Sashe 83
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Hoto fa ya yi kyau ƙwarai."
"Wani hoto kuma?
Ya faɗa da sauri ya na kallona ni kuma sai na yi kamar ban gani ba na yi masa mirmishi na fita. Ku san ai ya san abin da ya aikata sai ga shi muna ƙaryawa ya na yi min kame kamen su na maza in sun aikata wani abu na rashin gaskiya.
"Wannan hoton wai kike mgana?
Ya faÉ—a ya na nuna min wayarsa kallo ma bai isheni ba. Na cigaba da kurban tea É—in da ke gabana.
"Daugther ce ta matsa min sai mun yi hoton nan. Har walpaper É—in ma ina tunanin ita ta saka shi na gani ina ta son na cire sai na sha'afa"
Shi ya gama kiɗan shi sannan kuma ya yi rawan shi ban ce masa komai ba ganin haka yasa ya yi shuru shima bai ƙara mganar ba, ban sanin masa ba ko ya sauya sai can wata rana na ga ya saka hoton Khalipa da aka ɗauke shi ranar da ya zo duniya a raina na ce kai dai ka sani da munafuncin ka. Ko ya faɗa ko bai faɗa ba a irin soyayya da son da ya ke nuna ma Khalipa kowa ya shaida ya na matuƙar ƙaunar shi, ko ya na gidana ya dinga kallon hotunan Yaron da Video tare da yara suna nishaɗin su, wato ba zai iya ma kwana bai gan shi ba sai ya kalli hotunan shi ya ke jin daɗi. na san akwai abubuwa a gaba shi ya sa na roƙi Allah tun kafim zuwan lokacin ya ba ni haƙuri da juriya sannan ya ba ni wuyan ɗaukan koma mene ne zai faru anan gaba.
*****
*BAYAN SHEKARA UKU.*
KANO.
LODGE ROAD.
20 September 2019.
Lahadi. 11:30 na safiya.
Kwance na ke a kan makeken sabon gadona na kamfanin royal. Na lulluÉ“e kafafuwana zuwa cikina da lallusan bargo mai ruwan madara. A cikin barcin ina can ina mafarkin wai gani a makka na je gaban ka'aba ina ta addu'a ina kuka, har ina jin danshin hawayen a saman fuskata. Ƙara narkewa na yi har ina Æ™ara motsawa sai dai me? Ina jin danshin ruwa a fuskata har zuwa wuyana a tunanina mafarkin ne ina kuka ashe ba mafarki ba ne zahiri ne sai da na ji ruwa tsii na ta sauka a saman fuskata zuwa saman wuyana ya Æ™i tsayawa sannan na fara dawowa hayyacina.Â
Idanuwana na fara buÉ—ewa a kasalance, ai da sauri na rufe saboda ruwan da ya yi min feshi a cikin idanuwana da sauri na kare fuskata ina É—an yarfa hannuwana.
Dariya na ji ana yi ta yara ƙasa ƙasa da hanzari na zuro kafafuwana ƙasa ina goge fuskata. Khalipa na gani a tsaye a gaba na da bindigarsa ta wasa mai ruwa a jikinta wacce Yallaɓai ya siyo masa da ya je Saudiya wannan shekaran. Yaron ya na kallona ya na dariya wani takaici ya cika min zuciya kuma saboda bai da kunya har ya na ƙara saitani da bindigar ya na faɗi cikin muryan yara.
"Umma faya faya."
Wai Umma fire fire, ɗan mirmishi na ƙakaro kafin na miƙe tsaye na riƙe bindigar na duka a gaban shi ina kallon shi yaro ne ɗan kimanin shekaru uku da wattani, sai da Khalipa ya fara girma sannan mutane suka ƙara gasgata da Baby ya ke kama har ya na yin jikinsu na gaza gaza kamar na ƴaƴan hutu ko da ya ke ƴaƴan hutun ne tun da uban su yanzu ya samu duniya a tafin hannun shi sai juya ta ya ke yi a yadda ya so.
"Khalipa ba ka ga Umma na barci ba ne?
Na faɗa ina shafa sumar kansa, sai kawai ya fara min dariya. Ya na mgana amma ba a ganewa sosai amma ya na kiran sunan kowa kamar ni Umma da Abban su, sai Ya Jidda da Ya Baby sai sunan Mami wato Gimbiya a bakin shi da sunan su Nene ya san sunan kowa kuma ya iya kiran su, ina ƙokarin sake magana ya ƙwace bindigarsa ya fice da gudu daga ɗakin na bishi da kallo har ya fice sannan na miƙe ina hamma gefen gado na koma na zauna na ƙura ma window da ke cikin bedroom ɗina ido ina kallon rana da ta fara hudowa ta na shigowa ta tsakanin labulayen da ke cikin bedroom ɗina da ya sauya kamar ba shi ba sakamakon komai sabo ne a cikin ɗaki har ta fentin ma gabaɗaya.
A cikin shekarun ukun da suka gabata abubuwa da dama sun faru masu daɗi da aka sin su. Masu daɗin sun fi yawa shi ya sa zan fara da su. Yallaɓai ya samu ƙaruwa ta arziƙi da dama a cikin wannan shekarun, karuwan kuma ba iya na dukiya ko arziƙi ba har na ƙara samun ƙaruwan ɗa namiji daga bangaren Gimbiya Khalipa da na shekara ɗaya da rabi ta sake samun ciki wannan karon ma aiki aka sake yi mata. Tun da ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda na farko ma ai an farka ta. Ta na nan yanzu haka ta na goyen Muhamamad Yusuf(Anwar) bayan haka kuma Yallaɓai ya yi ta shura ya na ta samun manyan kwangilolin gine ginen manyan makarantu da ma'aikatu da gidaje mafiyan shaharan ciki shi ne na gina makarantun aikin jinya la da gina makarantun manyan jamu'u na gwammati da nayan kasuwa cikin shekarun ukun nan Yallaɓai ya samu ɗaukaka da shahara. Yanzu haka ya na nan ya na gina gma'aikatarsa ko na ce kamfaninda anan zooa road ne ya siya wani tsohon ma'aikatan siyar da motoci ya buge shi ya na gina ƙaton kamfanin shi mai hawa uku amma dai suna nan suna aiki a tsohon offishin shi in da yanzu gabaɗaya sama da ƙasa ya zama duka mallakinsa sannan ya ɗau ma'aikata masu karatun abin da ya shafi fanni zane zane yanzu shi ba ya zane sai dai ya saka yaran shi su yi, sannan ya na da yara a bangaren masu leburan aikin gini sama da mutum ɗari uku a ƙarƙashin shi, ya na matuƙar taimaka ma matasa da aikin yi, yanzu haka gidajen bulo ɗin sa sama da guda biyar ne a garin Kano. A cikin shekaran nan ya biya ma kansa Makka shi da Nene suka je suka sauke farali suka dawo. Da ya dawo ne gabaɗaya rabin tsarabarsa kayan wasa ne na Khalipa da Anwar, Jidda da ta zama yan mata shekaranta sha bakwai tana kuma SS2 ne a babban sakandiri a yayin da Baby ke da shekaru goma sha ɗaya a duniya ta na ajin karshe a primary ne. Su kaya ya siya musu tun da sun girma sun wuce kayan wasa.
 Yanzu haka gidan da Gimbiya ta ke ciki Yallaɓai ya siye shi ya zama mallakin shi sannan ya siya wani ƙaton fili a Aluvenue, kimanin sama da miliyan ashirin in da ya ce zai gina mana ƙaton gida da zai haɗe iyalan shi waje ɗaya. Sannan ni da ita gabaɗaya ya sauya mana fenti a gidajen mu sannan ya siya mana sabbin furtures, ni dai tsoffin nawa wasu na ba ma Inna Mariya wasu kuma na aika da su Yashe domin suna bukata kujerun babban falo na da gadona kuwa Rahila na ba ma wa tunda na yi sabbi masu kyau da tsada. Sauran tarkacen kayan kitchen kuma Maman Saude na ba ma wa. Katifa ma ta ɗayan ɗakin Maman Nana mai yi min kitso na ba ma wa.
 Har gobe kuma ina nan da sana'ar sai da hijabaina kuma yanzu har sari ma na ke ba da wa.Maganar buɗe shagon saloon ta daɗe da shan ruwa. Yallaɓai bai sake min mganar ba nima ban ƙara yi masa ba. Ita dai Gimbiya kam yanzu shagon sai da abayoyi gare ta da takalma kuma Yallaɓan ne ya kama mata shagon da cewa ita ta kama da kanta da gadon ta na tsohon mijinta. kuma ta cigaba da oder kaya daga kasashen ƙetare. Akwai mai zama mata a shagon amma itama wani lokacin ta na zuwa ta zauna in ta na da lokaci. Kuma har gobe ta na cigaba da aikin ta na Gwammati. Cikin kuma ƙaruwan da aka samu shi ne na bukukuwan da muka sha kai da kai.
Farko dai na Marwa da Kawu Abba muka fara yi ita yanzu haka ma ta na nan da yaron ta mai suna Abdallah ta na garin Rano sannan ta na aiki a asibitin Gwammati na garin Rano, bayan ita kuma a wannan shekaran muka yi bikin Anti ƴar wajen ya Murja ta yi aure anan garin Kano. Bayan na ta kuma muka yi na Jawahir da Musbahu a rana ɗaya. Jawahir ta na kaduna Musbahu kuma a garin Kano ya ke zaune a kuma gidan kan shi tun da shi ne Manaja na kamfanin Yallaɓai sannan shi ke rike da gidajen bulo ɗin su gabaɗaya a ƙarkashinshi suke, Adnan kuma ya na nan BUK ya na master ɗin shi. Datti ma ya gama kasu ya na Abuja gidan Ya Auwal ya na aiki da wani kamfanin littafai bai yi aure ba. An yi rashe rashe tun da har Baaba sani mun rasa daga yashe. Bangaren Yallaɓai kuma sun rasa Innayi sai dai fatan Allah ya yi musu rahama.