ga kayan waliman nan sun taho da shi.
Hauwa na kallah kafin na ce" Hauwa zan je ÆŠorayi Alhajinmu na son ganina."
Tare suka haɗa baki wajen tambayan lafiya na ce lafiya ƙalau, kafin na wuce sai da na gaya musu gidan Munnira za a yi waina gobe sai Hauwa ta ce Mutaƙƙa zai zo ya ɗauke ta da safe sai ta fara sauka a gidan Munnira in sun gama sai su taho da shi Sameena ma ta ce A Gwammaja za ta kwana amma da safen za ta je can gidan Munnira su yi aikin tare Farida dai nan za ta kwana ita zan dawo na same ta, Ya Balki da Ya Aina sun ce gida za su ta fi sai zuwa gobe, nan muka yi sallama Hauwa kuma har waje ta rako ni muka taka har bakin titi na samu abun hawa shi ne ta ke faɗa min ta ga yar uwata Ma'u da ƙawarta a wajen Walima su ne gaba gaba

"Allah ya kyauta."

Shi ne abin da na ce kawai saboda Ma'u daman ni na san duk in da za ta ga gazawata can ta ke sha'awa sai ta yi ta yi dadin abun ma itama kishiyar gare ta, kuma ba fata na ke yi mata ba Alhajin nan na ta sai ya ƙara aure ba kuma domin ina yi mata fata ba, na san zafin kishi ba zan taɓa fatan ko maƙiyina a yi masa kishiya ba. Sai da na kusa ma isa Ɗorayi sannan na tura ma Yallaɓai saƙon na taho Ɗorayi Alhajinmu na kirana ina gama tura masa saƙon na maida wayata cikin ƙaramar jakata. Ko da na shiga gida an ta salla isha'i a masallatai Alhajinmu ya tafi masallaci shi da Datti ashe ɗazu ya dawo garin.

Nima alwalan na yi na gabatar da salla, Gwaggo ma haka bayan mun idar itama ta yi ta min nasiha ta fi jadaddamin na yi hakuri na zauna da abokiyar zama ta lafiya na kuma zauna da ita da zuciya É—aya in ma ta na da wata manufan Allah zai maida mata kayanta. Ta na cikin yi min nasihan ne sai ga Alhajinmu ya shigo ya na jin mu a cikin É—akin Gwaggo da kanshi ya shigo nan, ita kuma Gwaggo ta fita ta bamu wuri.
Kalaman da Alhajinmu ya yi amfani da su wajen yi mini nasiha ko na ce tunatarwa su suka haɗe min da gyambon zuciyata na yi ta kuka ina shessheƙa.
Alhajinmu ya hore ni da abubuwa masu yawa masu girman ciki shi ne na yi hakuri na yi haƙuri na yi hakuri wata rana zan ci riba.

Alhajimmu ya kalleni ya kira sunana.
"Dubu"
Na ɗago fuskata ina kuka ga hawaye shaɓe shabe na amsa da "Na'am Alhajinmu."
Sai kawai ya gyara zama ya na faɗin" Ki saka a ranki abokiyar zama alheri ce. Ba ri na ba ki misali da mahaifiyarki lokacin da na faɗa ma Maimuna ga ta nan Gwaggon ku zan ƙara aure, duk da zafin kishi irin na mata ba ta nuna min ba, nan ta ke ta yi addu'an Allah ya sa mu riba ci junan mu da alheri dukkan wani sharri Allah ya tsare mu matsayinta na babba ta yi haƙuri kuma ta ci riba kina gani a cikin gidan nan ba su taba faɗa ba, ba wai kuma ba sa kishi ba ne a'a suna yi amma cikin ilimi da tarbiya. Har Rukayya ta koma ga Allah Gwaggonku da ni kaina Alherin ta muke faɗa kuma har gobe ba za mu daina tuna ta muna kuka ba. Bayan ba ta a duniya Maimuna ita ce uwa a gare ku ta taɓa nuna muku bambamci da su Murjanatu?
Ina kuka ina girgiza ma Alhajinmu kai, shi kuma sai ya cigaba da faɗin" To kin ga falalar alherin da ke cikin abokiyar zama. Ni ma ki saka misali a kaina Dubu. Mahaifiyarmu ta rasu ni da babarku Hasiya ta bar mu hannun Hajiya Allah ya jikanta itace ta zame mana uwar da har ta koma ga Allah muna alfahari da ita. Shin Hajiya kafin ta rasu ta taɓa nuna bambamci tsakanina da su Aminu? Ko ku ta taɓa nuna muku bambamci tsakanim ku da su Muntari? Duka ɗaya ne a wajenta to shima ya na daga cikin misalin alherin abokiyar zama saboda haka ya ke ƴa ta Halimatu mai babba suna ki yi gadom mai sunan ki yi rangwame ga haƙurin ki, ki danne zuciyarki ki yi fatan alheri a cikin wannan auran na mijinki, ko da rana ɗaya kar ki bari sheɗan ya saka miki sharri a kanta. Ki yi ƙoƙarin azaman da zai gudana a tsakaninku kar ki taɓa cutar da ita, in ita ta zo da niyar cuta Ubangiji da zuciya ya ke amfani sai ki ga ya yi miki sakayya. Ki daina kuka ina da kyakyawan yaƙini a kan Yusufa zai zama adalin namiji a gare ku, kuma zai yi muku adalci dai dai gwargwardo. Saboda haka ki rike girmanki ki yi ma Ubangiji godiya, in wani abu ya taso miki acikin zuciya ki kira sunan Allah, in kuma kin tuna da mahaifiyarki ki yi mata addu'a amma ki daina kuka, ki na damu kina da sauran ƴan'uwanki kina da mijinki da ƴaƴanki to ki ɗauka Ubangiji ya gama yi miki dukkan Ni'ima."
Chapter 30 · 0% Book details