← Book details Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 89

Sashe 13

Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na so ka da Saudatu Tafida kamar yadda Hajiya itama ta so hakan sosai wanda har sai da ta furta mini tun a wancan lokacin. Amma saboda kai ka kawo Sadiya kuma ka nuna ita kake so a lokacin in na ce ka bari za ka bari kuma za ka yi min biyayya ka auri Gimbiya sai dai na yi tunanin na zama azzaluman uwa tunda na hana ka abin da kake so domin ni na wa cikar burin shi ya sa ban taɓa yi maka mganar ba na taka ma su Bahijja burki a kan ƙin auran ka na ce su yi maka fatan alheri, domin ko suma a lokacin da Gimbiyar suke hangenka. Amma suka danne saboda na ce su bar mganar matan mutum ai kabarinsa. A lokacin da mganar auranka ya samu Hajiya ko da ba ta furta ba, ni na san ba ta ji daɗi ba amma sai ta yi fatan alheri a gare ku gabaɗaya.
  Na yi ta zura ido na ga ko za ka fahimci Gimbiya na sonka amma sai na ga ba ka nuna wata alama ba, wataƙila ka fahimta amma sai ba ka ba ma hakan muhimmanci ba. Gimbiya ta yi ta zaman jiranka ta na ture manemanta a yaƙininta cewa wata rana za ka iya fahimtar irin ƙaunar da ta ke yi maka. Amma sai ka kasa fahimtar ta, duk shekarun da ta ɓata ba ta yi aure ba ta kasa fidda yaƙini be a kanka ne, sai daga baya da ta fahimci ka fahimceta kawai dai ra'ayi ne a kanta ba ka dashi sai iyayenta da ƴan'uwanta suka yi mata faɗa har ta fidda wannam mijin ta aura sai ga shi cikin hukuncin Allah zaman bai yi tsawo  ba ya rasu ya barta. Ta dawo gida ta yi idda ta gama gashi yanzu ta dawo nan wajena da zama."

Sai Nene ta dakata ta na sauke numfashi har kuma lokacin Hannayenta na hannun Tafida ya damƙe sanyin da jikinsa ya yi ya sa gabaɗaya ya kasa motsi ya na ji zufan hannun shi na jiƙa tafukan hannayen Nene da ke cikin na shi.

"Yusufa."

Yusufu wani suna ne da in Nene ta kira shi dashi ya san mgana ce mai muhimmanci. Ba ta kiran sunan shi sai dai ta kira shi da Tafida.
Shi ya sa ya na jin haka ya É—ago da kansa ya na kallonta cikin dakiya ya amsa mata.
"Na'am Nene"
Ya amsa mata ya na tattaro dukan jarumtarsa a gabanta amma a ƙasan zuciyarsa ya yi rauni. Domin hasashen sa bai taɓa kawo sa ga wannan bingiren da Nene ta kawo shi yanzu ba.

"Ka taɓa fahimtar har yanzu Gimbiya ba ta daina sonka ba? Ko ka taɓa lura da cewa har yanzu ba ta cire tsammani da yaƙini da cewa za ka iya zama na ta ba?

Tambayoyin Nene sun yi masa tsauri da ya kasa cewa komai.. Sannan gashi ta ƙura masa ido ta na jiran amsarsa. In ya ce bai taɓa sanin Gimbiya na son shi ba ya yi ƙarya domin tun tana kunya har ta fito ma da alamomin da suke bayyana cewa ta na son shi, ba ma shi ba har mutanen da ke kusa da su sun fahimci irin soyayya da Gimbiya ta ke yi masa. Da farko shi ma ya ɗauka ya na sonta ne sai da ya haɗu da Sadiya anan ne ya fahimci ba so ba ne shakuwa ce kawai da haɗuwar jini. Sadiya ita ya ji ya na yi ma soyayyar da Ubangiji ya hallita tsakanin mace da namiji. Amma bai taɓa ƙin Gimbiya ba, sannan har gobe ta na daga cikin foverite ɗin mutane a wajensa amma bai taɓa tunanin ya saka tunanin auran ta a ran shi ba,  ba kuma domin ba zai iya auranta na ta ba sai domin tunanin hakan bai taɓa shiga ƙwaƙwalwarsa ba ne.

"Shurun ka na nufin amsarka da E Tafida"

Nene ta katse masa tunani, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Nene ba ni ba duk wanda ke tare da mu zai iya shaida akwai kyakyawan alaqa tsakanina da Gimbiya. Amma."
Hannu ya ga Nene ta ɗaga mai tana kallonshi kafin ta je fa masa wata tambayar da ta ƙara rikita shi.

"Kana son Saudatu!?

"Za ka iya zaman aure da ita?

Sai ya kasa mgana bakinsa na rawa ya na so ya yi mgana ya kasa. Tambayoyin suna da girma da tsauri in aka ce ya amsa su nan take kamar ana so ya yi gaggawa ne. A bari ya samu kamar sati ɗaya daga shi sai zuciyarsa ya gani ko za ta iya amsar tambayoyin Nene amma ina Nene ba ta bashi wannan damar ba yana ƙokarin mgana ta ƙara tare shi da faɗin" Ba buƙatar dogon lokaci ba ne Tafida ka faɗamin shin za ka iya auran Saudatu kuma ka yi zaman aure da ita?

"E. Amma Nene.."

"Ka gama min komai Tafida. Na gode da afarman ka. Na gode da biyyarka. Na gode da kyautatawarka a gareni. Allah ya saka maka da gidan aljannah. Allah ya shirya maka zuru'a ya yi ma rayuwarka da duk abin da ka saka hannu a kai albarka Na gode."
Nene ta faɗa ta na zare hannayenta daga cikin na shi sai kuma ta fara sharan ƙwalla ganin haka sai bakin shi ya mutu Nene na share hawaye ta na ta saka masa albarka da addu'o'in gamawa da duniya lafiya su suka haɗu suka ƙara kashe masa baki da zuciya gabaɗaya.

Ya ɗauka iya mamakin da Nene za ta gama bashi kenan ashe ba shike nan ba. Umarni ta bashi da cewa ya kira mata Zuwaira da Maimuna da Bahijja suma su taho gida yanzu tana son mgana da su. Ya ɗauka dai kan mganar da suka gama shi ya ke kiran su da wayarsa amma sai Nene ta karɓa ta yi musu mgana Zuwaira(Mimisco) ta fara zuwa tunda ita ce lokacin da aka kira ta ta na makaranta ta ce ma za su yi meeting ne amma ba ri ta saka a ɗaga zuwa anjuma sai ta taho. Sauran kuma suka ce yanzu za su shirya su taho suma dai hankalinsu ya tashi sun ɗauka jikin Nene ne sai da ta basu tabbacin ka da su damu ta na lafiya sannan hankalinsu ya kwanta suka ce ga su nan zuwa.

Lokacin da Mimisco ta iso gidan ta ɗan yi mamakin ganin Tafida zaune, amma sai ba ta yi mgana ba ƙila dai ya shigo gidan ne amma dai tana tunanin da akwai dalili acikin kiran na Nene.
Kalaman da Nene ta furta ma Mimisco ne ya sa É—an sauran gudun jinin da ke tafiya a jikin Tafida ya tsaya cak!

"Zuwaira Rano na ke so mu je a yau yau É—in nan."

"Rano kuma Nene! A yau kuma?

Ta faÉ—a ta na kallon Tafida shima ita ya ke kallo amma ya kasa mgana sai ta maida hankalinta kan Nene ta na faÉ—in" To wani abu ya faru ne a can Nene?
"Ba abin da ya faru sai Alheri. Aure na ke so yau a É—aura a tsakanin Tafida da Saudatu."

Shi dai sai da ya ji yam!  tsigogin jikinsa sun tashi. Numfashi ya yi sama sannan ya jawo shi ya dawo. Mimisco ko ido ta zaro ta na kallon Nene tana kuma kallon Tafida kafin ta ce"Wata Saudatun kuma Nene? Domin ita sai ta ji ma ta manta wacece Saudatun.

"Gimbiya ta mu."..

"Topha yau shi Tafidan da kan shi ya ce ya na son ita Gimbiyan! Sannan ya ce a yau ya ke son a É—aura auran?

Mimisco ta faɗa cikin ƙarin mamaki, ta na kuma mai kallon Tafida da ya kasa mgana. Nene ce ta yi mata bayanin komai ta ƙara da cewa" Tunda har ya ce zai iya zaman aure da ita me za mu jira Zuwaira! A ɗaura kawai daga baya sai a yi mganar tariyan"
Mimisco ta kasa mgana Tafida ta kalla sai taga itama ya kalleta yanayinsa kawai ta kalla ta fahimci a bazata mganar Nene ta zo masa in kiya ya yi mata ido itama sai ta yi masa alamun ya yi mgana mana.
 
Sai gani suka yi Nene ta miƙe tana faɗin" Bari na kira Hajiya na faɗa mata muna tafe."
Ta faÉ—a cikin murna wanda har ya bayyana a muryanta.
Mimisco ta yi saurin cewa"Nene dawo ki zauna."
Sai ta juyo ta na kallonsu kafin ta dawo ta zauna ta na faÉ—in" Me ya faru ne?
Mimisco ta kalli Tafida kafin ta ce" Ka yi mgana da Sadiya ne?

Sai a lokacin ma ya fahimci ƙura ne turƙe a gaban shi bai sani ba, sai ya girgiza kansa kafin ya ce" Yanzu yanzu Nene ta yi min mganar kuma a yanzun ta yanke wannan hukuncin."
Sai Mimicso ta kalli Nene kafin ta ce" Nene ki yi hakuri ki ba shi dama ya je gida ya yi mgana da matarsa zuwa gobe sai a yi yarda kike so."
Amma Nene ta ce ba ta amince ba, ya kira Sadiya a waya ya faÉ—a mata kuma ai yana da sauran lokaci.

"Waya kuma Nene? Gaskiya bai kyautu ya yi mata waya ba. Sai dai in haka kike so a je a É—aura É—in daga baya sai ya yi ma Sadiya bayani."
Nene ta ce hakan za a yi kuma ta san Sadiya za ta fahimcesa. Ba yadda ya iya har Mimisco ba ta so gaggawan ba amma ba yarda ta iya Nene ta dake har ta Kira Hajiya ta ce suna nan tafe, Bahijja ta fara zuwa daga baya sai Maimuna suna jin ƙudurin Nene suka haɗa baki suna rangaɗa guɗa su lamarin ya yi musu daɗi matuka sannan Nene ta biya su.
Da dai Tafida ya ga da gaske Nene ta ke sai ya roƙi su Bahijja da don Allah su yi shuru da wannan mganar kar Sadiya ta ji. Ya na so ne in ma za ta fara ji sai daga bakinsa har suka ɗan samu cacan baki da Bahijja domin ta ce bai isa ya hana su nuna farinciki ba.
Chapter 13 · 0% Book details