← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 89

Sashe 17

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ba tare da ta jira cewata ba ta fara gaya min yadda komai ya fara, ta in da aka hau da kuma ta in da aka sauka ta karishe da faɗin" Wallahi Allah ɗaya ne Tafida ya so na bashi ko kwana daya ne domin ya samu damar sanar da ke, ni kuma na ga duk ɗaya ne, ko ya sanar da ke kafin a ɗaura ko bayan an ɗaura tunda sai daga baya za a yi tariyan. A gabana kuma ya roƙi yan'uwansa da cewa su yi shuru da bakinsu ba ya so ki samu labari a bakin kowa sai daga bakin sa ba ki ga yadda ya ɗaga hankalinsa a jiyan da ya zo ya sameni ya na faɗa min ya haɗu da yayanki har ya yi masa murna sannan ya sanar masa ke kika faɗa masa. Ya damu ya ce ya na jin kunyar ki shi ya sa tun kwanaki ya kasa iya faɗa miki ba kuma domin don ya aikata haramci ba, a'a sai domin ke ɗin kina da daraja da ƙima a wajensa kina da mutumcin da ya ke tsoron ya sanar da ke labarin da zai ɗaga miki hankali, ya na jin kunya da nauyin faɗa miki ya yi aure ba tare da ya sanar da ke kafin auran ba. Yau da safe na kira shi ya sanar da ni bai faɗa miki ba sai na yi tunanin ya kasa shi ya sa ba tare da sanin kowa ba na ce Musbahu ya kawo ni domin ni na zaunar da ke na warware miki dukkan abin da ya faru na kuma ƙara tunatar da ke abubuwa ma su girman gaske da Ubangiji ya ba ki wanda nan gaba kar kishi ya rufe miki ido ki manta da su ko kuma ki kasa kallonsu a wani baiwa ko nasabar da Ubangiji ya ba ki Sadiya."

Nene na magana amma idanuwana sun cika da ƙwalla ina ƙoƙarin hana su zubowa a saman fuskata. To bayanin na menene! Ba ta saka shi ya auri ɗiyar ƙawarta ba to ni kuma me ta ke so ta faɗa min? Wannan fa shi ne an cuceka amma ana so a hana ka yin ihu da kuka, har ga Allah na ga baƙin Nene me ya sa ba za ta bari Yallaɓai ya yi mgana da ni kafin a ɗaura auren ba? Sai na ji zuciya ta sosu kuma a ganina ta yi min rashin adalci da za ta ce a yi min kishiya kai tsaye ba ta re da shiri ko tsammani ba."

Runtso idanuwana na yi, hawayen da na yi ta riƙewa suka zubomin shar! Duk Nene na kallona amma sai na kasa gefen hijabina ina sharewa a lokacin in za a tona zuciyata daga Uwar har ɗan duk haushin su na ke ji amma ina ƙoƙarin dannewa kuma a saman fuskata ina karyata abin da na ke ji a cikin zuciyata.

"Ki yi hakuri Sadiya. Ki yi hakuri."

Nene na bani haƙuri ina jin kamar ta na ƙara ma ciwo na barkonu ne, ina ta danne kuka na amma ina share hawaye ne wasu suna ƙara sauka kamar an buɗe famfo tun kuma da labarin auran nan ya zo min ko Yallaɓai ban taɓa zubar da hawayena a gabansa amma yau sai na ji na kasa iya wannan dauriyan ganin hawayen sun riga sun taho kai tsaye sai kawai na barsu suna ta zuba sharr, in suka kwaranya a saman fuskata har suna gangarowa a saman hijabin jikina, Idanuwana suna mai kallon zanen cafet ɗin da ke falon, ina jan hanci irin na masu kuka, so na ke yi na samu keɓewa ni kaɗai na fashe da kuka na yi birgima ko domin na ji sauƙi sauƙin abin da ke suka na acikin zuciyata.

  "Ki yi haƙuri Sadiya. Daure na san kishi. Na san kishi ya na da zafi Sadiya amma in aka yi haƙuri za a ci riba wata rana."

Kalamanta ya sa na kalleta, tabbas ta san kishi, ita da aka auro ma uku. Kenan itama ta san irin zafin da na ke ji a cikin zuciyata sai na ji na godema Allah a cikin raina ko banza za ta fahimci kwataƙwacin irin ɗacin da na ke ji a cikin zuciyata.
Kaina na ƙara maidawa ƙasa lokaci ɗaya ina share hawayen saman fuskata da gefen hijabin jikina muryata har ta fara chanzawa na ce.

"Bakomai Nene. Allah ya ba mu zaman lafiya da juna."

Ta amsa da Amin Amin cikin mirmishi kafin ta ce" Sadiya wallahi ban yi ma Tafida ta yi auran Saudatu domin na ga kin gazamin ba. Ko na ga shi kin gaza masa ba, sai dai kamar yadda na faɗa miki tsohon kuduri ne a zuciyarmu ni da Hajiya ina kuma son na cika shi kafin na bar duniya shi ya sa auran ya zo bagata tan. Amma wallahi Allah ɗaya kenan ba ki taɓa min wani abu cikin sanin ki ba ko ma kin yi min a cikin rashin sani na yafe miki na sha faɗa a gaban idon ki a kuma bayan idon ki bakomai a tsakanina da Matar Tafida sai mutumtawa da Darajawa saboda haka kar ki saka a ranki ko kin gaza ne, ko kuma na ware ki,  da ke da Tafida da Saudatu ɗaya kuke a wajena, ba bu bambamci a tsakaninku kamar yadda Saudatu ta ke ƴa a wajena kema ƴa ce domin iyayenki ranar da kika zama ɗaya daga cikinmu ni suka ba ma amanarki suka kuma ce min ni uwa ce a gare ki na yi miki gyara in kin yi kuskure tamkar yadda zan yi ma ƴaƴana na cikina ko kin manta Sadiya?

Kai na gyaɗa ai ba zan manta wannan ranar ba. Inna Mariya ce ta riƙa jadaddama Nene ƴa suka kawo mata ba suruka ba.
Kai na ƙara jinjinawa kafin na ce" Haka ne Nene."
Sai kuma na kalleta kafin na ce" Na gaza Nene. Na gaza wajen ba ki jikoki masu yawa daga tsatson Tafida kamar yadda kike so."
"Kul kar ƙi ƙara wannan mganar Sadiya. Ba ki gaza ba kin kuma biya ni domin kin haifa min takwara kin kuma haifa min ƴa. Ni ko me na ke nema a duniya da Allah bai ba ni ba? Allah na tuba ni jika wanne ne ba a haifa min ba Sadiya! Ki godema Allah kina da biyu wata ɗayan ma ba ta samu ba shi ta ke nema. Ki kuma gode ma da Allah da ya baki har biyu sai ki yi ma Allah butulci da cewa gazawa ce? Maza ki nemi gafaran Allah domin ya yi miki kyauta ba ki gode masa ki nemi gafaran shi ki gode masa sai ki ga ya ƙara miki da ni'imar da ta fi irin Ni'imar da ya baki a baya."

"Astagafurilla. Astagafrilla."

Haka na shiga furtawa da sauti, domin sai na ji tsoro kar na batulce ma Allah ya ƙi ƙara min wata haihuwar domin nan duniya ba ni da wani buri sai na ganin Allah ya sake ba ni haihuwa ko da guda ɗaya ne. Zuciyata har rawa ta ke yi in na yi hasashen ƴaƴa biyun da Allah ya ba ni wata rana in ya so zai iya ɗauke kayansa sai na ji jikina har ƙwaƙwalwata ya na amsawa cikin wani yanayi wanda ba ki ba zai iya misaltawa ba.

Nene ta ga yanayina ina ta rawan jiki sai ta ce na yi ta kiran sunan Allah har sai na samu natsuwa innalillahi na cigaba da maimaitawa a cikin zuciyata cikin ikon Allah sai ga shi na dawo cikin natsuwa Nene ta durkusa da kanta ta buɗe ruwa ta zubamin a kofi ta ba ni ta ce na sha da bismillah. Ban yi musu ba na karɓa na sha da yawa na miƙa mata kofin ta karɓa ta maida shi saman farantin sannan ta koma ta zauna ta na kallona ina ta sauke numfashi.
Sai da ta fahimci na samu natsuwa sannan ta shiga yi min nasiha mai ratsa jiki da cewa duk abin da na ga ya faru da bawa daga Ubangiji ne kuma duk abin da ya aikata dai dai ne shi ba ya kuskure, mu ƴan adam mu ke kuskure amma shi Ubangiji duk abin da ya yi a garemu mai kyau ne. Ta umarce da shawaran da daaina tunani na fauwalama Allah komai. Wataƙila jinkirin alheri ne nan gaba Ni'imar za ta fi ta baya yawa. Ina gyaɗa kaina cikin gamsuwa ina faɗin.

"Allah ya sa. Allah ya sa. Na gode Nene Allah ya saka da alheri"

Ta amsa da Amin kafin ta ce" Ina fatan kin fahimce ni. Sannan a mganganuna kin fahimci irin matsayin da kike da shi a zuciyar Tafida ko?
Sai na kalleta alamun bangane ba sai ta gyara zama kafin ta fara da kiran sunana.
"Sadiya ba ki fahimci irin martaban da ubangiji ya yi miki a acikin zuciyar mijin ki ba? To ko kin fahimta ba ki gane ba. Ni bari na warware miki irin taki baiwar da ubangiji ya yi miki ba ki sani ba."

"Sadiya."
Chapter 17 · 0% Book details