Sashe 15
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ya gyaÉ—a kanshi kafin ya kalli Nene ya na faÉ—a min" Nene abin mamaki a ina ta ji! Kuma wa ya sanar da ita?
Nene ta ce" Sanin wanda ya faÉ—a mata sai Allah. Amma ba abin mamaki ba ne domin ta ji labari. Magana in ka iya rufe bakin wani, ba za ka iya hana wani mgana ba. Ka yi kuskure da tun lokacin ba ka faÉ—a mata ba, amma yanzu ma baka makara ba ka tashi ka je gida ka zaunar da ita ka yi mgana da ita cikin Sigar da za ta fahimcen ka ka ji ko?
Sai ya gyaÉ—a mata É—an shafa kanshi ta yi kafin ta ce" Tashi ka je. In sha Allahu ba matsala."
Da haka suka yi sallama bai fita ba sai da ya ga ta koma ta kwanta har ya ɗan rufa ma ƙafafunta bargo ya kashe mata fitilan ɗakin sannan ya fita. Har ya kai ƙofa zai fice sai ya tuna da Nene ta ce ya shiga ya Duba Gimbiya sai ya fasa fitan ya dawo zuwa ɗakin da Gimbiyar ke ciki ya ƙwaƙwansa sau biyu daga ciki ta ce a shigo sai ga shi ya buɗe a hankali ya shiga da sallama.
Ta amsa masa sallamansa tana zaune a gefen gado amma ta saka wani ƙaramin hijabi hasken ɗakin a kunne ya ke alamun ita ta kunna.
Sun haɗa ido ita dashi sai ya yi mata mirmishi itama sai ta mayar masa. Tura ƙofar ya yi ta rufe kanta sannan shi kuma ya fara takowa zuwa gabanta da jikin wadrope ɗin da ke ɗakin ya Jingina wanda a baya babu shi a ɗakin ita Gimbiyar ne ta saka a ka yi mata anan garin.
"Sannu ya jikin?
Kan ya daina ciwo?
 Ya kauda shurun da ke tsakaninsu tun bayan gaisuwan da ya shiga tsakaninsu.
"Da sauƙi."
Ta faɗa a hankali, cikin sanyin murya. Sai ya yi mata fatan samun sauƙi kafin ya ce" Kin sha mgani?
Sai ta É—ago ta kalleshi kafin ta ce" E. Na sha."
Shuru na wani lokaci ba tare da tsammani ba kanta na ƙasa ta ga ƙafafunsa a gabanta kafin ta ɗago kanta ta ji tattausan hannunsa bi sa goshinta sai da ta runtse ido cikin wani yanayi.
"Uhm na ji kan na ki ba zafi sosai."
Haka ya faÉ—a ya na yin baya kaÉ—an.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali saboda yanayin da ta ke ciki.
Ya juya kamar zai fita daga É—akin ya na faÉ—in.
"Allah ya ƙara lafiya. Ki kwanta ki huta kin ji ko?
A ƙasa ƙasa ta amsa da Amin.
Har ya saka a hannu a jikin handel ɗin ƙofar sai kuma ya juyo daman itama kallon shi ta ke yi sai suka haɗa ido.
"Daughter."
Ya kira sunanta kamar yadda ya saba.
"Na'am Daddy."
Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce" Na faɗa ma Mamanki ke da ita ku ɗan ƙaramin lokaci kaɗan. Ina so na ɗan gama da wasu abubuwan ne first daga baya sai na zo mu yi mgamar tarewar ki ko?
Ya faÉ—a ya na mai kallonta da sauri ta sunkuyar da kanta kafin ta ce" To."
Ta na mirmishi, shima mirmishin ya yi mata sannan ya juya ya na faÉ—in" Sai da safe."
"Gud night."
Itama ta bashi amsa har ya fita ya rufe mata ƙofa ba ta daina mirmishi ba ya na fita ta faɗa gado ta na tsalle da kafafunta lokaci ɗaya ta na rufe bakinta. Ta ji shigowarsa falon Nene tun farko har leƙensa ta yi bai sani ba ta na ta Allah Allah ya shigo ta gan shi ko za ta ji daɗi sai ga shi Allah ya amsa roƙon ta. Wani irin rawa zuciyarta ya ke yi na soyayya da ƙauna har yanzu ba ta daina godema Allah ba domin ya gama yi mata komai. Ubangiji ya gama ba ta komai anan duniya tunda har ya mallaka mata Yusuf. Za ta iya jiransa ko nan da shekara ne ba dai an ɗaura ba ai an gama mai wahalan.
*****
10:50pm
Goma da minti Hamsin Yallaɓai ya shigo cikin bedroom ɗin mu. Ina kwance da waya a hannuna ina dannawa shi ya sa ma na duba lokacin. Na so na yi barci kafin ya dawo barcin ne ya ƙi zuwa dole na ja wayata na kunna data ina ta shige shige. Mun yi chart da Amina sai Munnira. Sannan kuma mun yi waya da Sameena ƙanwar Gimbiya yadda ba ta min mganar auran Yallaɓai ba, nima ban yi mata ba na san ta sani kawai ba ta so ne ta fara ɗauko min mganar amma mun yi hira da ita sosai.
Ni Munnira ke ba ni mamaki ta ƙi yi min mganar ni a tunanina ko wani zai ɓoye min su sai su ɓoye min amma ina jiran su wallahi sai na yi musu wankan soso da sabulu. Datti ma da daren nan ya kira ya na ce min ashe Yallaɓai ya yo amarya Amina ke faɗa masa shi bai damu ba dariyan shi ya ke yi to daman su maza ina ruwan su ko uku Yallaɓai ya ƙaro min lokaci ɗaya na tabbata cewa za su yi ya yi dai dai. Ko a jikinsu tunda daman duk halinsu ɗaya na son kansu.
Kafin ya dawo ba tunane tunanen da sheɗan bai gayyato min ba, in na runtse ido sai na riƙa hasko shi da Gimbiya a cikin yanayin da kan iya haifar min da hauhawan jinina sama. Lokacin da ya shigo da sallama na yi niyyar ne na ƙi amsswa amma sai na taushi zuciyata na amsa masa ta gefen ido ina kallon shi, domin ni kawai na saka a raina ya na wajen Gimbiya wato tun kafin ta tare ya fara raba ma na yini saura kwana kenan.
Wanan malolon abun da ya ke cikin ƙirjina tun san da na ji labarin auran sa da bai wuce ba har yau shi ne ya taso min.
Daƙyar na iya daurewa a shaƙe na yi masa sannu da zuwa sai na ga shima bai kalleni ba ya amsa kawai.
"Ya gidan ne? Ya kika je kika samu su Alhajin?
Ashe ya tuna in da na je. Ba ya kallona kayan jikinsa ya ke tuɓewa. Nima sai na kauda kai kafin na ce" Duk suna lafiya."
Daga haka na cigaba da duba waya ta a IG har Volume na ƙure da gangan saboda haushi bai kalleni ba, kuma bai ƙara mgana ba bayan ya bar gajerun wando na ga ya fita sai na ji ƙaran ƙofa kenan ya shiga Tiolet wanka ya yo ya fito ina nan in da ya barni kwance, ina ta nazarinsa ta gefen ido, har ya gama shirin barcinsa na ga bai yi min mgana ba kuma ya na shirin kwanciya sai na daure na waiwaya ina kallon shi kafim na ce"
Abinci fa na Dinner."
Sai ya kwanta a can gefensa sannan ya ce" Ba na jin cin wani abu yanzu."
Daga haka sai na ga ya juya min baya kawai ya yi kwanciyarsa. Mamaki ya kamani amma na kasa mgana sai nima ma juya masa bayan ina sakin ƙaramin tsaki kuma na tabbata ya ji ni. Amma bai yi wani motsi ba, da gayya na yi ta shiga Yuotube ina shiga waƙoƙi ina ji domin na dame shi amma har na gaji bai motsa ba, ba ni na kwanta ba sai 12pm sannan na ijiye waya da na ji barci, ina yin addu'an barci na runtse ido sai barci.
Zai da ya tabbatar da ta yi barci sannan ya juya yana kallon bayanta.
Dole ne ya sa ya yi avoiding ɗin Sadiya ya rasa da idanuwan da zai kalleta abin da ya yi shi ne dai dai. Bai ma ɗauka zai zo ya same ta idanuwanta biyu ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya yi kwanciyar rigingine ya na kallon rufin ɗakin na POP. Ya na kuma tunanin ta ina zai fara? Duk in da ya yi tunanin zai fara ta can sai ya ga hanyar ba mai ɓullewa ba ce, ya daɗe bai yi barci ba ya na faman juye juye amma har garin Allah ya waye bai samo mafita ba.
****
Saboda rashin barcin da bai samu a daram jiya ba ya sa tun bayan da ya dawo sallar asuba ya ke kwance ya na barci sai kiran wayarsa ce ta tashe shi.
Sai ya ga Nene ce ke kiran shi da sauri ya miƙe zaune ya na daidai ta yanayinsa.
Sannan ya É—aga kiran.
"Tafida."
Ta kira shi bayan ya yi mata sallama.
"Na'am Nene ina kwana."
"Lafiya lau. Kana gida ne?
Sai ya amsata mata da E.
"Ka yi mgana da Sadiya jiya!
Cikin kasala da muryan barci ya ce" Ban yi ba Nene."
"To ka jira ni. Kar ka yi mata mgana."
Cikin mamaki ya ce" Me ya sa Nene?
"Akwai dalili. Ka jira ni."
Daga haka ta yanke wayarta sai ya bi wayar da kallo yana mamaki bai koma ya kwanta ba amma ya kishigiɗa da gado ya harɗe hannayensa a ƙirji ya na hasoso tunanin Nene na cewa ya jira ta.
Bai taɓa tunanin shirin Nene na zuwa gidan shi ba ne sai bayam mintina talatin da wayarsu da Nene ya ji kamar ana buga get duk da ya san Sadiya na can cikin gida baya tunanin za ta ji, shima domin ya na cikin bedroom ne kuma window ɗin su na haraban gidan ne.
Sai ya miƙe daga shi sai bakin wando da singleti ya fita falo sai ya ga Sadiya kwance a falon yara kallo take yi ko kawai ta na kwance ne bai sani ba.