Sashe 34
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bai hana ni kuka ba sai da muka yi kusan mintina goma a haka, daga ni har shi muna ji ana ta kiran wayarsa da ke saman side drower ɗin gadonmu. Amma bai sake ni ba har sai da na gaji da kukana na yi shuru ni ce ma na sake shi tuna cewa ana can ana jiran shi a waje sannan ita kanta Gimbiyar ta na can ta na jiran sa. Ban kalle shi ba da sauri na juya baya murya ta shaƙe ina faɗin.
"Su Tariq na waje suna jiran ka."
Na faɗa lokaci ɗaya ina goge hawayena da hannuna guda ɗaya. Ƙaramar jakarsa na gani a saman gado alamun ya gama haɗa kayan shi da zai bukata acan ina kallon jakar sai ga hawaye sharr, amma ina ƙokarin tare su, ya na ƙokarim sake riƙe ni na yi saurin kaucewa ina faɗin.
" Yallaɓai ka je kawai sai da safe."
Na faɗa ina ƙokarin maida kukana da ya taso min amma zuciyata sai da ta rinjayene na fashe masa da kuka na ma kasa iya kallon shi, sai kawai na juya da sauri zan fita amma bai bar ni ba da sauri ya riƙo ni amma ina ƙokarin zamewa daga riƙon shi cikin kuka kamar ina masa magiya na ke faɗin
"Don Allah."
Ina kuka maganar ta tsaya mini na kasa cigaba da magana sai ya sassauta riƙon da ya yi min ya na kallona wai ni Yallaɓai ke yi ma kallon tausayi saboda ya san ɗin abar tausayi ce.
"Don Allah ka ƙyaleni."
"Don Allah."
Na faÉ—a ina masa magiya kuka na ke yi kamar raina zai fita, sai kawai ya sake ni na juya zan fita daga É—akin sai ya kira sunana.
"Sadiya."
Sai na dakata amma ban juyo ba, sai dai na saka hanuna guda É—aya na dafe bakina har sautin kukana ya fito.
"Ki yi hakuri."
"Kin ji."
Wai haƙuri ya ke ba ni? In na ce ban hakura ba zai fasa tafiya ne? Ko kuwa zai iya maida hannun agogo baya ne, ko juyawa ban yi ba na buɗe kofa na fice sai na rasa ina zani kawai sai na buɗe kofar tiolet na shige na rufe ƙofar da sakata na sulale sai ga ni na yi zaman dirshan a saman tayels ɗin Tiolet ina mai fashewa da kuka da karfin gaske, suya zuciyata ke yi, har hancina na ke jin ya na fitar da wani yaji yaji, idanuwana sun yi min mugun nauyin da na kasa iya juyawasu, kaina na wani irin saramin da ƙarfin gaske, kaina na kasa a cikin gwiyoyina ina cigaba da kukana mai sauti, roƙon da na yi masa ne ya sa ya ƙyaleni na ji fitowarsa daga bedroom sannan jikina ya ba ni ya daɗe a ƙofar tiolet ɗin kafin ya buɗe kofar korido ya fice, ba jimawa na ji buɗe get din sa tunda shima window ɗin makewayin na ta haraban gidan ne, ban san ko shi ya faɗa musu ga in da na ke ba domin can ba jimawa sai ga Farida ta zo har ƙofar tiolet ɗin ta na kiran sunana ban amsa ba, sai ga Sameena Amina da Rahila kar su yi tunanin wani abu ya sa daga ciki na yi musu gyaran murya.
Ban san suna tsaye a ƙofar Tiolet ɗin ba, har sai da na wanke fuskata ina fitowa na gansu tsatsaye cikin damuwa sai kawai na yi mirmishi na fito ina rufe ƙofar Tiolet ɗin lokaci ɗaya ina faɗin" Lafiya ta kalau fa kar ku ɗaga hankalin ku."
Na faɗa ina raɓawa ta gefen Rahila na buɗe kofar Bedroom ɗin mu na shiga sai na juyo ina rike da kofar ganin duk sun bi ni da kallon Tausayi sai na ƙara yin mirmishi da kumbararrun idanuwana kafin na ce.
"Da gaske na ke yi lafiya ta ƙalau. Sai da safe ina so na zauna ni kaɗai ne."
"Kin tabbata?
In Farida ita kuma Amina sai cewa ta yi" Ko na zo na taya ki kwana ne Ya Sadiya?
Sai na gyaÉ—a mata kai alamun toh, sai Sameena ta ce hakan ma ya yi, na juya na shiga cikin É—akin Farida ce kaÉ—ai ta biyo bayana sauran kuma suka koma a gefen gado na zauna ina yarfe ruwan fuskata.
Ta na tsayen ba ta zauna ba ta ce" Ki yi ta kiran sunan Allah, in natsuwar ba ta samu ba ki kunna karatun Qur'ani in sha Allahu za ki samu salama da Aminci."
Sai na amsa mata da toh, bayan na ce ta ɗauko mini wayar a can falo, sai ga shi ta fita ta kawo mini ta kuma fice bayan ta yi mini sai da safe, kayan jikina na sauya domin sun jiƙe, na saka riga da wando na barci da hula sai kuma na saka wani ƙaramin hijabi domin ina jin sanyi, sai da na kwanta na rufe kafafuna da bargo sannan na ɗauki wayar tawa sai na ga Yallaɓai ya tura mini saƙo yanzu ba daɗewa.
"Ki yi haƙuri Sadiya ta. Ki sani auran da na ƙara ba shi ne zai cire ƙaunar da na ke yi miki a cikin zuciyata ba. Ki sani ke ce Yusuf haka Yusuf ne Sadiya mun zama Hanta da jini ɗaya ba zai iya rayuwa ba ɗaya ba. Kar ki ji a ranki cewa matsayin ki ya sauya ke ce a jiya kuma har da gobe ma ke ɗin ce.
Ina ƙaunarki Sadiya ta ƙauna mara yankewa. Na gode da dukkan sadaukarwarki gare ni, na gode da karamci da mutumtawa, na gode da yaƙana da martabawa ba, na yi miki alƙwarin adalci mai yawan da zan kwantata a tsakanin ki da Saudatu.
Ki yi barci cikin salama Amintattaciya ta."
In a baya ne Yallaɓai ya turo mini waɗanan kalaman yini zan yi ko kwana cikin farinciki amma yau sam sai na ji ba su yi mini tasiri ba, ban goge saƙon ba amma na yi saurin fita daga kan sunan shi, domin sai na ji kamar zuciyata na zugani da na rubuta masa cewa in har ya na sona kuma adalci zai yi mini to ya saki Gimbiya ya dawo gareni, abin da ba zai taɓa faruwa ba kenan shi ya sa na yi saurin fita daga wajen na shiga cikin wayata na lalubo karatun Qur'ani baƙara na kunna na ɗan rage ƙara na saita shi dai dai kunnuwana sannan na koma na kwanta ga casbaha a hannuna ina ja, daman na rage hasken ɗakin sai duhu, ina kwance ina ta hailala da salati lokaci ɗaya karatun na shiga kaina duk yadda sheɗan ya so ya fassara tunanina na kasa barcin ayoyin Allah sun fattake shi, haka na ji iskar natsuwa na shiga jikina da zuciyata sai ga ni na yi luf a kwance ina lumshe ido barci na son kamani barcin da ban taɓa tunanin zai iya ɗaukata a wannan daren ba.
Sai ga shi kuma ya ɗauke ni, ba ni na farka ba sai uku na dare har lokacin karatun Qur'anin ya na ta yi, sai da na juya sai na ga Amina a gefena ta na barci da waya ta daman na duba lokaci uku ta gota sai kawai na sauko daga kan gadon na yaye bargo karatun na kashe sannan na yi amfani da wayar na haska tunda na ga sun ɗauke wuta Tiolet na shiga na ɗauro alwala na dawo ɗaki na shimfiɗa sallaya sannan na saka dogon hijabina na kabbarta salla sai da na yi raka'a takwas sannan na rufe da shafa'i da wuturi, bayan na idar na tashi na ɗauko Qur'ani na fara karatu daga suratul Tauba, a hankali na ke yi karatun saboda kar na ta da Amina, ba ni na tsaya da karatu ba sai da aka fara kiran salla na biyu daga msallatan kusa damu sannan na dakata na ɗaga hannayena sama na roƙi Ubangiji juriya da hakuri sannan na roƙe shi da ya iya yi min a dukkan lamarin da ni ba zan iya ba ya cire min kishi da kyashi ya ba ma zuciyata aminci da salama na daɗe ina kai ma Allah kukana sanman na shafa, na kuma koma ina neman gafaran Allah da casbahan hannuna lalle Ubangiji shi ne ke saukar da duk waraka sai ga ni zuciyata wasai sai ma wani iskar da na ke ji ya na shigata na salama da aminci.
Ni na ta da Amina na ce lokacin sallah ya yi sai kawai ta juya ta ce min ba ta yi, fita na yi zuwa É—akin kusa da ni sai na ga har sun ta shi ma Sameena ce kaÉ—ai cikin bargo Farida ta ce min ta na hutu, na san da ga ita har Rahila sun yi mamakin ganina kamar ba ni ba, Farida ta kalleni lokacin da na ce ba ri na je na ta da su Marwa har na juya sai ta kira sunana na juyo ina kallonta.