Sashe 14
Turken Gida Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da Mimisco ta shiga tsakani ta ce ya na da gaskiya. Za su tarwatsa masa gida ne ai ya na da gaskiya kuma mganar aure ai ba mganar wasa ba ne. Da haka dai suka yi alƙwarin ba za su fidda maganar ba. A lokacin ko awa ɗaya ba su ƙara a Kano ba suka ɗau hanyar Rano da shi da Nene da Mimisco da Bahijja Maimuna ta koma gidanta.
Suna kuma zuwa Nene ta isar da kudurinta sai da Hajiya ta tashi ta rumgumeta ta na mai nuna farincikinta a gidan Tafidan Rano ƙanin baban Gimbiya aka ɗaura auren Yusuf da Saudatu kan Sadaki naira dubu 100k. Kuma ba a ɗaura ba sai da shi Waliyin nata ya kira ta a waya ya tambayi izininta tunda bazawara ce kuma addini ya ba ta wannan damar ita kanta a ba za ta ta ji mganar wai ta na son Yusuf? Domin ga waliyanshi sun iso domin nema masa auranta. Da rawan jiki da na zuciya ta amince, a cikin office ɗin ta bayan Anty Bahijja ta kira ta ta ce an ɗaura auran ta da Tafida sai da ta faɗi ta yi sujjudar shukur ta na hawayen farinciki atleast dai yau burinta ya cika tabbas kar bawa ya cire tsammani duk abin da ya ke rabon ka ne ko ya hau sama sai ya faɗo a kanka. Alhamdulillah.
Bangaren Tafida Kawu Sa'adu ne da su Abba suka karɓa masa auran Sadakin kuma Nene ce ta biya da kuɗinta saboda yadda ta ke son Tafida da Saudatu. Bayan an gama ɗaura aure kuma acan gidan Hajiya aka fara ɗora girki na sadaka, bakinta har kunne ta kira sauran Ƴayanta a waya duk ta sanar da su kafin ka ce kwabo labari ya zaga Rano da kewayenta. Abba shi kan shi ya yi mamakin auran nan cikin gaggawa da Mimisco ya yi mgana ita ce ke yi masa bayanin yadda lamarin ya fara. Amma Yusuf bai iya ba, domin lamarin kamar a mafarki ya ke gani. Duk roƙon da ya yi musu sai da Bahijja ta ɗora a status a tunaninta ta cire Sadiya ko ta manta da Ma'u ne?
 Ko Tariq da ya ji yadda asalin lamarin ya faro ya ji wani iri. Duk da Gimbiya ƙanwarsa ce kuma ya na yi mata murna, amma bai ji daɗin yadda Tafida ya amince aka ɗaura aure ba tare da ya yi mgana da Sadiya ba shima Abba haka ya ce amma sun yi ta ba sa shawaran da ya koma gida ya sanar da ita gudun samun matsala, amma sai ya ji ya kasa ya na gani ta na tura masa saƙon Anniversary ɗin su sai a lokacin ma ya tuna muhimmancin ranar a gare su, sai dai ina ranar kuma sai ta rikice ta koma rana mara daɗi ga Sadiya ba zai iya kashe mata karsashinta wannan ranar ba, shi ya sa har ya gama nuku nukunsa ya koma gida ya kasa iya faɗa ma Sadiya wai shi ya ƙara aure ba tare da ta sani ba. Ya kusa shafe sama da awa ɗaya a waje ya kasa iya shigowa ga shi dai ba abin kunya ya aikata ba amma yana jin tsoro da kunyar haɗa ido da Sadiya a wannan yanayin.
Lokacin da ya shigo gidan suka haɗa ido da Sadiya sai ya ji kunya kwataƙwacin kamar ya ci amanarta haka ya ji. Ya kasa iya sarrafa kansa a gabanta. Har aka wayi gari yana cikin wannan yanayin sai daga baya ne ya fara warwarewa. Bai taɓa tunanin Sadiya ta ji mganar auran shi ba, duk da dai mganar ta zagaya dangi tunda ana ta kiran shi ana masa fatan alheri. Ya yi ta mamakin duk labarin ya je ma kowa, a tunanin shi Sadiya ba za ta sani ba shi ya sa ya ke ta shirye shiryen yadda zai tunkare ta da maganar sai ga shi duka shirinsa ya rushe. Ga shi shagon da ya kama mata har ya biya kuɗin shekara key na hannun shi, kunya da nauyin sun saka ya kasa yi mata mgana, balle yanzu in ma ya nuna mata a zuciyarta za ta ce ba domin Allahya yi ba saboda ya yi mata kishiya ne shi ya sa ya kasa bata. Ya tuna jiya har sai da Musbahu ya yi masa mganar shagon.
"Yaya Tafida wai ƙasa za mu koma ne?
Sai ya girgiza masa kai a lokacin. Domin shi kan shi bai san mafitan shi a lokacin ba. Sanin da Sadiya ta yi ba tare da ya faɗa mata ba ya yi masa mumnunan duka, saboda yanayin da ya ke ciki tun da aka ɗaura auran sau biyu suka taɓa waya da Gimbiya gidan ma sau ɗaya ya je suka haɗu bayan kuma gaisuwa wata mgana mai tsawo ba ta shiga tsakaninsu ba, ya fi so sai ya gama da Sadiya sun samu daidaituwa kafin wata mgana ta biyo baya. Ya tsara a jiya zai yi mata mgana ya sanar da ita sai kuma Allah bai so ba ya yi tunanin yau ɗin in ya koma gida amma tun haɗuwarsa da Yaya Abubakar gabaɗaya tsarin sa ya ruguje mafita ya ke nema ya rasa mafitan. Shi ya sa ya kasa iya komawa gida da wuri ya kama hanyar gidan da dadaddren kenan kuma sai ga kiran Nene ya riskeshi.
******
Ya na cikin motan bai fito ba sama da mintina talatin. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi. Wayar sa ya laluɓo a gaban Aljihunsa ya sake kiran Abba.
 Yana ɗauka bai ko jira sun gaisa ba cikin roƙo ya fara faɗin" Don Allah Kawu ka taimaka min ka zo gida gobe ka ta ya ni fahimtar da Sadiya don Allah."
  Daga can bangaren Abba ya ce" Sai kuma ka yi. Wallahi ba in da zan zo. Kai ba ka da baki ne? Ko kai ba Namiji ba ne?
A sanyaye Tafida ya ce" Kunyar ta na ke ji fa."
"To ai sai ka murje kunyar ka sanar da ita. Duk da dai bakin alƙalami ya riga ya bushe. Sai dai ka yi gyaran mgana daga baya."
Â
"Kai yanzu don Allah ba za ka zo ka yi mgana da ita ba?
"Wallahi ba zan zo ba. To ni me ye nawa! Ni ne mijinta? Kai ne mijinta kai ya dace ka zaunar da ita ka koyo kalaman haƙuri da kare kai har sai ta fahimceka. Kai fa namiji ne kuma ka fi ni sanin matarka sosai ka san kuma hanyoyin da za ka bi da ita har ta fahimceka. Amma ni dai na roƙe ka don Allah ka daina saka ni a cikin wannan mganar."
Ko ma ya jira cewar Tafida ya kashe wayarsa ya bar sa cikin damuwa da tararradi Ya daɗe zaune yana tufka ya na warwara amma duk in da ya kamo ya fara tufka sai ya warware ya kasa samun mafita guda ɗaya da zai kama. Dole dai ya buɗe mota ya fito a kasalance kamar mara lafiya ya wuce cikin gida saboda dare ya yi kowa na cikin ɗakin shi, ɗakin Maman Farko ya leƙa suka gaisa daga nan ya wuce shashen Nene falon shuru har sun rage haske alamun sun kwanta da ya yi sallama ne ya ji muryan Nene daga ciki ta na amsa masa, sai ya cire takalminsa nan ƙofar falo ya shiga har cikin bedroom ɗin Nene
Ya iske ta har ta kwanta ma ganin shi ya sa ta miƙe zaune bayan ta miƙe kafafunta ta na faɗin" Tafida sai yanzu?
Ya na sosa kansa ya ce" Wallahi na tsaya gamawa da Office ne Nene"
Ya faÉ—a dai dai ya na zama gefen kafafunta a gefen gadon. Gaisawa da tambayan iyalan shi ya ce suna lafiya kafafunta ya É—auka ya É—ora a saman cinyarsa ya na matsawa.
"Suna ciwo ne yanzu?
Ya faɗa ya na kallonta lokaci ɗaya kuma yana ƙara matsa mata kafafun duka biyun.
"Ba sosai ba. Saudatu na shafa min man zafi in zan kwanta."
Kallonta ya yi kafin ya ce" Amma yau dai ba' a shafa ba ko? Ban ji zafin sa ba "
Ya faÉ—a ya na shinshina hannunsa.
"E. Ba ta jin daÉ—i yau kanta ke ciwo ta ce min da wuri ma ta baro wajen aikinta."
Cikin nuna jimami ya ce" Subhanallah ta sha mgani?
"E. Ta sha da sauƙi ta ce bari ta kwanta ne. In ka tashi tafiya sai ka shiga ka duba ta." Sai ya amsa mata da toh sun ɗan fara taɓa hira ganin dare ya yi ya sa ta kalle shi kafin ta ce" Kan mganar Saudatu ne daman."
Sai ya maida hankalinsa a kan Nene ganin haka ya sa sai ta cigaba da faÉ—in" Na ga an kusa yin sati da É—aurin auran ku kuma ban ga kana zuwa ba, ballantana ma ku yi mganar yadda za ku tsara tarewar na ta."
Shuru na wani lokacin kafin ta ƙarƙare da faɗin" Shi ne daman na kira ka na ce ka zo na ji ko lafiya?
Shuru ya yi kafin ya sauke numfashi.
"Nene."
Ya kira ta amsa kafin ya ce" Daga ke har Gimbiya ku ɗan ƙaramin lokaci don Allah"
"To shike nan"
Nene ta faÉ—a ta na kallon shi a yanayinsa kawai ta gane akwai damuwa.
"Akwai matsala ne Tafida?
Sai ya gyaɗa kai da sauri ta sauke kafafunta ƙasa ta zauna dakyau ta na faɗin" Sadiya ce?
Sai ya ƙara gyaɗa mata kai ya ce" Ta ji labari Nene ta ji labari."
Cikin mamaki ta ce" Ta ji labari? Ba ka gaya mata ba ne daman?
Nan ma kai ya gyaɗa mata kafin ya ce" Na kasa faɗa mata ne. Ina ta riƙe mganar daman yau na ke shirin faɗa mata sai kuma na haɗu da yayanta wajen jana'iza sai gashi yana min murna kuma ya ce ita ta faɗa musu na ƙara aure."
Ya karishe faÉ—a kamar zai yi kuka Nene ta dafa kanshi kafin ta ce" Ka kwantar da hankalinka. Kuna da fahimta kai da Sadiya. Yanzu ka tashi ka tafi gida ka zaunar da ita ka yi mata bayani na san za ta fahimta.'