← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 89

Sashe 47

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina kwance a kan gado ya shigo na yi masa sannu da zuwa ya amsa ya na kallona.

"Ba ki yi barci ba?

Ya faÉ—a lokaci É—aya ya na cire agogon hannun shi.

"E."

Na bashi amsa a gajarce sai ya jinjina kai kawai ya fice ya shiga tiolet ya ɗan daɗe sannan ya fito bai yi wanka ba na ga dai fuskar shi da ruwa, duk ina zaune ina kallon shi na yi masa ta yi abinci kamar yadda na yi zato sai ya ce min ya ƙoshi ya ci abinci a can Gwammaja.
Sai da na bari ya yi shirin kwanciya ya na zaune gefen gado da wayarsa a hannunsa ya na dubawa ina kallon shi ya na ta mirmishi koma mene ne ya ke dubawa ya na jin daÉ—in haka.

"Ya jikin Nenen?

"Da sauƙi Alhandulillah."

Ya ba ni amsa amma hankalinshi na kan wayarsa.

"Allah ya ƙara mata lafiya."

Ya amsa da Amin haka a gajarce, sai na É—an yi shuru kafin kuma na yaye bargon jikina na sauko da kafafuna daga saman gado na sauke a saman cafet É—in gefe da gefen gadon.

"Yallaɓai."

"Uhm."

Ya amsa min a ciki hankalin shi har a lokacin na kan wayarsa.

"Na ce ba."

Sai ya ji na yi shuru sai ya juyo ya na kallona bayan ya ijiye wayar a gefen shi, ya na mai kallona kafin ya ce.

"Ina jin ki. Kika ce me?

Kai tsaye na ke kallon shi kafin na ce" Wata shawara na ke so ba ba ka Yallaɓai."
"Ina sauraran ki."
Ya faɗa ya na mai ƙureni da ido amma fa ya wani haɗe rai kamar ya san abin da zan faɗa

"Me zai hana duk ranar girkin Gimbiya ka riƙa kwanan ka kawai a can Gwammaja."

Giransa ya tattare waje É—aya ya na min wani kallo amma ban fasa mgana ta ba.

"Zai fi tunda akwai É—akuna a can"

"Me ya kawo wannan mganar kuma?

"To ai na ga kana raba mana dare ne da ita. Da zuwan da kake yi kana raba dare barci kawai ke kawo ka nan shi ne na ce duk ranar girkinta ka riƙa kwanciyarka a can har ta koma gidan ta."

Ya daÉ—e ya na kallona bai ce min komai ba, ni kuma ganin ya yi shuru ya sa na tashi zan fita zuwa tiolet har na É—an gota shi zaune a gefen gado.

"Kin gama mganarki?

Sai na juyo ina kallon shi kafin na ce" E. Na gama."
Sai kawai na ga ya miƙe ya wani harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ya fara takowa gabana cikin wani yanayi, sai na tsaya kawai ina kallon shi ba tare da na yi mgana.

"Sadiya."

Ya kira sunana a kausashe bai ma jira na amsa ba ya ce" Kishi ne ke rufe miki ido ko?
Cikin mamaki na kalleshi ina shirin mgana kawai ya wani É—aga min hannu a fusace ya ce" Ke kaÉ—ai ce mai bakin magana!? Ko ke kaÉ—ai ce ake yi ma ba dai dai ba? Ko ke kaÉ—ai ce ake zalunta ehe?

Ya ƙarishe faɗa ya na mai yi min tsawa, sai na yi baya kawai ina kallon Yallaɓai na kasa mgana.

"Ko domin kin ga bana son ina yi miki faɗa? Ko kina tunanin ina tsoron ki ne? To bari ki ji na faɗa miki ba ki isa ba, ba ke kike aurena ba ni na ke auran ki Sadiya saboda haka ki shiga hankalinki tun kafin ki ɓata min rai na buɗe miki bakina ba za ki ji daɗi ba."

Sai na fara mamakin sa? To wai ya na jira na ne, me na yi masa da zai wani fara balbaleni da masifa daga faɗin gaskiya ni ma ko a fusacen na kalle shi kafin na ce" To wai me aka yi maka? Daga faɗin gaskiya sai ka fara wasu mganganu da ban gane musu ba! Ni na ce ka yi laifi ne! Rayuwarka ce yadda ka so ai haka za ka tafiyar da ita. Kuma da kake maganar za ka buɗe bakin ka in ka bude ba zan ji daɗi ba, to don Allah Yallaɓai ka buɗe bakin naka ka yi mgana mana sai me?

Na faɗa ina watsa hannayena daman raina a ɓace ya ke kuma a kusa na ke.

"Kika ce sai me ko Sadiya?

Na taso masa ina faɗin" E sai me in ka buɗe bakin? Me za ka faɗa min wanda ayyukan ka ba su nuna min ba. Koma za ka ce ka ce gaskiya na faɗa ina lura da kai kwana biyu nan kake cin abinci kuma ka dawo a kan lokaci kwana biyu kuma kana can Gwamnaja sai dare ka ke dawowa in na yi maka ta yi abinci ka ce ka ci a can, me ya sa ba zan yi tunanin ka raba ma kwanan ba ne kar a cuceta? Ni fa mafita na kawo maka domin kar ma ka yi tunanin alfarma ka ke yi min da kake kwana ranar girkinta a gidana shi ya sa na ce ka je can ka kwana ko ka riƙa tafiya can gidan nata kana kwana babu ruwana tunda in ba ka kwana a nan ɗin ba ba mutuwa zan yi ba, sannan kwanan ma da ka ke yi anan ɗin ba wani amfani kake tsinana min ba."

Raina ne ya ɓaci na riƙa sakar masa mganganu na gama na juya zan bar masa ɗakin sai ya saka hannu ya fizogoni ya dawo dani cikin ɗakin da karfi har ya na hankaɗani na yi baya Allah ya sa ban faɗi ba.

"Ina za ki je! Tun da kin gama fadin na ki sai ki jira nawa Malama."

Ya faɗa ya na nuna min yatsa, sai kawai na koma na yi tsaye na harɗe hannuna a ƙirji ina girgiza jikina kafin na ce" Ai ban hana ka mgana ba."

"Me ke damun ki? Me kuma kike taƙama dashi ne? Tun da na yi auran nan kike bi na da fitina ina ƙyaleki saboda ina ganin kamar ni ne ban yi miki dai dai ba, amma me ya sa haka! Me ya sa kike da ɓakin kishi ne Sadiya?

Na buÉ—e baki na rufe ya fi sau uku ina rufewa na kasa mgana.

"Ni ke kake kira da mai baƙin kishi Yusuf?

"E mana baƙin kishi ke damun ki, kin ƙi ki kwantar da hankalinki ki yi ta zarge zarge. Kar ki manta itama Matatace kamar yadda kike matata kuma auren da na yi zunubi ne? Ko Allah ya hana ne?

Ai sai kawai na rufe bakina na yi shuru, ganin idanuwan shi sun rufe ya na zaro maganganu.

"To ba ri ki ji na faɗa miki ba ki isa ba. Ke in har kina da tunani za ki kawo wannan mganar? Gwammaja nan ne gidan Ubana kuma uwata ce ba lafiya ta ke jinya. Gimbiyar da kika saka ma ido kike kishi da ita ita ce ta bar komai na ta har da ni mijin da kike takama da ni ta je ta zauna ta na kula da mahaifiya ke ina kike? Ba kina gida akwance ba? Kin taɓa tunanin cewa bari ki je ki taimaka mata! Ko shekaranjiya da na kira ki na ce ki je kin je! Kin je? Na ce kin je?

Ya ƙara daka min tsawa sai na saka hannuwana duka biyu na toshe kunnuwana saboda sosai ya yi min ihu a saman kaina.

"Ki saki kunnuwan ki saurareni da kyau. Daughter ta yi min komai kuma komai za ki ce kin daɗe ba ki ce ba. Kwana kuma babu ruwanki ba ke za ki faɗa min abin da ya kamata in yi ba, in ina son kwana a can ke ba ki isa ki sani ko ki hana ni ba, shawara da zan ba ki ki riƙa saka alheri a cikin zuciyarki Sadiya saboda wata rana kar ki ji kunya."

"Ba ni da alheri a zuciyata ka ke son ka ce mini Yusuf?

Na faÉ—a muryata na rawa ina nuna kaina.

"To ina alherin. Kin bi kin kwazzabi kan ki tunda na yi auren ba ki bar ni na huta ba daga kice na yi miki kaza sai kice ƴan'uwana sun yi miki kaza duk dai na biki da ki yi hakuri saboda a zauna lafiya. In ba zuciyarki ba ta saƙa miki alheri ba yanzu ya kamata a wannan halin ki tare ni da wannan mganar? Gimbiyar da kika tsana ita ce ke son ki tsakanina ga Allah ƴaƴanki kamar na ta ta ɗauke su amma ke ko sau ɗaya a zuciyarki ba za ki ɗan mutuntata ba? Ta na can ta na wahala da mahaifiyata ko sau ɗaya kin ji a ranki ya kamata ki gode mata! Ai ba ita kaɗai ba ce matata ke ma ɗin matatace kuma akwai haƙƙin mahaifiyata a kan ki Sadiya, kin je? Ba daina zuwa duba ta kika yi ba amma kullum anan gida na ke barin ki kwance amma saboda ba ki da kunya har kina tara ta da wata mganar banza saboda kin ga na yi miki shuru? To ki fita daga idanuwana ki kuma fita daga abin da ya shafe ni da matata babu ruwanki, kamar yadda kema kika ce na daina saka ki a lamarinta tun a baya to kema babu ruwanki da sha'aninta ko wani abu dake tsakanina da ita. Ni ne na ijiye ki, da ni za ki yi ba ita ba."

Ko kafin ya gama mganganunsa na durƙushe a ƙasa ina kuka mai sauti lalle duniya juyi juyi wai ni yau Yallaɓai ke faɗa ma ba ni da alheri a zuciyata.

Ina kuka na ɗago ina kallon shi hawaye wani na koran wani cikin shaƙewar murya na nuna kaina ina faɗin" Ni ka ke faɗa ma ba ni da alheri a cikin zuciyata Yusuf? Ni Sadiya?

"E ke kika ja. Me ya sa zuciyarki ba ta ba ki damar ganin alherin mutanen da ke tare da ke? Kishi hauka ne Sadiya?
Chapter 47 · 0% Book details