Sashe 75
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da muka isa falon Alhajinmu cike, har Baaba ta iso matar nan ina gaisheta ba ta amsa ba, ni ko ban ƙara ba na wuce wajen Gwaggo na duka ina gaisheta ita da Alhajinmu. Shi kuma Yallaɓai ya fara gaisawa da Mazan har Ya Auwal na gani shi jiya da yamma ya sauka garin. Sai Ya Muntari da Ya Abubakar sai Alhaji Mustapha, matan kuma daga ni sai Ma'u sai Ya Aina sai Ya Balki sai kuma Ya Murja sai Gwaggo da Baaba.
Dukkansu na yi musu magana ban da Ma'u. Saboda sai da na ganta na sake jin wani ƙuna ya taso min daga ƙasan zuciyata ta kalle ni nima na kalleta amma ba mu yi ma juna mgana ba. Sai dai na ɗan ji sanyi da na ga fuskarta gefe da gefe duk sun kumbura.
A gefen Ya Aina na samu waje na zauna shi kuma Yallaɓai sai ya zauna a gefen da Ya Hamza ya ke zaune a ƙasan cafet ɗin da ke malale a falon Alhajinmu.
 Ya Muntari Alhajinmu ya umarta shi ya buɗe mana taro da addu'a. Sannan ya ce dangane da sanin dalilin taruwarmu wasu sun sani wasu kuma ba su sani ba. Amma yanzu zan ƙara mamaita dalilin taruwarmu anan wajen yanzu nan kuma.
Kiran sunana Alhajinmu ya yi na amsa sai ya ce na faɗi duk abin da ya faru daga farko har ƙarshe. Na ko gyara zama na fara maida zence kafin na gama Ma'u ta fara kukan makirci Baaba ko ina dire maganata ta nuna ni da yatsa kafin ta ce" Ƙarya kike masharranciya. Asma'un ne za ta faɗi haka? Ai ko ba ta san in da kika fito ba Sadiya Asma'u ba ta da wannan halin ki dai canza wata ƙarya wannan ba ta hau ba."
"In karya ake yi mata ai ga ta nan sai ta ƙarya ta ko?
Ya Hamza ya katse ta itama sai ta kalleshi kafin ta sake wata mgama ya kalli Ma'u ya na faÉ—in" Ba ga ta nan ba. Ta buÉ—e ta ce duk abin da aka faÉ—a sharri ne ba gaskiya ba."
Sai Baaba ta kalli Ma'u ta na faÉ—in" Bar kuka buÉ—e baki ki karyata ta a gaban kowa da kowa"
Na san daman Ma'u za ta iya karyata ni shi ya sa ma da ta buɗe ba ki ta ce ƙarya ne ita ba ta faɗa ba ban yi mamaki ba.
"To kun ji dai ko? Ina fatan yanzu za ku yarda Sadiya na bin Asma'u da bi ta da ƙulli. Kuma magana kan dangin bokaye ba Mau ce ta faɗe shi ba tun tale tale haka ake kiran gidan su Ruƙayya da shi, su kan su ai ba su isa su hana ba. Wataƙila itama yayar mijin na Sadiya a can a gari ta ji labarin shi ne saboda kin tsani Asma'u za ƙi kulla mata sharrin ita ta faɗa ko?
Ta ƙarishe faɗa ta na kallona sai ma na kasa mgana, ina tattaro abin da ya kamata na maida mata kar ace na yi rashin kunya.
"Baban Jidda ko za ka taimaka ki kirana mana ita yayar naka? Kamar muna bukatar ta anan wajen"
Ya Hamza ya faɗa fuskarshi a ɗaure. Shi ko Yallaɓai ya fito da waya a cikin aljihun ya na faɗin" Ba zai gagara ba, bari na kirata na ce ta taho yanzu."
"Yauwa mun gode. Ke kuma yanzu ita wacce kika faÉ—a ma mganar za ta zo. A cikin su za mu gano mai son ya yi wasa da hankalim mu"
Ya faÉ—a ya na mai kallon Ma'u Gwaggo na gefe ta ce gwara haka domin kar ma a ja mganar da nisa. Alhajinmu kuma na zaune amma bai yi mgana ba.
Ina ga Ma'u ta ɗauka wasa ne ba za a kira Anty Bahijja ba. Sai da ta ga Yallaɓai ya kira wayarta ya kuma saka a speaker sai ta rage kukan makircinta ta na ƙifta idanuwana kamar wacce ta yi ƙarya. Allah na tuba ai ƙaryan ma ta yi.
Ta na ɗaukan wayan da sallama Yallaɓai bai ma tsaya amsawa ba ya ce" Ina gidansu Sadiya. Ana maida mgana Ma'u ta ce ita ƙarya ake yi mata mganganin da kika ce ita ta faɗa ta ce ba ta ita ba ce.
"In ji ita Ma'un?
Anty Bahijja ta tambaya cikin mamaki.
"E. Shi ne aka ce ko za ki iya zuwa nan gidan su Sadiyan?
"Me zai hana? Ai sai na zo. Kuma in ba Ma'un ta ke faɗa min ba ina na ke jin wasu labaran? Ita ta san ita ta zo asibiti duba Gimbiya ta faɗa min mu yi hankali da Sadiya za ta iya sanadin cikin Gimbiya tunda sun yi gadon shiga bokaye ko a gabanta zan iya maimaita haka sai ta ƙaryatani na gani"
"To shike nan in da buƙatar zuwan na ki zan sake kiran ki"
Daga haka Yallaɓai ya katse kiran gabaɗaya sai kowa ya maida hankalin shi kan Ma'u da ta yi wani iri da ka ganta ba ta da gaskiya. Shi kan shi mijin na ta a cikin mamaki ya ke kallonta.
"Da sake. Wannan sharri ne ban yarda da mganaganunsu ba."
Baaba ta faÉ—a a fusace itama fa ta san gaakiya amma ta na neman take gaskiyan.
"Za ki faɗa mana gaskiya ko sai ranki ya ɓaci?
Ya Hamza ya faɗa cikin tsawa. Da ya sa Ma'u ta tsorata daman ko a baya ta na son shi amma kuma ta na shakkar shi. Sai kawai ta fara ɓarin jiki amma ta kasa mgana.
"In faÉ—a ko ba ki faÉ—a ba?
Ya sake maimaita tambayarsa cikin hargagi da ba ta san lokacin da ta ce e ita ta faɗa, Masu ƙoƙarin kare ta ma duk sai suka yi shuru jikinsu ya yi sanyi kuma ta ce ita ta faɗa amma ta koma ta na ta faman kuka.
Ya Hamza sai sake mgana Alhajinmu ya É—aga masa hannu.
"Ƙyaleta Hamza. Yi mata a hankali mana."
Ya faÉ—a cikin yanayinsa kafin ya mai da kallonsa kan Ma'u da ke kukan munafumci.
"Asma'u"
Ya kira sunanta ta amsa cikin kuka in ka ganta sai ka rantse da Allah an yi mata wani abu ne ko wani nata ne wani abu ya same shi ko an yi mata mutuwa.
"Me ya sa kika aikata abin da kika aikata Asma'u? Me ya sa kika zaÉ“i ki tozarta yar'uwamki da ahalinta a idon duniya? Me ya sa kika aikata haka? Me ya sa kika zama haka? Ina ganin ki da girma a cikin idanuwana amma aikata abin da ban yi zato ba ya sa girmanki da Æ™imarki da na ke gani ya ragu a cikin idanuwanan tabbas Asma'u kin yi É“arna. Æarnan ma mai tarin yawan da kafin a yafe miki sai an É—au lokaci. Kin ci amanar zumunci, kuma ba Dubu kika tozarta ba, ni kika tozarta kamar yadda itama in ta yi miki wani abu na tozarrci to itama ba ke ta yi ma wa ba. Ni ta yi mawa"
Ya ƙarishe faɗa cikin kaushin murya ka na ji za ka san ran shi ya gama ɓaci. Ma'u sai kuka ba mgana saboda ba ta da tacewa.
"Ina jin ki. Ki bar kuka ki faɗamin dalilin ki na yi ma zuru'an ki wannan tozarcin Asma'u. Ni fa da kaina na kira ki na kira Dubu na kira mazajenku na tara ku na yi muku sulhu. Na san Dubu da na fitina da riƙo amma ba ta tsallake mganata tun da na ce ta yi zumumci da ke ta ce za ta yi na san za ta yi ne. Kuma zan iya ba da shaidar ta ba ma ita ba kaf ɗin su ba za su yi miki ƙwataƙwacin abin da kika yi ba, sannan in suka ga wanda zai ci mutumcin ki sai in da ƙarfin su ya ƙare. Amma abin tir sai ga ki da kan ki kike zuwa kina cin zarafin yar'uwanki domin ki ɓata mata suna ki kuma haddasa mata fitina a gidan aurenta? Shin me kika aikata? Kin san sunan abin da kika aikata! To sheɗanci ne. Kin zama sheɗaniya tun da kin zama silan haɗa fitina da dama. Kin ba ni kunya, ban taɓa zaton haka daga bangaren ki ba Asma'u."
Ma'u sai kuka ba mgana, kowa jikinsa ya yi sanyi amma ban da ni domin ni na san wace ce Ma'u a kukanta ma ba Saduda a cikin shi. Alhajinmu ko a yadda ya ke mgana ranshi ya riga ya gama ɓaci, Baaba ce ganin Ma'un ta ƙi mgana sai kuka sai ta tare mganar da cewa.
"Yaya Sule ba fa gaskiya ba ne Ma'u ba za ta yi ma Sadiya haka ba. Sai ma ita Sadiyar ce in aka ce ta yi hakan ba zan yi musu ba, saboda tun tuni ba ta ƙaunar Asma'u kowa kuma ya san haka. Shi ya sa na ce a yi.."
"Ba ke na ke tambaya ba Hasiya. Ki bari Asma'u ta ba ni
Amsa."
Alhajinmu ya dakatar da ita a fusace da ya sa dole ta yi shuru ita kanta ta ji kunya ba za ta nuna ba ne, to ga suruki a wajen kuma ya gano munafuncin yarki dole kunya ta kamata amma da ya ke ba ta san kunya ba, ta na ƙoƙarin nuna a yi adalci yarta ce mai gaskiya ni ce mara gaskiya.
"Muna sauraran ki. Ki faÉ—a mana dalilin ki na aikata abin da kika aikata."
Alhajinmu ya sake tambayarta da ya sa cikin shessheƙan murya ta ce" Ban da wani dalili Alhaji sharri sheɗan ne don Allah ka yi haƙuri."
Ta faÉ—a ta na kuka kamar za ta shiÉ—e Ya Hamza ya fara masifan ai mutum ba ya aikata laifi kuma ya ce ba dalili ita dai ta san dalilinta na aikata abin da ta aikata.
"Wallahi ba ni da wani dalili kawai dai sharrin sheÉ—an ne"
Ta sake faÉ—a ta na gunjin kuka. Sai kowa ya yi shuru ya ba sauraranta.
"Alhajinmu ka yi haƙuri ka yafe min. Kuma zan karɓi duk hukuncin da ka yanke min"