Sashe 66
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ni ko na ce ita mijinta da yan'uwansa da ta shanye su sai abin da ta ce itama kenan gaban na na ta ta wanke ta ba shi ya sha kenan.?
Sai ta fara haƙilon faɗin" Ai mu kowa ya san zuru'ar mu ba mu da tambarin bin bokaye kuma ba a ji labarin wata cikin ahalin ta mutu cikin hauka ba."
Har ta na cewa na yi shige shige na na haɗa Kawu Abba da ɗiyar yayata saboda shima a shanye shi sai yadda aka ga dama dashi to na rubuta na ijiye ko ta ce bokan mu ya yi ƙarya Abba ba zai auri dangin masu asiri ba har ta na faɗin me aurena ya tsinana ma Tafida? Ni kuma na ce in ba ta saka ya sake ni ba, to ba ta haifu ba.
"Kuma dangin asirin su Kawu Abba ya gani ya ce ya na so in Allah ya haÉ—a ki raba in kin isa "
"Mata kin bi kwazzaba ma rayuwata a gidan aurene? Me na tsare miki? Zaman ki na ke yi! Ke da kika miƙe kafa a gidan na ki mijin wa ya takura miki? Ko kema shige shigen kike yi? Ke ki ce kina son ki ji daɗi a gidan wani da zuru'an wani amma kuma ke ce wata ba za ta zo na ku zuru'an ta ji daɗi ba? Ashe haka kike da son kan ki? To wallahi kin kure ni akan matakin da ba zan ɗauka ba tun da kin fito ta haka to nima zan fito miki ta bangaren da kika fito min ni da ke shege ka fasa Bahijja"
"Sadiya ba ki da kunya? Bahijja ba yayar mijin ki ba ce?
Anty Maimuna ke tare ni da faÉ—in haka har ta na shan gaba na, idanuwana sun rufe yadda bacin rai ke sarrafa zuciyata a wajen ko mari na ta yi sai na rama.
"Au ni ce ma ba ni da kunya daga ƙarshe kenan!? Ke ba ki ji duk mganganun da ta ke faɗa min ba ne! Me na yi mata? Kamar ta na jira. Ai ita ba ta kama girmanta na yayar mijina ba. Shi ya sa nima na bi girman nata na tattaka ni da ita wallahi sai mun cire renin da ke tsakanin juna."
Nene hankalinta ya tashi ta yi ta yi Bahijja ta yi shuru ba ta yi ba sai ta Umarci Maman farko da ta ja ni zuwa ɗakin ta tun da ita ma Bahijjan ta ƙi sauraranta har da Halima a masu jan Anty Bahijja amma ta na wani zillo ai nima na haukace musu ta na zagina ina zaginta itama.
Suwaiba da Maman farko da su Hauwa suka yi ta ja na Dakyar suka shiga dani ɗakin Maman farko na zame musu kamar mai aljanu sai da suka haɗa da rufe ƙofa Maman farko fadi ta ke yi" Innalillahi Sadiya ki yi shuru mana."
"Ku kira Tafida mana."
"Bari na kira shi"
Cewar Suwaiba ta na wucewa cikin uwar É—aki."
"Ki yi hakuri Sadiya."
In ji Munnira ta na kuka ganin na zaune saman cafet É—in tsakar É—akin Hajiya iya na rushe da kuka kamar wata yarinya.
"Kazafin fa suka yi min? Sun ci mutumcina ni da zuru'ata?
"Ki yi haƙuri amma tabbas an ci zarafin ki."
In ji Maman farko Hauwa kuma faÉ—i ta ke yi" To daga ina wannan mganar ta fara fitowa?
"Ko da ga ina ne ko waye wallahi ba zan bar wannan mganar ba sai hukuma ta ƙwatomin haƙƙin ƙazafin da suka yi min."
Na faɗa ina jin ƙuna a ƙasan raina lokaci ya yi da zan tauna tsakuwa domin a ya ta ji tsoro.
Ba Ma'u ba ko Baaba ce sai na yi kararta ba Bahijja ba ko Nene ce ta yi min wannan ƙazafin sai na ji dalilinta wallahi. Ina kuka zuciya ta na wani irin zafi ina ma jin turarin zafin daga maƙoshina. Duk alherin da na yi ma Gimbiya ni ce za ta saka ma da sharri. Lalle na yarda da maganar hausawa da suka ce mai kishiya ba ya mutuwar Allah. To an kawo gabar da komai zai ƙare, zan yi abin da hankalin kowa zai koma jikinsa.
Jikina ba in da ba ya rawa kawai hasko kaina na ke yi na kama Ma'u na yi mata shaƙan da sai ta kusa zuwa lahira. Kawai sai gani na na yi na mike Munnira da Hauwa da suke ta jajanta lamarin suka mike suma, ganin na nufi hanyar barin falon na Maman farko ya sa Munnira ta ce.
"Sadiya ina za ki je?
Maganarta ya dawo da hankalin Maman farko a kan mu saboda itama wayarta ce a hannu ta na dannawa kamar neman wani ta ke yi a wayar.
Kuma daga ma nan dakin muna jiyo hargagin Anty Bahijja da zage zagen da ta ke yi.
"Ina kuma za ki je?
Suwaiba ta faÉ—a ta na fitowa daga ciki.
"Jakata zan É—auko da mayafina "
Na faɗa muryata a shaƙe sai Maman farko ta ce ba zan fita ba Hauwa ta je ta ɗauko min,sai na yi shuru amma ban zauna ba ina tsaye ina karkaɗa jikina in ba sumar da Ma'u a yau ba, ina jin ba zan huce haushina ba kafin na haɗa da jami'an tsaro sai na bar mata taɓon da za ta kiyaye ni har gaban abada. Ko raba ɗayan biyu ba zan yi ba Ya Murja ta faɗa ma Ma'u maganar Marwa da Kawu ita kuma ta zo ta fesa ma uwarta ai kuma komai ya zo karshe daga yau zan kawo karshen makircinta a kaina.
Hauwa ta buÉ—e falon ta fita dai-dai lokacin da Maman farko ke faÉ—in" Kin samu Tafidan?
"E ya ce ga shi nan a kan hanya. Ya ma ce Halima ta kira shi ta faÉ—a masa ba ki ji yadda hankalin shi ya tashi ba na ce ya taho a hankali Sadiya ta na É—akin ki mun rufe ta."
"Wayyo bawan Allah."
Maman farko ta faɗa cikin wani yanayi ni dai ina tsaye kiƙam na kasa zama. Sai ga Hauwa da Hajiya jiya sun shigo, jakata kawai Hauwa ta dauko min da sauri na karɓa wayata na ciki da kuɗi lokacin biyu na rana har ta gota daman sai da na yi azahar na fito daga gida.
"Sadiya ki yi hakuri. Kai wannan lamarin bai yi daÉ—i ba"
In ji Hajiya Iya, Mama ko faÉ—i ta ke yi" Ni Bahijjan ce ta ba ni mamaki ko gaya mata abu aka yi ta yarda ba ta da shaida?
Suwaiba ta karɓe da faɗin" Ita ko ke da shaida ba ku ji suna faɗin Gimbiya ta ce ta ga ƙanwar Maman Sadiya ta kawon mata magani ba! Itama ai ta haɗa fitina ita da wacce ta tari Bahijja da mganar wani tarihin wata ta mutu da hauka."
"Ma'u ce tare suka tashi da Sadiya. Da babansu da ita mahaiyar Ma'u uban su É—aya uwar su É—aya'
Hauwa ta faÉ—a sannan ta kora musu jawabin ta in da suka haÉ—u da Anty Bahijja.
Hajiya iya na salati Maman farko na yi, Suwaiba ta ce" Na gane ta wata yar fara haka. Amma ko ta yi asara wallahi."
Hankalinsu ya ɗauke da hiran su ba su san na zari mayafin da na gani a saman kujeran hanyar fita ba, na buɗe kofa na fice ko takalmi babu a kafata sai wani da na gani a ƙofar ɗakin na saka. Karan rufe kofa ta suka ji sannan suka far ga ga na fita sai suka biyo ni da gudu suna kiran sunana sun ɗauka ɗakin Nene zan koma sai su ka ga na fara sauka daga Bene Suwaiba da su Hauwa suka biyo bayana suna kiran sunana amma kamar wata hajijiya haka na rika sauri kamar zan kifa a haraba na ci karo da Mimisco ta iso itama ina ga kiranta aka yi. Har ta na tsayawa ta ɗauka zan yi mata mgana ne sai ta ga na wuce ta fuu kamar zan kifa.
"Sadiya tsaya. Ki tsaya na ce Sadiya."
Ko sauraranta ban yi ba mayafi a saman kafaɗa ina rike da ƙaramar jakata na fice da sauri kamar zan faɗi. Ba san ni ba ko sun biyo ni ni dai ina fita na fara sauri ina haɗa hanya har da gudu gudu ina hango bakin titi kawai na ga Motar Yallaɓai ta sha wo kwanar, yadda na dumfari in da zuciyata ke son zuwa ko waye ya tsaida ni ba zan tsaya ba ko da Alhajin mu ne kuwa.
Ya wuce ni, ni ma na wuce shi da sauri sai ga shi ya na dawowa da baya da baya a motar ya na kiran sunana bayan ya sauke gilashi ko jin sa ban yi ba ganin ya tsaya da motar yasa na saka gudu ina zuwa bakin titi na saka hannu mai adaidaita na zuwa ba kowa a ciki ya tsaya na shiga ciki da sauri na ce.
"Mu je Rijiyar zaki. Ka yi gudu da ni sosai."